TUN KAFIN AURE 43

TUN KAFIN AURE💐43




Kwanansu hudu da dawowa bayan sunyi sati uku a kasa mai tsarki Hafsi ta taje kano tayi sati biyu. Sun sha hira da ummati ta fada mata halin da take ciki. Gashi dai ta kara kyau ga hutu amma babu nutsuwa a tare da ita. Bikin dake gabanta ne duk yasa ta dan manta da halin da take ciki. Ansha shagali don ummati ita kadai ce mace a gidansu. Duk kayan da ta saka da ma wasu abubuwan Hafsi ce  tayi mata. Idan aka tambayeta mijinta kuwa sai tace yayi tafiya ne. Haka suka sha biki aka kai amarya gidanta. Bayan an gama biki Alhaji ya turo mata da kudin jirgi tana zuwa mota na jiranta suka wuce gidan Nafisa.

Ya kusa rabin awa yana jiran Imi a kofar super market din sai ga Tanimu  wanda yazo gidansu a matsayin baban Tilly yana bin wata mata da kaya niki niki a baya. Tabbas shine don ga uku ukun bakinsa nan. Rufe motar yayi ya fito ya karasa inda Tanimu yake shirin lodawa matar kaya a booth dinta. Assalam alaikum....ai kafin kace kwabo Tanimu ya zura da gudu don kuwa ko a mafarki baya jin zai manta wannan fuskar. Ita kuwa matar kyawun Junaid duk ya dauke mata hankali kana ganinta kasan tana da aure. Wani fari ta rinka yi masa da ido da kwarkwasa. Hafsi ce ta fado masa, gabansa ya fadi. Ya rasa dalilin da yasa baya iya bude bakinsa ya nemeta ko ma yayi zancenta. Hango Tanimu yayi zai tsallaka titi ya bishi da gudu. Wuyan rigarsa ya kama ya fizgo shi. Tanimu duk ya gama rudewa don bai manta yadda senator yace zai iya sa a batar dasu idan suka yi masa karya. Gwiwoyinsa a kasa ya daga hannu sama yallabai kayi min rai wallahi sani suka yi. Junaid yace meye alakar ka dasu? Ya cigaba da magiya faci nake a tsallaken titin gidansu kuma ina hada su da  maza. Dama dai yasan matan banza ne amma dai baiyi tunanin iyayen karya ta kawo ba. Sam baya jindadin rayuwarsa yanzu kullum jinsa yake kamar an kulle shi a cikin kwai. Imi yaji ya taba shi ya Juni meke faruwa ne? Junaid ya kalli Tanimu dake zaune gabansa ya fadawa Imran ko shi waye. Imran ya kira waya ba dadewa ta shiga suna zaune police biyu suka zo yace a tafi da Tanimu har ya fadi inda sauran suke. Yallabai ai ba sai an dake ni ba muje na nuna muku su duk abokai na ne. Keyarsa suka tasa a gaba suka tafi shi kuma Imi ya dawo motar junaid ya zauna. Wai meyasa kaki yarda mu hadu a gidanka ne? Wani zafi jikinsa yake yi yace Imran ina cikin problem sosai, wallahi na tsani rayuwata. Ba abinda ke min dadi....yanzu fa ina shiga gida da naga matar nan babu abinda nake so kamar kusantar ta. Tun ana abu da marmari yanzu ya koma kamar cin tuwo. Ita kuma idan ba kudi ta gani ba ta rinka gara ni kenan. Imran yace ai laifinka ne, tun a wurin bikinka nace ka barni nayi maganinta kaki. Yanzu kuma gaskiya na tuba...junaid yayi yar dariya Allah Ya kara shiryamu. Amin dan uwa...ai in fada maka wata shegiya ce. Au wallahi na tuba fa. Hmmm yarinya na dauko bayan an gama abu sai da nayi kwana biyu  bansan inda kaina yake ba saboda na kasa fitsari. Wani mugun ciwo tasa min in takaice maka labari sai da aka yi min aiki a Germany. Abinda ya gabata Allah Ya yafe mana amma ni da mace sai matata insha Allah.


Batul Mamman💖
Post a Comment (0)