NAYI WANKAN JANABA SAI MANIYYI YA ZUBO MINI




*_NA YI WANKAN JANABA, SAI MANIYYI YA SAKE ZUBO MINI?_*


                          *Tambaya*
Assalamu Alaikum tambayata itace idan mata ta sadu da mijinta tayi wanka immidietly bayan ta gama tana zaune sai taji sperm ya zubo mata shin zata kara yin wani wanka ko kuma wanda tayi ya isa ?


                            *Amsa*
Wa'alaikum assalam, To idan sabuwar Sha'awa ce ta zo mata, ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma idan saboda saduwar da suka yi ne a baya: za ta wanke wurin ne, ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka, wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bidayatu Almujtahid 1\48 da Insaf 1\232.

Allah ne mafi sani.

2\1\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)