IDAN 'DANKA KO 'YARKA SUN KAI SHEKARUN FARKO NA TASHEN Balaga...

IDAN 'DANKA KO 'YARKA SUN KAI SHEKARUN FARKO NA TASHEN BALAGA, TO KA LURA DA WANNAN:--


1. Duk lokacin da yaro ko yarinya suka kai matakin tashen balaga wato "early adolescence", musamman daga shekara 11, 12 zuwa 13... 18... To wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga yara da iyayensu.

2. A lokacin ne yaro yake samun zama na gari ko na banza, me amfanar da al'umma ko mai cutar da su.

3. Yaro ya fi tasirantuwa da abokansa ko ƙawayenta fiye da malamansa ko mahaifansa.

4. Yaro yana jin shima daidai yake da kowa a duniya, kuma zai iya yin komai kamar yadda kowa yake yi, haka ita ma yariyar.

5. A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon mahaifansa akansa. Yana son ɗakinsa daban, wajen kwanciyarsa da ban, abinci, kayan sakawa da aski sai wanda ransa yake so.

6. A lokacin ne yake jin ƙarfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa. 

7. A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga, ba kan gado babu natsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tinaninsa), idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi/ita
INA MAFITA?
MAFITA:
1. Iyaye su ja yaronsu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi masa gyara da tarbiyyarsa.

2. Kar su nuna masa karfi ko iko, domin zai iya bauɗare musu, a ƙarshe ya haifar musu da hawan jini.

3. A kula sosai da su waye abokansa, ko ƙawayenta. A haɗa shi da na gari, a raba shi da na banza.

4. A samar masa da aikin yi, wajen nuna masa yadda zai dogara da kansa (koda kuwa dan masu kudi ne shi).

5. A tsara masa ayyukan da zai yi a kullun tun daga safe zuwa rana, misali: makaranta, bacci, cin abinci, ziyara, hutu, da sauransu.

6. Iyaye su zama abokan 'yayansu wajen bincikar matsalolin 'yayan, da magance musu ita.

7. Ka da a hana yaro wani abu, face sai a maye masa gurbinsa da wani, idan ba haka ba, to zai yi wanda aka hana shi muni.

8. Kar ayi amfani da ƙarfi, da duka, da tsattsauran hukunci wajen ladabtar da shi, har sai idan abu ya ta'azzara, sai a je da ga malamai na sunnah ,da guidance and counseling domin neman shawarwari.

9. A riƙa tunatar da su ayoyin alqur'ani da hadisan Manzo s.a.w. da tarihin magabata da sukai magana akan biyayyar iyaye.

10. Sannan a hada da addu'ar nema musu shiriya da nagarta a wajen Allah s.w.t.
Allah tarbiyyarta mana 'ya'yanmu da dukkan 'ya'yan musulmi baki ɗaya
Ɗan uwanku a muslinci:
Salisu Ɗahir Abdurrazaq
Post a Comment (0)