MUNGO PARK MABUDIN KWARA 11




11. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
NA ZAMA WANZAMI!
Larabawan Benaum, ko da ya ke su kansu ragwaye ne, masu son jiki, duk da haka ba su barin wanda ya shiga @bukarmada hannunsu ya yi sukuni. Yarona Demba shi a ke turawa kullum ya samo wa dokin Ali ciyawa. Nikuwa bayan an jarraba ni a sauran ayyuka duk an tarar ba zan yi amfani ba, ran nan sai aka ce in zama wanzami. Na zama Sarkin aska, don an ce a fada zam fara aski, kuma a kan wani dan yaro, autan Ali, zam fara nuna gwanintata. Aka @bukarmada nuna mini wuri na zauna, yaron kuma ya zauna a gabana. Aka dauko mini wata 'yar aska, tsawonta kamar inci uku, aka ce in shafa ruwa, im fara. Na shafe kan duk da ruwa, don Larabawan wannan jiha su kan aske kan 'ya'yansu ne duk. Na kuma danki aska na shiga aski. @bukarmada Abinka da mai koyo, da farawa sai kuwa askar ta yanki yaron kadan a kai, sai jini. Da Ali ya ga haka ya husata, ya ce lalle ban san yadda a ke aski ba, saboda haka in sakam masa kan da, in ajiye askar, im fita. Kora ba ta da dadi, amma na yi murna da wannan korar da aka yi mini. Na riga na daura niyya a zuciyata duk abin da zan yi mutanen nan su ce da ni @bukarmada madalla, ba na yinsa. Don na ga ta haka ne kadai zan iya samun kubuta daga hannunsu.
Ran nan sai na sami labari wai wadansu Larabawa su hudu sun zo tare da tafintana Johnson. Wai sun kamo shi a masaukina a Jarra, suka kuma tilasta mai masaukin nawa ya ba su duk kayana da na bari ajiya a hannunsa. Aka kai Johnson gaban Ali, aka @bukarmada kwance kayan. Aka aika aka kira ni na zo na fadi akin ko wane abu. Sai Ali ya sallame ni, ya sa aka daure kayan aka sa a wani katon burgami da ke cikin tantinsa. Da na komo gida, sai Ali ya turo mutanensa ya ce a gaya mini akwai barayi da yawa, saboda haka ya fi kyau in aika da kayana duka gare shi ya ajiye mini. Na tattara na aika masa, na dai san niyyarsa. Da aka wance masa kayan, bai ga abin kirki ba, sai haushi ya @bukarmada kama shi. Da shi zatonsa ina tafe da zinariya ne mai yawa.
Amma dai har yanzu bai yarda ba ni da zinariya ba, saboda haka ya sake turo mutanen nan na farko ya ce su zo su caje ni kaf, da jikina da dakina. Kura fa ta sami akuya, ai abin sai kallo. Suka shigo suka ce im mike, suka fara caje ni, duk jikina babu inda ba su taba ba. Suka kwashe zinariyar da na boye, da ambar da gogon @bukarmada hannuna, da magwajin jiha (kamfus). Allah Ya sa na yi dabara na boye kamfus guda cikin rairayi tun daren jiya. To, ban da shi kamfus din nan da na boye sai tufafin da ke jikina kadai wannan mugu, Ali, ya bar ni da shi a duniya! @bukarmada
Ali ya yi murna da samun zinariya da ambar, amma ya fi murna da samun kamfus din nan. Suna duban kamfus wani abin sihiri ne kwarai, don haka Ali ya ce in zo in bayyana masa yadda ya ke. Ya tambaye ni dalilin da allurar fuskar kamfus din kullum sai hamada ta ke duba. Na rasa amsar da zam bayar, in na ce ban sani ba su zaci wani abu ne muhimmi na ke so kada su sani. Can sai wata hikima ta zo mini, na ce amfaninsa yana nuna mini halin da uwata ke @bukarmada ciki ne. Tana zaune can da nisa n e gaban hamadar Sahara. To, muddin tana da rai, alluran nan za ta nuna jihar da ta ke, in kuma ta mutu, ta nuna mini jihar kabarin. Mamakin Ali fa ya karu da jin haka. Ya juya kamfus din nan, ya sake juyawa, ya karkada, amma a kowane lokaci sai ya ga arewa allurar ta ke duba. Sai tsoro ya fara kama Ali, ya dauko kamfus dina a hankali kamar wanda ke rike da kwai, ya mayar mini da abina. Ya ce ya tabbata akwai wani sihiri @bukarmada game da shi, saboda haka shi ba zai ajiye kayan sihiri a gidansa ba.
Wata rana zafin rana ya dame ni, sai na fita daga bayan gari, na. kwanta a gindin wata itaciya. Can sai ga wani dan Ali da yaransa sun zo bisa dawaki a sukwane, suka ce sai in tashi mu koma gari. Na tashi na bi su, sai gaban Ali. Na tarar ya tara girar sama da ta kasa, ya daure fuska mirtik. Sai ya @bukarmada buga mini harara, ya zage ni da Larabci, sa’an nan ya jeho mini wata 'yar bindiga. Da na tambayi irin laifina, aka gaya mini wai tun da na tafi bayan gari ba tare da izni ba, lalle ina neman hanyar gudu ke nan. Saboda haka am ba da izni duk wanda ya gan ni a bayan gari daga ran nan ya harbe ni, ba kome.
Wannan abu ya firgita ni, amma ashe ma firgita ba ta zo tukuna ba. Domin ran 20 ga Maris na ji Ali ya kira majalisarsa sun shawarta abin da za a yi da ni. Ko wane ya kawo tasa shawarar irin @bukarmada ukubar da ya ke so a yi mini. Wani ya ce a kashe ni domin ni Kirista ne wani ya ce a yanke mini hannuna na dama kurum a sake ni. Ina dai jin wai-wai-wai, ban yarda ba, sai da wani yaro dan Ali, duk bai fi shekara tara ba, ran nan ya zo dakina. Da ya waiga bai ga kowa kusa ba, sai ya matso kusa da ni, ya rage murya, ya ce mini ya ji wani kawunsa yana rokon Ali kada a kashe ni, kada a yanke hannuna, amma a cire mini idondunana ne, saboda sun yi kama da na kyanwa. Ya ce @bukarmada wannan shawara kuwa a kanta a ke yanzu, amma ubansa ya ce ba zai cire idona ba tukuna, sai an kai ni Fatima ta gan ni. Malam, shiga zuciyata a lokacin da na ji wannan labari ka ga firgita!
NA GA FATIMA
Yau watana daya a tsare a hannun Ali. Kowace rana kuwa cikin watan nan da irin nata bakin cikin da za ta kawo mini. In rana ta fito a gabas ba ni da sukuni, duk in kosa, hankalina ba zai fara kwanciya ba sai na ga ta sunkuya za ta fadi, don a lokacin nan ne kadai miyagun nan za su rabu da ni. A lokacin nan ne kuma a ke kawo mini @bukarmada abinci da ruwan sha, da ni da yarona, im mun ci, sai kuma yammar gobe. Dalilin haka kuwa don wannan wata na azumi ne, Musulmi ba su ci, ba su sha da rana, shi ya sa suka nemi tilasta mini yunwa, ko da ya ke ni Kirista ne. An ce yau da gobe bai bar kome ba. Tun ina jin kaifin wannan yunwa, har na bar ji. Yanzu ma babban abin da ya dame ni shi ne rashin aikin yi, saboda haka sai na shiga koyon rubutun Larabci @bukarmada maganin zaman banza. Mutanen da ke zuwa wurina su ne ke koya mini. Haka na zauna.
Shiru shiru, Fatima za ta zo yau, za ta zo gobe, ba ta zo ba. Sai ran nan Ali ya yi sirdi ya tashi ya nufi arewa, aka ce zai bi ta. Ya tashi da kwana biyu, sai ga wani Sharifi ya zo da @bukarmada kayan gishiri. Aka saukad da shi kusa da dakina. Na yi murna da zuwan wannan mutum, domin mutum ne mai wayayyen kai. Ya yi yawo ya ga duniya. Shi ya gaya mini halayen kasashen da ke gaba, da yadda mutanensu su ke daukar bako irina. Ya ce ya tafi har Hausa, kuma ya dade a Tambutu. Ya @bukarmada ce wai Hausa gari ne babba wanda bai taba ganin gari mai girma kamarsa ba. Na ji dadin zuwan wannan mutum. Shi ya debe mini kewar irin zaman duniyar da na saba da shi, watau na son juna, da tausayi, da girmama mutum, don bai tashi ba sai da Ali ya komo. Kafin dawowar Ali, a kullum sai na tuna labarin cire ido da dan yaron nan ya @bukarmada ba ni. Watau iyakar idona da ganin wani abu a duniya kafin zuwan Fatima ne kurum, da ce ta zo ta kare kallona, za a kwakule su. @bukarmada Wannan mugun abu ya firgita ni kwarai, har in na kwanta da dare ba na iya barci, sai ajiyar zuciya.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)