RIGAKAFIN SIHIRI DA SHAYTANU GUDA GOMA SHA BIYAR.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WA BARKATUHU.
Kafun mu daura akwai gyara a karatun jiya. 1. Alkamar da za a ayi amfani dashi wurin kununcan ba a surfawa bakacewa kawai akeyi. A nika.
2. Magani na sha bakwai (17) bayan an sha habbatussauda an tattauna ruwan zamzam da za a sha za a zuba masa zuma don ya rage baurin habba."
Rigakafi goma sha biyar. Abubuwan da idan ana yi da izinin Allah sihiri ko shaydanu bazasu shafe mutum ba koda sun shafe shi bazasuyi tasiri ba.
1. Cin dabino guda bakwai da sassafe, (ajwa) yazo a hadisi cewa ko guba kaci a yinin ranar sai dai ka amar dashi ba abunda zai kamaka na cutarwa bi'iznillah. Gida masu dabino sune masu arziki.
2. Zama da alwala kodayaushe. Mutum ya kasance mai rike alwala yana karyewa a sake dauro wata, shaidanu bazasu samu damar shiga mutum ba.
3. Tsare ko kiyaye sallah a jam'i idan mace ce kuma sallah a kan lokaci. Ana kirar sallah a tashi ayi alwala ba jinkiri wannan ma zai hana shaidanu shiga jikin mutum.
4. Qiyamullayli. Duk mugun abu ya taso zai shigeka ya samu kai mai tsayuwar dare ka bautawa Allah ne to bakin ciki kashe shi yakeyi don ba yanda za ayi ya cutar da wanda Allah Ya kubutar ya yiwa ni'ima ya kuma boye karkashin rahamarSa.
5. Addu'ar shiga bandaki. A bandaki akwai najasa nan ne matattarar shaydanun aljanu, musamman idan kazantaccen bandaki ne. Akwai hatsari sosai ta cutar zahiri da na shaytanu don haka lallai a rungumi tsaftace muhalli don tserewa shaytanu. A bandaki akafi ajiye sihiri don haka a kula.
6. Cewa A'udhubillahiminashaytanirrajeem bayan addua'ar bude sallah kafun a fara karatun fatiha.
7. Yiwa amarya Addu'a a ranar farko, idan miji ya shiga ya kama goshin matarsa ya karanta "Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha 'alaihi wa a'udhu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha 'alaih"
Don a sabbin gida ko kullallun gida shaytanu na nan a baje a ko ina musamman cikin ceiling da empty rooms duk inda akayi ta addu'o'i to ana weakening makamansu.
Harma a koresu.
8. Bude rayuwar aure da sallah na nafila raka'a biyu zai kara tsare ku daga shaytanu. Malam yayi bayani yana da kyau mace tabi mijinta su gabatar da wannan idan bai iya alwalar mai kyau ba tayi ya bi. Idan kuma itace bata iya ba ta bishi suyi ko ta iya yanayi tana yi zai yi creating bond tsakaninsu na yin ababe tare. Idan ango yace bismillah shigo muyi alwala, amarya kar ta gwasale shi tace ai ni na riga nayi ko kinyi ki tashi ku sakeyi tare wannan ne step na farko da zaku gina gidanku da shi ku fara cikin tarayya da kaunar juna da kula da juna.
9. Karanta addu'ar saduwa "Bismillah Allahumma jannibnashaytana wa jannibishaytana ma razaqtana". Karanta wannan zai sa shaytan bazai taba cin galaba akan abun da Allah zai azurtaku dashi ba a wanan daren.
10. Yin alwala kafun bacci da karatun ayatul kursiyyu yana kariya. Alwalar bacci baya karyewa har sai gari ya waye, kuma duk mai alwala kafun ya kwanta yayi bacci, mala'iku zasu na roka masa gafarar Allah har gari ya waye domin yana cikin tsarki. Koda ace ya fidda iska cikin dare.
A duba kissar shaytan da Abu Huraira inda yace shaytanu basa iya cutarda wanda ya karanta ayatul kursiyyu kan yayi bacci.
11. Fadin la'ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shay'in qadir *100
12. Fadin " A'udhu billahil azeem wa bi wajhihil kareem wa sultanihil qadeem minashaytanirrajeem. Bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulillah. Allahummaftahliy abwaba Rahmatik. " idan za a shiga masallaci. Wunin ranar gaba daya shaytan bazai shafe ka ba in sha Allah.
13. Idan gari ya waye a karanta wannan sau uku
"Bismillahilladhi la yadurru ma'a ismihi shay'an fil ardi wala fissama'i wa huwassami'ul 'aleem"
14. Bismillahi tawakkaltu 'alallahi wa la haula wala quwwata illa billah. Da zaran za a bar gida. (tunda kai ka fita wannan zai kareka, a gida kuma yana da kyau ka musu addu'ar kariya ka bada amanarsu gurin Allah "astaudi'ukumullahallazi la tadi'u wa da'i'uhu." idan miji yayiwa matarsa wanann addu'ar da yaransa idan zai fita mace kuma ya kyautu ta masa wannan addu'ar don samun nasara a harkokinsa da neman albarka a rayuwarsu. "zawwadakallahu taqwa wa gafara zambaka wa yassara laka khaira haythu ma kunta" da iznin Allah albarkatu zasu samu sai dai a dawo miki da busharar hajji ko mota tear leather 😂 nasha nasha budi zai zo.)
15. Karanta "A'udhu bikalimatillahi tammat min sharri ma khalaq." Kowace yamma.
Allah sa mu dace.
A nan zamu dakata bi'iznillah.