HANYOYIN MAGANCE MATSALAR YAWAN SHA'AWA

HANYOYIN MAGANCE MATSALAR YAWAN
SHA'AWA



Salamun alaikum
Inaimana fatan alheri
Yamukaji da zafi? ALLAH yanunamana wucewa lafiya.
Akwai wani group na matasa maza da mata marubuta
Sun nemi da nagabatarda lecture adaren yau akan hanyoyinda marasa aure zasubi dan kaucewa ko rage matsalar sha'awa
Dafarko dasukanemi cewa inyi bayanin nadanji dummmm daga baya bayan nafara bincike hakika naga muhimmancin lamarin
Domin bawai marasa aure ne kawai ke famada wannan matsala ba har wasu masu auren suna samun kansu acikin irin wannan matsanan cin halin na yawan sha'awa
Masana ilimin jinsi sunakiran wannan matsala da suna ﺍﻟﺸﻬﻮﺓ ﺍﻟﻤﻔﺮﻁ
Wato sha'awar da ta wuce misali
Eh! Hakika duk mai rai mutum ko dabba indai lafiyayyene ana bukatarsa da sha'awa
Rashin sha'awa kwata kwata cutane
Idan kuma ta tsananta nan ma matsalane
Dabi'a mafi kyau kakasance a tsaka tsaki
Atakaice duk mai fama da wannan matsala ta tsananin sha'awa yakamata yanemawa kansa mafita ta hanya mekyau dan yasaita kansa yazama daidai da sauran jama'a
Akwai sinadarai dasuke saita dabi'ar jiki musamman akan wannan bangare damuke magana akai.
Daga cikin sinadarai da nagamsu dasu ga kadan daga ciki
YANSUN DA NA'ANA'A
shan kofi 2 arana zai taimaka maka wajen rabuwa dayawan sha'awa
But ko kana ko kinada yawan sha'a indai amare ne to karku takura shan shayin na'a na'a
Akwai sinadaranda lallai amare ba'aso suna ci saboda Tsaro.
BARDAQUS
shima tsiro ne dayake taimakawa wajen ragewa Dan Adam sha'awa ana tafasashi kafin akwanta asha kofi daya.
KAFFU MARYAM
itama wannan ciyawa ce datake taimakawa me yawan sha'awa zata ragu
.
TSAMIYA
tana taimakawa itama wajen kashe sinadaran sha'awa ajikin Dan Adam.
saikuma uwa uba KAFUR OIL
Yafi duk wadannan cire sha'awa anashansa a tea
Akwai kuma tiraren
Wannan yanahana daukar ciki idan aka shaqashi to aranar dai ciki bazai shiga ba
Danhaka abarshi muwuce gaba
Koda yake akwai kuma shawarwari da yakamata masu irin wannan su dinga bi
Dayawa wasu matan koda sunada miji rashin lafiyarsa zata'iya jawo rashin sukuni ga'ita matar
Baduk namijine ke iya biyawa iyalinsa bukatunsu ba
Kamar yanda baduk mace itama take iya share hawayen oganta ba
Koda yake wannan lecture kawai dan marasa aure ne bawai akan masu aure ba
SHAWARA GA MASU YAWAN SHA'AWA
*Duk me fama Da matsalar sha'awa yaguji kawaye ko abokai marasa da'a
*Yaguji karanta Labaran batsa ko kallon hotunan batsa ko video na batsa
*Kalizimci damuwa damuhimman ayukka
*Daukar kaya masu nauyi ko aikin wahala duk suna taimakawa wajen cire sha'awa
*kai kokarin yin aure.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100

1 Comments

Post a Comment