HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA BAYAN ƊAUKEWAR JINI KAFIN TAYI WANKA

*_SADUWA DA MAI HAILA, BAYAN DAUKEWAR JININ, KAFIN TAYI WANKA!!_*


                                *Tambaya:*
Assalamu alaikum, Malam kasancewar saduwa cikin haila laifi ne, to ina hukuncin saduwa bayan tabbatar da daukewar jinin amma gabanin wankan tsarki??


                                      *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shine: ba'a saduwa da mai Haila sai ta yi wanka, saboda fadin Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 222 (Idan Mata suka yi tsarki, to ku zo musu ta inda Allah ya umarce ku), inda suka fassara tsarki a wannan ayar da wanka, Kamar yadda Ibnu Rushd ya ambata a littafinsa Bidayatul Mujtahid.

Saidai shehin malami Abu-hanifah ya fahimci tsarki a wannan ayar da yankewar Jinin haila, wannan yasa suka halatta saduwa da macen da ta kammala haila kafin ta yi wanka. Duk da cewa duka maganganu biyun suna iya shiga ayar, saidai zance mafi inganci Shi ne maganar farko saboda Allah ya kira haila da kazanta a cikin Alqur'ani, kazanta kuma tana bukatar tsafta da gyaran jiki, don kaucewa bacteriar (kwayar cuta) da ta kunsa.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)