MIYAR OGNO

*👩‍👩‍👧‍👧S.H.D.G STARS*👩‍👩‍👧‍👧


*_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV&GENTLE)._*



*14/8/2018.*






*MIYAR OGNO*






*Ingredients:-*


* Nama
* Kifi danye da busasshe
* Ogbono
* Ganda
* Kayan miya
* Man ja
* Maggi da gishiri
* Curry da tafarnuwa
Preparation:
Ki tafasa namarki da gishiri, tafarnuwa, albasa, ki soya man ja amma kadan, ki zuba markadadden kayan miyarki a kai, su ma ba da yawa ba, idan ya soyu sai ki zuba dakakken crayfish kamar cokali biyu, ki zuba busasshen kifinki da kika gyara, ki zuba ruwa a kai, idan ta dahu sai kisa baking powder kadan dan tayi yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura, shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti biyar ko goma shike nan kingama miyarki.😋






*MIYAR SHUWAKA*

*Ingredients:-*

* Nama
* Shuwaka
* Busasshen kifi
* Albasa
* Tafarnuwa
* Kayan miya
* Thyme da curry
* Maggi da gishiri
* Man ja
Preparation:
Ki wanke shuwakarki idan ba kya son dacin da yawa, sai ki dinga murje ta kina mutsittsike ta kina tace ruwan da rariya, sai kinyi kamar sau biyar ko sau shida, in kuma kina son dacin sosai sai ki wanke sau biyu ki tafasa namarki da thyme, da albasa da tafarnuwa da gishiri, ki zuba markadadden kayan miyarki da soyayyen man janki a kan tafasasshen namanki, idan ya dahu kamar minti bakwai, sai ki zuba shuwakarki, da gyararren busasshen kifinki, da yankakkiyar albasarki, da maggi, gishiri da curry, ki rufe tayi ta dahuwa, ba'a so tayi ruwa anfi sonta sa kauri.😋



~S.H.D.G~



*_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV&GENTLE)._*
Post a Comment (0)