IYA GIRKI


IYA GIRKI

Bissmillahir Rahmanir Raheem

Kowacce al'umma ta na da irin al'adun ta, wasu ka ga suna kamanceceniya da juna wasu kuma su saɓa. Al'amarin iya girki yana ɗaya daga cikin abubuwa ƙalilan waɗanda kusan duk al'ummomin su ke da al'ada kusan iri ɗaya akai, wannan kuwa Shi ne: Kowa yana so ace mahaifiyarsa, matarsa, ƙanwarsa, ɗiyarsa, jikarsa da duk wata mace makusanciyarsa ta iya girki, hakan shaida ne ga kowa dangane da muhimmancin a ce mace ta iya girki.

Rashin iya girki yau a ƙasar mu ta Hausa ya zamo wa mata tamkar wata masifa ce, domin kuwa da yawan su sun zama zawarawa a sanadiyar rashin iya girki, wasu ga su da kyau da tsafta da duk abinda ake nema ga mace, amma ba ta iya girki ba, hakan ke sa dole mijinta ya ƙaro aure domin ya samu wannan biyar buƙata na cin abinci wanda aka sarrafa shi bisa ƙwarewa. Abubuwa da dama sun ba da gudunmuwa wajen haifar da wannan matsala ta rashin iya girki a tsakanin matayen mu na yau, daga ciki akwai sakacin iyayen mu mata wajen horar da 'yan mata davarun girki, akwai kuma lalaci da ga wasu 'yan matan ma su tasowa da kuma rashin bai wa girkin muhimmancin da ya kamata ace ana ba shi. Alhamdulillahi yanzu an fara samun sauƙin lamarin saboda an samu jajurtattun mata su na koyar da dabarun girke-girke iri daban-daban a kafafen rediyo, talabijin da kuma shafukan sada zumunta. Sai dai kuma duk da haka, ƙalubalen raguwa ya yi, amma matsalar ta na nan.

Matan aure da 'yan mata da yawa yau sun maida hankali sosai wajen ganin sun iya matsi tare da shan kayan ƙarin ni'ima fiye da yadda su ke ƙoƙarin ganin sun iya girki. To ba laifi bane don kin koyi wannan tun da shi ma wata hanya ce ta gyaran zamantakewar aure, amma 'yar uwa ki sani cewa. "Mijin ki yana iya sati ko fiye da haka bai kusance ki da kwanciyar aure ba, amma babu yadda za'a yi ya yi sati ba tare da ya ci abincin ki ba matuƙar yana gida ba tafiya yayi ba". Kenan in hakane, iya girki shi ya kamata ace kin fi maida hankali a kai fiye da shaye-shayen magungunan ni'ima waɗanda wasu ma suna cutarwa.
Akwai mataye da dama da iya girkin su kaÉ—ai ya sa mazajen su ba su sake su ba, amma ke kina nan kina taÆ™ama da kyau ko diri, akwai mata da yawa waÉ—anda iya girki ya hana a yo mu su kishiya, ke kuma kina nan kina hauragiya da hauma-hauma. Lallai 'yan uwana mata ina ba ku shawara da ku dage ku iya girki, domin yana da muhimmanci matuÆ™a a rayuwar ma'aurata. 

(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Subhanak Allahumma Wabi Hamdika Ash Hadu Anla Ila Ha Illah Anta Astagfiruka Wa Atubu Ilaika. 

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. 

•┈┈••✾•◆❀◆•✾••┈┈•
      Haiman Raees 
•┈┈••✾•◆❀◆•✾••┈┈•

         08185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @HaimanRaees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Haimanraees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook: Haiman Raees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Haimanraeesposts
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Haiman Raees 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────

Miyan Bhai Ki Daring 

2 Comments

Post a Comment