ALLAAH YA LA'ANI SHAIƊAN

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
 *ABOKIN FIRA * 
 *Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
 
 *DRS NA 003* 
 *Allah ya La’ani Shaidan*
Wani mutum ne aka yi a wani gari. Kullum abokansa sai su
la’ani Shaidan, shi kuma yana kushe su. Yana cewa, me ya yi maku? Wanda ba ku taba ganin sa ba balle ku ce ya cuce ku! Ana haka watarana sai ya yi mafarki. Ya yi mafarkin ya hadu da
Shaidan a wata unguwa. Shaidan ya gode masa bisa kariyar da yake ba shi. Ya kuma taya masa cewa, ya zo ya rakashi zuwa wani gari ta cikin sararin samaniya. Shedan kuwa ya goya shi
suka shilla zuwa sama. Can suna cikin tafiya sai ya ji fitsari yana damun sa. Sai ya roqi Shaidan ya dan saurara ya sauka ya yi fitsari. Shaidan ya ce, haba! Kai ba abokina ne ba? Mene ne matsala don ka yi fitsarinka a kan bayana? Sai ya ce, ai ba zai yiwu ba. Shaidan ya lallashe shi har ya amince ya kwarara fitsarinsa. Yana gamawa sai ya farka, ya tarar duk ya jike shimfidarsa da fitsari. Buda bakinsa sai ya ce,” Allah dai ya la’ani Shaidan”.

 *Darasi:* Shaidan makiyinmu ne bayyananne.

📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G 
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.


Post a Comment (0)