Domin Yara

DOMIN YARA
Misalin karfe tara da minti arba'in, na safiyar ranar wata Laraba. Maman Abba na zaune tana wanke-wanken kwanoni, bayan ta gama sharar gida, sai ga danta Abba, dan kimanin shekaru tara da haihuwa, ya dawo daga makarantar firaimari. Yana goye da jakar littattafansa a baya, ya shigo yana kuka.
Mamarsa ta tare shi da sauri, ta zaunar da shi, tana tambayarsa daliln da ya sa yake kuka, ta ce, "Wa ya bugar mini Abbana? ko faduwa ka yi? Na sha fada maka ka daina gudu da yawa."
Abba ya share hawaye ya dubi mahaifiyarsa yana sheshekar kuka ya ce mata, "Bayan almajiran makarantar Malam Dudu, inda muke zuwa karatu da dare, suka tare ni yanzu suna ce mini, wai ni dan wuta ne tunda ina zuwa makarantar boko, Audu yana ta yi mini gwalo yana dariya, shi kuma Bala ya zungure ni."
Mamman Abba ta dafe kirji cikin mamaki, domin dai ta nuna wa danta damuwarta a fili, sa'annan ta ce, "Su Audun da Balan suka buge ka? Ai kuwa ba zan kara ba su abinci ba idan suka zo bara."
Abba ya kara zumbure baki yana cewa, "Kuma kullum in mun taso makaranta sai su yi ta yi mini waka suna cewa, 'Dan makarantar bokoko, ba karatu ba salla, sai yawan zagin malam'."
Maman Abba ta shafa kansa, ta ce, "Kyale su, bari idan Babanka ya dawo in fada masa, ya je ya fada wa Malaminsu, yau sai sun sha kashi. Ba mai kara jan ka cikinsu."
Abba ya yi murmushi ya ce, "Yawwa Mama, a ba su kashi sai sun yi kuka." Ya kwance jakarsa daga bayansa, ya rike ga hannu. Ya kuma duban Mahaifiyarsa ya ce, "Wai Mama da gaske ne Allah ya hana yin boko? Kuma wai duk wanda ya yi karatun boko idan ya mutu sai an sa shi wuta?"
Maman Abba ta yi dariya, ta ce, "A'a, wannan karya ne. Allah bai haramta neman ilimi ba kowane iri ne, muddin dai ba zai raba ka da yin addininka ba. Masu irin wannan ra'ayi, na haramta karatun boko, suna da nasu dalilai, sai dai dalilai ne da suka yi wa bahaguwar fahimta.

A cewarsu, boko haramun ne, tunda ana hada maza da mata wuri daya, kuma ana koyar da abin da ya saba wa koyarwar Alkur'ani mai tsarki, kamar yadda ake yin ruwan sama, da yadda duniya da halittu suka samo asali, da duba a kan abin da zai iya faruwa gobe, ko wata mai zuwa, ko ma shekaru masu zuwa.
Masu wannan ra'ayi sun manta cewa sau da yawa kisan kai yakan kawar da rotse. Watau idan sun ce ba za su yi karatun boko ba, saboda ana hada maza da mata wuri daya, me ya sa suke shiga mota maza da
 mata a yamutse? Me ya sa idan suka kai matansu asibiti maza ke duba su? Ina ce ko a Makka, akwai inda maza da mata ke cakudewa wurin aikin hajji. Saboda haka haduwar maza da mata lalura ce, wadda ba za ta hana musulmi yin karatun boko ba. Sauran fannonin da suka saba wa Alkur'ani mai tsarki a karatun boko kuwa, ai ba cewa aka yi dole sai musulmi ya yarda da su ba, karanta su ne dole, domin cin jarabawa, ba yarda da su."
Maman Abba ta takarkare tana ta yi wa danta bayani, kamar mai magana da babban mutum, da ma tuni tana cike da takaicin masu irin wannan ra'ayi. Shi kuwa Abba kallonta kawai yake yi, kamar mai kallon sabuwar mahaukaciya, bai san inda zancenta ya dosa ba. Ita kuwa ta ci gaba da bayaninta, Ba ruwanta da dan nata, ko yana fahimta ko baya fahimta, burinta kawai ta amayar da abin da ya dade yana damunta a rai. "Idan Musulmi ba su yi karatun boko ba, wa zai zama likita a cikinsu? wa zai zama soja? Wa zai zama Dan sanda? Wa zai tuka musu jirgin sama? Wa zai....."
Kafin ta karasa abin da za ta ce, da Abba ya ji ta ambaci jirgin sama, sai ya yi farat ya katse ta da tambaya, "La, Mama da ma sai mutum ya yi boko zai iya tuka jirgin sama?" Maman Abba ta ce, "Kwarai kuwa, sai da ilimin boko ake iya tuka jirgi." Abba ya yi dariya cikin murna ya ce, "Mama idan na gama karatuna, tukin jirgin sama zan yi. Kullum in zan wuce zuwa Makka, zan biyo ta saman gidan nan, in leko da kaina in daga muku hannu, ke da baba. Kuma in bi ta saman makrantar Malam Dudu in leko in yi wa su Audu da Bala gwalo in wuce." Maman Abba ta fashe da dariya, ta ce, "To, Allah ya nuna mana lokacin. Tashi ka dauko abincinka, ka ci ka koma makaranta, ka ga har karfe goma ta kusa yi, kada ka makara a yi maka bulala."
Abba ya shige daki domin cin abinci, ita kuma Maman Abba ta koma wurin wanke-wanke, tana tunani a cikin ranta, "Mhm! Yaro ba mutum ba, sai ya girma. Hakika masu ra'ayin cewa karatun boko haramun ne, suna jawo wa al'ummarsu babbar illa. Idan har muka yi sake 'ya'yanmu suka watsar da neman ilimin zamani, lallai su da jikokinsu, za su zama bayin 'yan kudancin kasar nan, masu neman ilimin zamani ido rufe, ta hanyar mamaye dukkan ma'aikatu, da masana'antu, da madafun ikon kasar nan. Allah ya ganar da su illar wannan ra'ayi nasu." Ta ci gaba da wanke-wankenta.
© Waziri Aku 2013
http://fb.com/waziriaku
Post a Comment (0)