*GASKIYAR ZANCE 👌*
Zaune take a gidan iyayenta cikin walwala, lumana da kwanciyar hankali, ba rashin ci babu rashin sha, ba rashin sutura ballantana matsuguni. A koda yaushe tana kallon iyayenta tana kara samun sakewa, tana ganin 'yan uwanta tana samun nishadi, ba ta rasa komai ba na daga kulawa daga wajen iyaye da 'yan uwa, sun ilimantar da ita, sun ba ta tarbiyyar da ya dace gwargwadon iyawarsu. Tun tasowarta ta taso ne a cikin iyayenta da 'yan uwanta, idan ta shiga damuwa za su share mata hawayenta. A lokaci daya ka zo ka kwallafa ranka a kan sai ka aure ta, iyayenta suka yarda suka ba ka ita ba don sun gaji da ita ko don sun rasa abin da za su ci gaba da yi mata hidima ba, ita ma ta amince ta bi ka gidanka ta ci gaba da rayuwa da kai, ta sadaukar da debe kewar iyayenta da 'yan uwanta don saboda ta rayu da kai, ta amince ta zama uwar 'ya'yanka, ta yarda ka san inda babu wanda ya sani a jikinta, ta yarda ta kare rayuwarta a gidanka, ta yarda ta zamo mai hidima a gare ka. Shin wadda ta yi irin wannan sadaukantakar ta cancanci kulawa ne ko wulakanci?!
.
Dan uwa wannan wani description ne na matarka, a koda yaushe ka dinga tunawa da irin halarcin da ta yi maka kafin ka hakaito wani aibinta. Matarka na tsananin bukatar kulawarka, tana son ka, sai dai kuma tana da rauni a wasu wajajen, to me zai hana ka mu'amalance ta da kyautatawa, tausayawa tare da tausasawa? Meyasa za ka yi mata tsawa ko ka zage ta, meyasa iyayenta suka zama abin zagi a wajenka bayan jajircewa da suka yi na rabuwa da wani bangare na jikinsu? Meyasa za ka muzanta mata ta hanyar danne mata wasu hakkokinta? Meyasa ka rabo ta da iyayenta idan ba ka shirya sauraron matsalolinta ba?
Ya kai dan uwa mai daraja! Ka sani, *hakuri* wani laqani ne na cin ma dukkan wata bukata wanda ba a ta6a jaraba shi aka samu faduwa ba. Haquri babban jigo ne na kyautata mu'amala da assasa zaman lafiya, walwala da nishadi tsakanin ma'aurata.
Ka dauki aure ibada, Sannan ka nemi sanin yadda za ka kyautata zamantakewa da iyalinka.
Mace abar tausasawa ce, domin ta kasance wani bangare na jikinmu. Ka yi hakuri da da'ifancinta, ka nuna mata soyayya, ka Qaunace ta kamar a ranar da ka fara ganinta, ka so ta saboda Allah don neman yardarsa....
.
Ya Allah Ka hada mu da abokan zama masu addini da kyawawan dabi'u 👏🏼
Qaninku a har kullum:
*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
*🕌ISLAMIC POST WHATSAPP.*