RASHIN KARANTA ƘUR'ANI A GIDA

RASHIN KARANTA ALQURANI A GIDA


Karanta alQurani a gida yana janyo saukar Rahama da alkhairi ga ma'abuta wannan gida sannan yana korar masu da ashaidhan,shaidhanu basu iya zama agidan da ake yawaita karatun alqurani musamman suratul Baqara.

Amma kuncin rayuwa da rashin albarka da Rahama da rashin jin dadi yana tare da gidan da ba'a karanta alqurani.

Abi Hurairata رضي الله عنه yac:
*Lallai gidan yana samun walwala da jin dadi acikinsa ga mazauna cikinsa,kuma Mala'iku suna ziyartar wannan gida kuma shaidhanu suna gudu daga wannan gida,kuma alkhairin masu yawa yana sauka acikinsa idan ana karanta alqurani a wannan gida*"

Kuma lallai gida yana samun;
*"Kunci da damuwa da rashin walwala ga mazaunansa kuma mala'iku suna kauracewa wannan gida,kuma shaidhanu su mamaye wannan gida,kuma alkhairi yana karanta acikinsa sai sharri ya yawaita acikinsa,duk saboda rashin karanta alqurani"*.
@سنن الدارميّ (٣٣٥٢)].

  Allah ne mafi sani


Allah bamu ikon karanta alqurani mai yawa tare da ikhlasy.
Post a Comment (0)