DOMIN IYALI




DOMIN IYALI 

Aksarin ma'aurata a Arewacin Nigeria sun dauka cewa, aure ba komai ba ne face jima'i da tara zuri'a. Hakan ne ma ya sa:

1. Yana da wuya ka ga ma'aurata suna sumbatar juna a goshi koh a kumatu, kuma idan ka ga sun rungume juna, toh labari mai dadi ne ya samu. 

2. Yana da wuya ka ga miji yana baiwa matarsa abinci a baki, Idan ka ga hakan kuwa toh ka tabbata matar ce bata da lafiya.

3. ldan ba a drama ba, zai yi wuya ka ga miji ya bude wa matarsa kofar mota.

4. Abu guda daya da yake sanya magidanci a Arewa ya taba wuyan matarsa shine lokacin da take korafin zazzabi yana damun ta, ba zai kuma kara tabawa ba sai wani sabon zazzabin ya zo. 

5. Lokaci daya ne za ka ga miji ya dauko matarsa a hannu, lokacin kuwa shine idan ta fara labour (nakuda) zai kai ta asibiti.

6. ldan ka ga ma'aurata na zaune a waje da daddare, kada ka dauka tsabar soyayya ce, fiya-fiya suka watsa a dakin suna jira warin ya ragu.

7. Yawancin mata idan ka ga sun sayawa mazajensu wani abu kyauta, toh ka tabbatar an kwantar da mazajen ne a gadon asibiti, sannan ne mai tausayi za ka ga ta sayi lemo da ayaba.

8. ldan ka ga ma'aurata suna tsere-tsere, toh ka tabbata abin tsoro suka gani kowa yana ta kansa.

9. ldan ka ga ma'aurata tare sun fito da yammaci suna tafiya, ba wai shawagi suka fito ba, yawanci togacciya za su kai na wani da ya duki É—an su. 

10. Lokaci daya ne suke wanka tare, ldan zasu fita aiki ya zamana duk sun yi latti.

11. Lokaci daya ne mace ke kallon idon mijinta dab da dab, lokacin da ya nemi taimakon ta don wani abu da ya faÉ—a cikin idanun sa.

MAFI BAN HAUSHI KUMA SHINE:

Idan aka yi sa'a miji ya zama mai bawa iyalin sa kulawa, sai ka ji jama'a suna cewa : Ai mijin Hajiya ne, Bawan Dudu, koh kuma ta gama dashi, ƙarshe ma ka ji ana kiran sa da "Mijin tace".

Baki daya an dauki aure tamkar azaba, abin da ake yin sa domin jin dadi. Allah ya ganar da gidadawan ma'aurata, Amin.
Post a Comment (0)