MUNGO PARK MABUDIN KWARA 07




7. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
@bukarmada
...
Muna cikin zama a waje sai ga wata tsohuwar baiwa da kwando a kanta. @bukarmada Ta gaishe ni, ta kuma tambaye ni ko na rigaya na ci abincina na yamma. Sai na zaci ba'a ta ke mini saboda haka na fita sha'aninta. Amma yarona ya gaya mata irin halin da mu ke ciki, ya ce Sarki ya washe ni duk, ba ni @bukarmada da ko aninin sayen abinci. Da jin haka sai tausayi ya kama ta, ta yi ta duntso gyada tana ba mu. Ta wuce abinta, ko tsayawa ta ji godiyarmu ba ta yi ba. Wannan alheri ya yi mini dadi kwarai a zuciya, har abada kuwa @bukarmada ba na manta shi, ba na kuwa manta mai yinsa. Wannan tsohuwar baiwa ta ba ni sha'awa. Don in an dubi irin halin da ta ke ciki, da irin wuyar bautar da ta ke sha, amma duk da haka ta san jinkai abin kirki ne, lalle a yaba mata. Ta san yunwa ba ta da dadi, don ita kanta ta sha @bukarmada dandana azabar yunwa.
Bayan mun babbaka gyadarmu mun ci, mun sha ruwa, sai muka shirya. Har za mu tashi sai aka ce wai wani dan'uwan Sarkin wai shi Demba Sego zai zo mu gaisa. @bukarmada Da muka sadu da shi, na kwashe masifar da na ke ciki duka na fada masa. Ya yi bakin ciki kwarai da gaske ya yi mini alkawarin fisshe ni kasar Kaja'aga har zuwa kasarsu, Koson. Na yi murna, na shirya, muka tashi daga Joag ran 27 ga Disamba. Da shi da mutanensa da nawa mun kai mu talatin, a haka muka yi ta tafiya har muka kai Sami. A nan muka kwana, @bukarmada kashegari da sassafe muka tashi, rana tana sunkuyawa za ta fadi muka isa Birnin Koson.
Da isa Koson sai Demba Sego ya nuna mini halin 'yan duniya, wadanda ba su yin kome don lada sai don la'ada. Ya ce tun da ya fisshe ni daga hadari, lalle kuwa in yi masa wani dan alheri in nuna godiyata. A zatona ba zai mini haka ba, ganin yadda na nuna masa wason da Sarkin Kaja'aga ya yi mini karkaf a Joag. @bukarmada Na dai kanne, na ba shi dunkulen amba kawai da daurin ganyen taba. Ya yi murna, ya gode. Na tashi daga Koson, sai Tisi inda uban Demba Sego ya ke dagaci. Uban ya yi mamakin ganina, ya ce tun ran da Allah ya yi shi bai taba ganin Nasara ba, sai labari. Na gaya masa irin abin da ya kawo ni kasar, don in ga yadda ta ke ne kurum, da yadda mutanenta su ke, da irin halinsu @bukarmada Amma bai yarda ba. A zatonsa lalle ina da wata niyya dabam wadda na boye. Ya ce sai in je Kunyakare in ga Sarki !
A Tisi ne na fara ganim ma idona irin azabar da bayi ke sha. Na ga yadda mutum ke shimfide dan uwansa mutum yana bugu, bai kula ba, @bukarmada kamar yana bugun ice babu tausayin rai, ba tsoron Allah.
Ran 9 ga wata na ga tashin hankali. Sarkin Tisi, uban abokina Demba, ya turo dan ya ce ya zo wurina im ba shi kudin fito, in kuma biya duk ladan dawainiyar da suka yi da ni. Na gaya wa Demba ba ni da kome, duk an washe ni a Joag. Nan da nan sai ya sake fuska ya yi kamar da dai duniya bai ma taba sanina ba. Ya sa yaransa suka bude kayana, ya kwashi abin da ya yi masa dadi. Aka bar ni finfirimfin, babu kome kuma. @bukarmada Ganin haka fa yarana suka tasam ma yi mini tawaye, don sun sani ba mu da sauran abin yi, sai ko mu yi bara kana mu sami abinci. Na yi na yi da su mu ci gaba, suka ki.
Sai na yi dabara na ciro kudi, na ce a je a sayo katon rago a zo a yanka mu ci. Da ganin haka sai suka zaci akwai ni da tsimina a boye, sa'an nan suka yarda suka bi ni.
Amma kafin in tashi daga Tisi bari im fadi wata shari'a da na ji mai ban dariya. Mutanen garin addininsu ya kasu kashi biyu, da na Arna da Musulmi. Wata rana wani dan Arna ya auri wata kyakkyawar yarinya. Yana sonta @bukarmada kwarai, har don tsananin so ba ya son abin da zai raba su, ko da rana daya. Ana nan sai yaki ya tashi tsakaninsu da mutanen wani gari. Sai yaron nan ya tafi wurin wani malami, ya roke shi ya taimake shi kada a kama shi wurin yaki. Sai malami ya ce to, kada ya rika kwana a gidansa sai bayan kwana arba'in. Ashe malami yana zagawa @bukarmada yana kwana. Da yaro ya gane ya kai shi kara gun Sarki, aka kira matar ta tabbatar.
Nan da nan aka yanke shari'a, aka kukumce malam aka ce yaro ya zaba. Ko dai malam ya ba shi bayi biyu ko kuwa yaro ya kama malam ya zama bawansa. Amma yaron ba ya son ko daya, ya ce shi abin da ya ke so shi ne a shimfide malam a kofar gidan Sarki @bukarmada a yi masa bulala. Sarki ya yarda, aka sa malam ya tube sai wando, sa'an nan aka sa ya rungume wata itaciya, aka hada hannuwansa aka daure. Wani shirgegen kato cikin mutanen Sarki ya jawo kwagiri ya dinga shimfida wa malam, ji ka ke talau, talau, sai da aka yi arba'in daya babu. Malam sai kugi, yana ta kwabin laka wuri guda. Mutanen da ke kewaye @bukarmada kuwa, maza da mata da yara, sai dariya su ke yi, suna yi wa malam eho.
Da ya ke an ce tilas sai na ga babban Sarkin kasar a Kunyakare, sai na tashi daga Tisi na nufi can. Muka iso Madina, garin daya daga cikin abokan tafiyata. Da muka kusato kofar garin, sai muka tarad da @bukarmada yayyensa biyu sun zo tariyarsa, ashe har sun ji yana tafe. Suka dauko maroki musamman daga gari don tariyar. Muka dunguna cikin gari tare da su marokin nan yana kan gaba yana rera waka. Da shiga sai garin ya yi caa, mutane na duddulowa daga kowace jiha. Suka bi mu duu har gidan su mutumin nan. Da isarmu kofar gida aka yi ta rusa bindiga, @bukarmada aka alamta sauka. Sauran 'yan'uwansa da abokansa sai ihu, suna tsalle saboda dawowa tasa lafiya. Ana cikin wannan murna, sai ga uwa tasa ta zo don ta yi masa barka da sauka. Tsohuwa ce tukuf, sai da sanda ta ke iya tafiya, kuma ba ta gani. Ta shafa fuskarsa, da kansa, da kuma hannunsa, ta gode wa Allah da ya sada ta da dan nan nata tun ba ta mutu ba. Saduwar uwan nan da danta ya ba ni @bukarmada tausayi kwarai, kuma na tabbata da Bakar Fata da Bature duk halittarsu guda ce, ko da ya ke sun bambanta a fatar jiki.
Da kura ta kwanta, aka ce mutane su zauna don mutumin nan ya fadi labarin tafiyarsa. Da zai fara, ya yi wa Allah godiya saboda tafiyarsa Gambiya lafiya, da komowa tasa gida lafiya. Ya kuma fada musu irin taimako da @bukarmada na yi masa, ya nuna ni a inda na ke zaune a gindin wani daki, Duk idon mutane ya juyo kaina ashe wadansu ma ba su lura ina wurin ba sai a lokacin saboda yawan murna. Da ganin irin fatar jikina, da yawa cikinsu sai suka firgita. Mata masu 'ya'ya kowa ta jawo danta kusa da ita. Da ce na dam motsa sai ka ga kowace ta figi danta ta ruga. Sai da kyar sa'an nan @bukarmada abokin tafiyata ya ciwo kan mutanen suka yarda ni mutum ne kamarsu, ba aljan ba.
Na kwana biyu a Madina, na tashi na nufi Kunyakare, inda Sarkin Koson ke zaune. Kafin in kai, sai na baude na tafi wani dan gari wai shi Sulo, don in ga wani farken bayi da a ke kira Salim Daucari. @bukarmada Shi Salim Daucari sun saba da Dr. Laidley kwarai da gaske, har akwai dukiyarsa ta bayi biyar a hannunsa. Da zan taso daga Gambiya, Dr. Laidley ya ba ni takarda in kawo wa Salim, don in karbi dukiyan nan in sami guzuri. Muka kuwa yi sa'a Salim yana gida. Ya karbe ni da murna, ya yi mini kyakkyawar sauka.
Amma abin mamaki shi ne ko sa'a biyu ban yi ba da shiga Sulo ashe har labari ya kai kunnen Sarkin Koson a Kunyakare. Muna zaune sai ga Sambo, dan Sarkin ya ce wai ubansa ne ya aiko shi ya ji dalilin da @bukarmada ban tafi Kunyakare ba, na toge a Sulo. Salim Daucari ya ba shi magana, ya ce ya je ya gaya wa ubansa ga mu nan tafe da maraice. Rana na sunkuyawa za ta fadi, sai muka tashi har da Salim Daucari sai Kunyakare. Kafin mu isa, Sarki ya shiga gida ya kwanta, @bukarmada saboda haka ba mu gan shi ba sai da safe. Sambo Sego ya kai mu gidansa, muka kwana.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)