MUNGO PARK MABUDIN KWARA 06




6. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
Ba ka jin motsin kome, daga na busasshen ganye da mu ke takawa sai kukan namun daji. Sai kuwa kowane jimawa ka ga @bukarmada kura, ko damisa, ko kyarkeci sun gitta. Cikimmu dai babu mai cewa kala, ko tari mai karfi ba mai yi. Haka muka kwana muna @bukarmada cikin wannan irin fargaba har gari ya yi shaa, sa'an nan muka isa wani gari wai shi Kimu, muka sauka muka yi kalaci, muka yi gaba.
Wannan kasa ita Faransai ke kira Gallam, amma a bakin mutanenta da Kaja'aga su ke kiranta. Bisa alama kasa ce mai lafiya, domin ba ta da zafi kamar kasashen bakin teku, su Gambiya. @bukarmada Akwai tuddai da duwatsu ko ina. Ta tsakiyar kasar kuma Kogin Senegal ya bi. Ana kiran mutanen kasar Sarawulli. Sarkinsu yana da iko kwarai, kuma mutanen suna kukan zalunce-zalunce iri iri, da ya dame su da su.
Su Sarawulli babban cinikinsu shi ne fatauci. Suna da ilmi mai yawa na sha'anin saye da sayarwa. @bukarmada Suna cinikin bayi da zinariya da Faransai, suna kuma sayar wa Ingilishi da ke zaune a Gambiya bayi da hauren giwa.
An ce su masu gaskiya ne wajen ciniki, ba rikici, ba kuma cin kura. Im mutum ya dawo daga fatauci, 'yan uwansa da abokansa su kan taru su ga @bukarmada irin ribar da ya ciwo. In an ga ya zo da dukiya an san ya iya ciniki ke nan, sai a maishe shi mutumin kirki, a ba shi girma. Amma in kasuwa ta bashe shi, @bukarmada bai komo gida da kome ba, sai zagi da zambo. Su kan ce wai wane da ya je fatauci bai komo da kome ba sai gashin kansa!
Ran 24 ga Disamba muka isa wani kauye wai shi Joag, muka sauka a gidan dagacin garin, ana kiran sarautarsa "Duti'' Musulmi ne cikakke, kuma karimi. @bukarmada Akwai mutane dubu biyu a garin. Yamma da garin akwai wata yar korama, ana yin albasa mai yawa a fadamarta.
Da yamma ta yi aka ce in je in yi kallon rawa. Wai al'adarsu ce im bako ya zo su shirya wani wasa wanda zai ba shi sha'awa. @bukarmada Rawar tana da ban sha'awa, kuma matan sun iya rangaji da rangwada mai kyau in suna taka rawar.
Kashegari ina barci da dare, sai ga masu dawaki mutum biyar suka zo, suka ce da Duti wai Baceri, babban Sarkin kasar Kaja'aga, ya ji wani Bature ya shigo kasarsa, saboda haka ya turo su don su neme ni. Suka zo dakina, suka kewaye ni. Sai daya daga @bukarmada cikinsu ya yi mini magana cikin harshen Mandingo, ya ce wai na shiga cikin kasar Kaja'aga ba tare da biyan fito da gaisuwar Sarki ba. Saboda haka, bisa shari'ar kasar, yanzu duk abin da na ke da shi za a karbe. Kuma ya ce Sarki ya umurce su maza su tafi da ni Ma'ana, garin da Sarki ke zaune. In kuwa na ki tafiya a kan girma da arziki, am ba su umurni su kai ni ko da halin @bukarmada kaka. Yana rufe baki, sai sauran duk suka mike, suka ce in wuce mu tafi.
Na roke su su bar ni im ba dokina ruwa, kuma in sallami Duti, mai masaukina. Na kebe mai masaukina waje guda, na kawo 'yar kyauta na yi masa, na kuma nemi shawararsa bisa wannan al'amari. @bukarmada Ya ce yadda duk mutanen nan suka juya ni kada in yarda in tafi Ma'ana. In tafi kurum in gaya musu cewa na san na yi laifi tun da na shiga kasar Sarki ba tare da biyan kudin fito ba, amma @bukarmada zam biya yanzu. Ban yi haka don na raina Sarkinsu ba, sai don rashin sani. Sai na tafi na kawo awon zinariya biyar da Sarkin Bondu ya ba ni, na ba su, na ce su kai wa Sarki. Suka karba, amma suka ce ba su yarda ba sai sun yi cajin kayana. @bukarmada Nan da nan suka kwance kayan, suka tona, suka wargaza babu wani abin kirki. Ashe su da zatonsu za su sami zinariya ne a ciki. Da ba su samu ba, suka ce ba za su bar ni kawai ba, saboda haka suka kwashe mini galibin tarkacena suka tafi. @bukarmada
Na zama abin tausayi. Na komo ba wuri, ba kayan wuri, wadansu cikin mutanena suka karai a zuciya, suka ce sai mu juya gida, don kuwa tafiya gaba ba ta yiwuwa a wannan hali. @bukarmada Tafintana Johnson ya ce ai mafarki ne in ce zan ci gaba. Na ce ni kuwa ba zan koma ba.
Da gari ya waye muna son mu ci gaba, amma yunwa ta ci karfimmu. In na ce zan ciro kudi in sayi abinci, za a tafi a gaya wa Sarkin a ce ina da kudi, ya aiko a washe ni. Saboda haka @bukarmada muka yi niyyar daure yunwa har mu sami damar sayen abinci, ko mu yi bara. Haka muka zauna har maraice, babu wanda ya sa abinci a bakinsa. Yunwa ta ci, har ta fita.
Muna cikin zama a waje sai ga wata tsohuwar baiwa da kwando a kanta. @bukarmada Ta gaishe ni, ta kuma tambaye ni ko na rigaya na ci abincina na yamma. Sai na zaci ba'a ta ke mini saboda haka na fita sha'aninta. Amma yarona ya gaya mata irin halin da mu ke ciki, ya ce Sarki ya washe ni duk, ba ni @bukarmada da ko aninin sayen abinci. Da jin haka sai tausayi ya kama ta, ta yi ta duntso gyada tana ba mu. Ta wuce abinta, ko tsayawa ta ji godiyarmu ba ta yi ba. Wannan alheri ya yi mini dadi kwarai a zuciya, har abada kuwa @bukarmada ba na manta shi, ba na kuwa manta mai yinsa. Wannan tsohuwar baiwa ta ba ni sha'awa. Don in an dubi irin halin da ta ke ciki, da irin wuyar bautar da ta ke sha, amma duk da haka ta san jinkai abin kirki ne, lalle a yaba mata. Ta san yunwa ba ta da dadi, don ita kanta ta sha @bukarmada dandana azabar yunwa.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)