ISTIGHFARI YANA JANYO ALKHAIRI DA ALBARKA MAI YAWA SANNAN YANA TUNKUDE BALA'I

ISTIGHFARI YANA JANYO ALKHAIRI DA ALBARKA MAI YAWA SANNAN YANA TUNKUDE BALA'I


Manzon Allah ﷺ baya sabon Allah saboda Allah ya bashi kariya da dukkan sabon Allah,sannan da zaiyi sabon Allah to Allah ya gafarta masa dukkan abinda zai aikata,amma duk da haka Manzon Allah ﷺ yafi kowa yawaita Tuba da Istighafi da komawa zuwa ga Allah.

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Wallahi ina yin Istighfari ina tuba zuwa ga Allah ayini fiye da sau Saba'in....)*

 A wata riwayr yana cewa:-
*(....Ina Tuba kuma ina neman gafarar Allah a yini sau dari...)*

Daya daga cikin Sahabban Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*"Muna kirgawa Manzon Allah ﷺ a wajan zama yana nemi gafara da istighfari zuwa ga Allah sau dari awajan zama guda daya".

Dan haka wajibine ga dukkan kowane bawa mai so da imani da koyi da Manzon Allah ya yawaita tuba da istighfari mai yawa.

Wani mutum ya shiga Wannan Babban Tabi'i wato Imam Hasan Albasary RHA,sai yace:
"Ya Imam Sama ta daina zubar da ruwanta,sai Imam yace;-
*"Kuje ku yawaita yin Istighfari"*.

Sannan wani mutum ya shiga wajansa yace:Ya Imam Matata bata haihuwa,sai Imam yace masa;-
*"Kuje ku yawaita Istighfari mai yawa"*.

Sannan sai wani mutum na ukku yace ;Ya Imam ina fama da Talauci mai yawa,sai Imam Yace;-
*"Ka yawaita yin Istighfari:*sai daya daga cikin Dalibansa yace da shi,Abin mamaki a gareka ya Imam,mutane guda ukku sun shigo suna tambayarka akan abubuwa daban daban amma duka kana basu amsa da su yawaita Istighfari??

Sai Imam Hasanul Basary yace da shi;-
*"Shin baka karanta fadin Allah Ta'ala ba
﴿فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّاراً * يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَاراً *وَيُمْدِدْكُمْ بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَلْ لَكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَلْ لَكُمْ أَنْهَارl)*

Fassara;-
*{"Shi na ce,'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku,lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.""Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki,kuma Ya sanya muku koguna}*

Allah yana cewa:-
﴿وَيَا قَوْمِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَارًا وَيَزِدْكُمْ قُوَّةً إِلَى قُوَّتِكُمْ وَلَا تَتَوَلَّوْا مُجْرِمِينَ ﴾

Fassara;-
*("Kuma,ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara,sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi,zai saki ruwa sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa,kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi)*.
@هود: 52.

الإمام القرطبي رحمه الله -:
Yana cewa:-
*"Yana daga cikin falalar istighfari da Tuba,Allah baku abinda da ya hanaku na ni'imarsa tare da yalwata maku arziqi mai yawa da albarka mai yawa"*.
@الجامع لأأحكام القرآن( 9-2 ).

   Allah ne mafi sani.

*Allah muna rokonka da sunayenka mafiya kyawu da siffofinka mafiya kamala da daukaka,Ya Rabbi Ya Rabbi ya Allah kayi rahama da gafara da afuwa ga dukkan musulmin duniya baki daya masu rai da wadanda suka rigamu gidan gaskiya tun daga Annabi Adam har zuwa yanzu,Amin Amin Amin ya Allah*.
Post a Comment (0)