MUNGO PARK MABUDIN KWARA 17

17. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...


 
Saboda haka na ce gwamma in koma gida da dan abin da na gano, don kada im mutu ya bace. Amma kuma sai na zama gaba zaki, baya sayaki. Ba na iya ci gaba, kuma ba na iya komawa baya. Tsakanina da Gambiya ya kusa mil dubu, ga shi ba ni da lafiya, ba ni da doki, ba ni da kudin saye, ga damina ruwa ko yaushe. To, amma kuma im ban koma ba, wurin wa zan zauna ? Kila duk wanda ya duba dalilan nan nawa da kyau, da irin halin da na ke ciki, ba zai zarge ni ba saboda na komo da baya, ban ci gaba har in gano kurewar Kwara ba. Na tabbata na yi @bukarmada iyakar kokarina bisa bin tsawon kogin har in gano bakinsa. Kasawa na yi, ba na ki ba ne. Da a ce na tabbata na kusa da karshen Kwara, ko in da zan sami taimako a gaba, da na wuce. To, rashin wucewan nan fa tilas ce ta sa, ba gudun wuya ba ne, ba kuwa tsoron kamu ba ne. Saboda haka ban kula da zargin da mutane za su yi ba, tun da dai ni na tabbata tilas ta sa ni komowa, ba son rai ne ba, ba kyauya ba, wadanda suka aiko ni kuma sun tabbata hakanan. Sun san na yi kokari, za su kuma yaba dan abin da na gano wa duniya game da Kogin Kwara da kasar Afirka. Saboda haka na ji dadi, na kuwa gode wa Allah.
Da na daura niyyar komawa baya daga Silla, sai na ga ya kamata in sami sanin yadda Kogin Kwara ya ke daga gaba, da inda ya nufa, da kasashen da ke gaban Silla, da halin zaman mutanensu. Saboda haka na shiga tambaya fatake da Larabawa labarin kogin. Kowa na tambaya sai ya ce kogin ba shi da iyaka, makurarsa bayan duniya. Amma wai daga nan Silla kogin ya fada a wani babban tafki da a ke kira Dibbi. Daga nan ya rabu, ya yi wani babban tsibiri, ya sake gamewa a Kabra, kusa da Birnin Tambutu. A cikin kasashen da ke gaba, an ce akwai Hausa, da Katsina, da Masina. Arewa maso gabas da Masina, nan ne mashahurin garin nan Tambutu ya ke, wanda a ke ta jin labarinsa a Turai, amma Bature bai taba ganinsa ba. An ce duk garin babu matsiyaci, wadansu ma sun ce da zinariya aka dabe titin garin duka! Wadannan su ne irin labarun da na samu na kasashen da ke gaba da Silla.
NA KOMO DA BAYA DAGA SILLA
To, saboda dalilan nan da na bayar, sai na juyo da baya daga Silla. Na fada wa Sarkin garin haka, na ce kuma da ya ke dalilin zuwana don in ga yadda Kogin Kwara ya ke ne, yanzu zan ketare im bi tsawonsa ta gabar kudu in kara saninsa sosai. Sarkin Silla ya ce gwamma in koma ta hanyar da na biyo, watau gabar arewa, don gabar kudu ba ta biyo da damina, saboda fadamu. Na bi shawararsa, na juyo. Ya sa aka dauke ni a jirgi sai Mursau. A can kuma na yi hayar wani jirgi zuwa Kea, na biya wuri arba'in. Sarkin garin ya hana ni masauki, sai da na biya shi wuri arba'in. Ya tura ni a wata bukka inda bayinsa ke kwana, muka kwanta tare da su. A cikin bayin wani ya ji tausayin huntancina, sai ya ciro wani @bukarmada gwado nasa babba, ya ce in rufa maganin sanyi da a ke yi, da safe im mayar masa. Kashegari na tashi daga Kea, na kuwa yi sa’a akwai kanen Sarkin garin zai tafi Modibbo a ran nan, sai muka jera tare. Ni ina dauke da farin kudina, shi kuma yana dauke da sirdina.
Muna cikin tafiya sai muka tarad da wadansu tukwane a gefen hanya. Sai na ga abokin tafiyata ya figi ganye ya jefa a kan tukwanen. Ya yi mini alama ya ce ni ma in yi hakanan. Ban ki ba, na yi. Da muka wuce na tambaye shi dalilin wannan al'ada, sai ya ce wai tukwanen nan kowa haka ya gan su, ba a san mai su ba, na aljannu ne. Don haka kowa zai wuce sai ya rufe su da ganye don ban girma ga mai su. Muna tafe muna tadi har muka zo wani wuri. Sai na ga abokin tafiyata ya yi baya yana nuna yatsarsa a kasa. Ko da na duba sai na ga kafar zaki inda ya taka yanzu. A nan gardama ta tukke, shi abokin tafiyata tsoro ya kama shi, yana cewa sai in wuce. Can sai @bukarmada gardama ta baci, sai ya jefar mini da sirdina, ya shiga daji. Da na ga haka sai na ce a zuciyata mene ne ma amfanin sirdi a gare ni tun da ba ni da doki, ba ni da kudin saye? Saboda haka sai na cire likkafun, sirdin kuwa na dauka na jefa cikin Kwara. Ashe mutumin nan yana duban duk abin da na ke yi. Sai na gan shi but ya fito daga cikin duhuwa a guje, ya fada funjum a cikin Kwara ya dauko sirdin. Yana fitowa ya garzaya a guje ya tsere da shi, rabuwarmu ke nan. Nan ya bar ni a kungurmin daji, na yi ta tafiya ni kadai, zuciyata sai harbawa ta ke yi don tsoron zaki. Da haka dai har na isa Modibbo.
Na iso Modibbo, ina dauke da takarduna da kayan farin kudi. Muna gaisuwa da Sarkin garin, sai na ji haniniyar doki.
Sarki ya ce, “Ka san mai haniniyar can ?" Na ce, "A'a"
Ya ce, “Ai dokinka ne, ga shi nan ya murmure sarai, sai ka kama abinka.”
Sai na ji kamar ya ba ni duniyan nan ne don murna. Bayan haka kuma ya ce in yanki daji ne, kada in kuskura in shiga wani gari a cikin kasar Bambara, domin Sarkin Sego ya aiko da mutane su neme ni, su kama. Domin wai bayan na bar Sego an gaya masa ni dan rahoto ne. @bukarmada Babbar sa’ata kuma sai na tarar mutumin nan da ya gudu mini da sirdi ya ji tsoro kada im fada wa Sarkin Modibbo, ya ba shi sirdin.
Saboda haka na yanki daji, na dinga bin gefen kogi. Ashe labarina duk ya watsu a kasa, inda na tafi sai a kore ni. Da haka har na bulla a Sansandin. A nan ne na tabbatad da gaskiyar wannan labari, domin da na tafi wurin Kunti Mammadi, Sarkin garin, da kyar ya amsa gaisuwata, da kuwa, lokacin da zan wuce, shi ya taimake ni har na tsira daga hannun Larabawa. Can wajen tsakar dare sai Mammadi ya shigo dakina, ya ce da ni ya kamata im bar Sansandin tun da asuba, kuma in kauce wa Sego. Ya kawo guzuri ya ba ni, muka yi sallama. Na gode wa Mammadi, mutumin kirki ! Da azahar sai na isa Kabba. Amma da kusatowa kofar garin, sai na hangi mutane a zaune. Can sai na ga wani cikinsu ya zo ya kama linzamin dokina, ya nuna mini wata hanya da ta zaga bayan gari, ya ce in yi maza im bace. Na ce ya bar ni in kwana da safe in wuce, don kuwa ga dare ya yi. Sai ya harare ni, ya daka mini tsawa ya ce, “Ka tafi, aka ce. In ka ki kuwa, yanzu ka cim ma na lahira !" Na kutsa kai a dajin Allah da dare, ga namun daji iri iri. Bayan na taba ’yar tafiya, sai na iso wani kauye. Na cim ma dagacin garin yana faskaren itace. Da na ce ina son wurin kwana, sai ya ce im fita masa gari.
Na yi ta bin tsawon Kwara, ina kauce wa mutane, har na wuce Sego, na kai wani gari wai shi Kaimu. Nan na sami wurin kwana da kyar, amma da na nemi dawa da kudina, sai suka ki sayar mini. Ina cikin damo-damo da yunwa, sai wani ya kunso tsabar dawa danya ya kawo mini. Ya ce ya ba ni sadaka ne don in yi masa addu'a. Ashe sun dauke ni wai Sharifi ne. Na @bukarmada karbi tsaba na juye, na yi masa addu’a a fili da Turanci, na tofa masa, na shafa kansa, ya tashi da murna yana godiya. Tsabar dawar ita na raba biyu, na tsuki rabi, na ba dokina rabi. Yau kwanana uku ke nan ina tsukun dawa danya, abincina ke nan.
Da tashi na isa wani gari wai shi Song da yamma, amma da ganina mutanen garin suka rufe kofar garinsu. Na kwanta a gindin wata itaciya daga wajen gari. Zuwa can dare sai na ji rurin zaki yana kusato ni. Na firgita, na sheka sai kofar garin. Na bugi kofar, na buga, na yi kururuwa, na ce da mutanen su bude mini, ga zaki zai cinye ni. Sarkin kofa ya ce in tsaya sai ya fado wa Sarki tukuna.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Telegram: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)