GASKIYAR ZANCE 02

*GASKIYAR ZANCE 002 👌*


Cikin daruruwa da dubunnan matan da ake da su a gari, ga su nan birjik iya ganinka, mai yiyuwa ma a gidansu akwai 'yan mata wadanda babu abin da kika fi su, ga classmates dinshi nan birjik wadanda suka yi karatu tare, amma duk da haka ya ketare wadannan matan ya za6o ki domin ki zamo abokiyar rayuwarsa, ya yarda ki zamo uwar 'ya'yansa, ya aje ki a gidansa be gudun ki san dukkan sirrinsa, ya ke fita cikin rana ya yi zufa don ya nemo abin da za ku ci, duk wata fafutuka domin ki ne. To don me ba za ki kasance mai biyayya a gare shi ba.


Mijinki shi ne komai naki, ki kasance mai hakuri da gazawarsa, abin da ya kawo ki amsa ki yi godiya tare da yi masa addu'a da fatan alkhairi, kada ki bai wa kowa damar shiga gidansa sai da izininsa, ki san dukkan abin da yake so, sannan ki san abubuwan da ba ya so don ki kiyaye. Mijinki yana da girman hakki a wajenki fiye da kowa, don haka ki yi kokari ki samu aljannarki ta sanadiyarsa.


Mijinki aljannarki 'yar uwa! Ki nemi ilimin rike abinki, kada ki bari wasu can a waje su rude shi. Sannan ki dinga bibiyan yadda matan Annabi (ﷺ) suka mu'amalance shi.
.
.
Ya Allah Ka hada mu da mata nagari 👏🏼



*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*


*🕌ISLAMIC POST WHATSAPP.*
Post a Comment (0)