TUN KAFIN AURE 42

TUN KAFIN AURE💐42




Sau uku tana katse wayar tare da yin tsaki. Ya kalleta fuskar nan babu fara'a. Ya rasa dalilin zamansa da ita don ko kadan baya sonta. Bashi da sukuni indai ba kusantarta yayi ba shiyasa take gara shi sosai. Parties kala kala yake dawowa ya tarar ta shirya a gidan samari da yan mata su taru su hole. Idan yayi magana kuwa ranar sai ya kusa kuka zata bashi hakkinsa. Yana dai zuwa gaida iyayensa idan ta gadama amma zancen Hafsi tace ko zuci yayi zata sani kuma tayi rantsuwa ranar sai dai hawayensa su kare bazata bashi kanta ba.

Kallon wayar yayi waye ke kiranki? Mtsw rosie ce duk ta dame ni tana son na taimaka mata da kudi. Ina wanda na baki last week baki bata bane? Ta kara yin tsaki kasan gayyar tsiya na rasa me take da kudin. Yace to bari idan na fita zan kawo ki bata. A ranta tace kyayi kya gama bazan bayar ba don yanzu kam yadda yake yawan hade mata rai tasan magani ya fara ja baya kuma da kunya ta koma gidan rosie. Wata biyu rabon da taje kudin da take karba ma account dinta yake shigewa..

Rosie ta kalli wayarta da katon cikin dake gabanta. Kudin abinci ma yanzu gagararta yake amma Tilly taki taimakonta. Gidan da ta tare ma bata sani ba bare tabi sawu. Shawara daya ta yanke ta neme malaminta a warware abinda takewa Junaid ya dawo hayyacinsa ya koreta.

A kasa mai tsarki hafsi da sauran iyalan senator Rufai Bukar sun dage da yawan sallah da adduoi don nemarwa Junaid shiriya. Shi kanshi senator da ya dage da istigfar ba karamin mamaki yayi ba yadda yake jin canji game da al'amuransa. Idan Junaid ya dawo garesu dole su koma a nemi ilimin addini sosai.idan da asiri a jikin junaid to harda sakacinsa ta bangaren addua.



Batul Mamman💖

Post a Comment (0)