JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 16

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 16 
.


ZAKARIYYA AS
Shi ma annabi ne daga cikin annabawan banu Isra'ila, an fadi danganensa inda ya qare ga Suleiman bn Daud AS, Allah SW ya turo shi ne cikin banu Isra'ila don kira zuwa ga kadaita shi, da bauta masa shi kadai da barin waninsa, a lokacin da barna ta yi yawa da kafurci, fasiqanci ya watsu a ko'ina, ga zalunci da munanan ayyuka da suka mamaye su, a lokacin sarakunan banu Isra'ila kafurcin ne da fajirci kadai a gabansu, ba abinda suka qi jini kamar addini da masu bautar Allah, shi ya sa ma suka abka wa muminai da kisa da zalunci.
.
Annabi Zakariyya ya yi zamani ne a lokacin da musluncin ya yi rauni ba shi yake jagoranci ba, ya yi fama da su sosai, har ya zo yana tunanin halin da zai shiga in ya bar duniyan, Allah SW ya fado abinda yake cewa {وَإِنِّي خِفْتُ الْمَوَالِيَ مِن وَرَائِي وَكَانَتِ امْرَأَتِي عَاقِرًا فَهَبْ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيا*يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنْ آلِ يَعْقُوبَ وَاجْعَلْهُ رَبِّ رَضِيًّا} (Haqiqa ina tsoron masu zuwa a bayana ga matata ba ta haihuwa, ka ba ni majibanci. Da zai gaje ni ya gaji dangin Yaquba ya Ubangiji ka sanya shi ya zama amintacce).
.
MATAR IMRANA
Mijinta mai bautar Allah ne sosai, ya sa matarsa ma mai addini ce, a lokacin da ta sami cikin ta riga ta girma, duk da haka ta yi alqawarin sanya dan da za ta haifa a mabautarsu don ya yi wa addini hidima, to sai dai da haihuwar ta zo sai aka sami mace, baqon abu ne a ce mace na hidima a wurin bauta don aikin maza ne, duk da haka ta ba da ita don ta cika alkawarinta, da yake mahaifin bawan Allah ne kuma shugabansu sai ya zamanto kowa na son ya dauke ta.
.
Don yana ganin shi ya cancanta da haka ko kuma dama ce gare shi tunda ba mahaifinta, da sulhuntawar ta gagara sai a ka yi matsaya kan yin quri'a, wajen yin quri'ar ne ya fito wa Zakariyya AS cewa shi ya cancanta ya riqe ta, wannan yarinya ba wata ce ba illa Maryam AS, mahaifiyar Isa AS, annabi ne kuma manzon Allah, haka Zakariyya AS ya raine ta, ya ba ta cikakkiyar tarbiyya ta gidan annabci.
.
Allah SW ne ya san hikimar da ya sa ta taso a gidan annabta da tarbiyyar annabin Allah kuma manzonsa, har zuwa lokacin da ta girma a wannan halin, shi kam Allah SW bai ba shi haihuwa ba, amma yana ganinta yana jin dadi, duk lokacin da ya shigo wurinta ya ganta da nau'ukan abinci sai ya tambaye ta inda ta samo ita kuwa sai ta gaya masa cewa daga wurin Allah ne, daganan sai ya roqi Allah ya ba shi haihuwa.
.
Allah maji roqo ya ji addu'arsa ya kuma azurta matarsa da d'a namiji wanda suka sanya masa suna Yahya, shi ne ya zamanto Annabin Allah daga baya, amma shi Zakariyya wato (Zachariah) AS ya ci gaba da kira musu Allah duk da ba sa so, tarihi ya nuna cewa shi ne fitaccen manzo na farko cikin manzannin da Qur'ani ya kawo qissoahinsu wanda kafurawan banu Isra'ilan suka kashe.
.
YAHYA AS
Annabi ne daga cikin annabawan banu Isra'ila, shi ma mahaifinsa manzon Allah ne, kamar dai Suleiman AS da Yusuf da Ya'qub da Ishaq, sunansa a Ibriniyance Yohana, da Turanci John, mu kuma da Larabci mu ce masa Yahya AS, in ka lura da zuwar Yahya AS za ka ga cewa wata shimfida ce ta zuwan Annabi Isa AS, domin banu Isra'ila sun saba da ganin manzanninsu a manyan shekaru kimanin arba'in, sai ga Yahya AS ya zo da qaramin shekara, Allah SW ya ce {يَا يَحْيَىٰ خُذِ الْكِتَابَ بِقُوَّةٍ ۖ وَآتَيْنَاهُ الْحُكْمَ صَبِيًّا} (Yahya ka riqi littafin da qarfi, muka ba shi hukunci yana qarami) wasu malaman tafsiri suna cewa da ga shekara 3-7.
.
Akwai addinin Sa'ibanci da ake cewa su ba Kiristoci ba ba Yahudawa ba, suna bin Yahya AS ne, koda yake sun yarda da annabawan da suka gabata amma suna jayayya da annabawan da suka zo bayansa, an fi samunsu a tsakankanin Iraqi, Turkiya da qasashen Sham, rukunnan addinin sun hada da Tauhidi, wanke zunubi a ruwan kogi, azumi, akwai alwala da salla, sai alwalan ana wanke gwiwa a dan zuba ruwa a kan qafa, an sami sabani game rasuwarsa, wasu na cewa kashe shi aka yi kamar yadda banu Isra'ila suke yi wasu ke cewa rasuwa ya yi.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)