FASSARAR WAƘAR MAIN QAIDI NUMBER 796

Fassarar Waƙar Main Qaidi Number 796

* Sunan Waƙa - Main Qaidi Number 786 (Poem)

* Sunan Fim - Veer-Zaara

* Shekarar Fita - 2004

* Rubutawa - Aditya Chopra

* Sunan Kamfani - Yash Raj Music

* Rerawa - Shah Rukh Khan

* Mai Fassara - Haiman Raees

MATASHIYA

Waɗannan Kalamai da zaku karanta su ne Kalaman da Jarumi Shah Rukh khan ya furta a kotu yayin da Alƙali ya tambaye shi ko yana da abin faɗa. A ciki zaku ji yadda ya bayyana kansa a matsayin sa na Fursuna mai lamba 786 da kuma yadda ya ɗauki duniya. Sannan yayi jawabi dangane da Saamiya wacce ita ce lauyar sa da Ƙasar su ta India da kuma Masoyiyar sa Zaara tare da wasu muhimman abubuwa.


* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Din, mahiney, saalon ko yug mein badalte dekhta hoon

Yayinda Ranaku, Watanni da shekaru suke Canjawa izuwa ƙarnoni

* Is miti se mere bauji ki kheton ki khushbu ati hai

Daga Ƙasar nan da nake, ina iya jiyo ƙamshin gonakin mahaifina

* Yeh dhoop meri matti ki thandi chaas yaad dilati hai

Wannan hasken ranar kuma yana tuna min da irin abincin Mahaifiya ta

* Yeh baarish mere sawaan ke jhoolon ko sang sang lati hai

Wannan ruwan saman kuma yana tafe ne da iskar damina

* Yeh sardi meri lodi ki aag sikh ke jati hai

Wannan lokacin ssnyin kuma yana tuno min wutar da akan kunna a kowane daren Lodi.

* Woh kehta hai yeh tera desh nahi

Sun faɗa mini cewa nan ba ƙasa ta bace

* Phir kyun mere des jaisa lagta hai

To ya aka yi kuma take kama da tawa? (Ƙasar)

* Woh kheta hai mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin su bane

* Phir kyun mujh jaisa woh lagta hai

To ya aka yi kuma suke kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Sapno ke gawn se utri ek nani pari ko dekh ta hoon

Naga wata ƴar aike Yayinda da ta fito daga ƙauyen Mafarkai

* Kehti hai khud ko Saamiya aur mujh ko Veer bulati hai

Ta kirayi kanta da Saamiya sannan ta kirani da Veer

* Hai bilkul begani paar apno si zid woh karti hai

Ita Cikakkiyar baƙuwace a gare ni amma tana faɗa a kaina tamkar dama can ta daɗe da sani na

* Uski sacchi baaton se phir jeene ko maan karta hai

Jin Kalaman ta na gaskiya yasa naji cewa ina sake rayuwa a raye

* Uske kaasmon vado se kuch karne ko maan karta hai

Jin alƙawuranta yasa naji ya kamata inyi wani abu mai nagarta

* Woh kehtay hain ke woh koi nahi hai

Sun faɗa mini cewa ita ba kowa bace a gare ni

* Phir kyun woh mere liye duniya se ladti hai

To me yasa kuma take faɗa da duniya saboda ni?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Mere gaon ke raango mein lipti ek nayi Zaara ko dekhta hoon

Inda daga cikin kala a cikin Kaloli naga Zaara

* Mere khwabon ko pura karte khud ke khwab bhool chuki hai woh

(Wacce) Saboda ta cika Mafarkaina ta manta da nata (Mafarkan)

* Mere logo ki sewa karte apne logo ko chhod chuki hai woh

(Wacce) saboda yiwa jama'a ta hidima ta bar nata (jama'an)

* Uska daaman aab khushion se bharne ko jee karta hai

Ina ma ace zan iya sake cika mata rayuwarta da dukkan wani farinciki

* Uske leya ek aur zindagi jeene ko jee karta hai

Wa ita, zan so na sake rayuwa a raye

* Woh khete hai ke mera desh uska nahi

Sun faɗa mini cewa nan ba Ƙasar ta bace

* Phir kyun mere ghar woh rehti hai

To me yasa take zaune cikin ahali na?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama

* Woh khete hai ko woh koi nahi teri

Sun faɗa mini cewa ba mu haɗa komai ba da ita

* Phir kyun woh mere liye duniya se ladti hai

To me yasa kuma take faɗa da duniya saboda ni?

* Woh kehte hai ke mein us jaisa nahi

Sun faɗa mini cewa ni ba irin ta bane

* Phir kyun mujh jaisi woh lagti hai

To me yasa kuma take kama da ni?

* Main qaidi number 786 jail ki salaakhon se bahar dekhta hoon

NI, Fursuna mai lamba 786, ina kallon Waje daga cikin ɗakina da ke Magarƙama


<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)