Hattara Iyaye Da Mazaje

*Hattara Iyaye da Mazaje*

✍ *Dr.Mansur Sokoto*

Na kalli wani faifan video da ake watsawa na wani karatu mai ban tausayi da ban takaici hade da mamaki. Ba zan iya tura ma kowa shi ba. Amma ina son in yi wata fadakarwa a nan.
- Ya zama wajibi mu kula da yayanmu tun suna kanana; mu koya masu addini. Ina amfanin mutum ya girma yana jahili?
- Mazaje su binciki karatun iyalansu. Allah zai tambayi kowane magidanci akan karatun iyalansa.
- Ba a girma ga yin karatu, ba a tsufa ga neman sanin addini. Don Allah duk wanda ya san akwai bukatar gyaran karatun sallarsa ya/ta nemi malami/malama mai koya masa/mata. A lahira Allah ba ya karbar hanzarin wanda ya ce bai sani ba ko bai iya ba.
- Yan siyasa su daina bayyana wallensu a gaban jama'a ta hanyar kuri da takama da sanin addini alhalin ba su sani ba.
Daga karshe, mu sani, in Allah ya yi uzuri ga mutanen kowane zamani game da jahiltar addini ba zai yi uzuri gare mu ba a wannan zamani saboda hanyoyin karatu sun yawaita sun saukaka kuma sun game duniya.
Allah ya yi muna muwafaqa ya sa mu gyara karatunmu da halayenmu.
Post a Comment (0)