MALLAKAR MATA

☜MALLAKAR MATA ☞





*✎...1 zuwa 10...
✄ ga ma'aurata domin gyaran aure*

✎① ka zama Mai tsabta da gyaran jiki.
___________________________________________
✎② himmatuwa da biya wa juna bukata.
___________________________________________
✎③ banda duka banda mummunar magana.
__________________________________________
✎④ ka guji rowa ka zama Mai sakin hannu.
__________________________________________
✎⑤ ka guji yawan ganin laifi.
_________________________________________
✎⑥ ka guji bayyana sirrinka a social media tsakaninka da matarka.
_________________________________________
✎⑦ ka guji mummunan zato ga matarka.
_________________________________________
✎⑧ kada ka zama Mai shige da fice a gidanka.
_________________________________________
✎⑨ ka guji saurin tuhumar matarka da wani kuskure.
_________________________________________
✎⑩ siffofin mazajen da Mata suke so.
▃▃▃▃▃▃▃
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
✎・1・✎
❮・KA ZAMA MAI TSABTA DA GYARAN JIKI・❯
_________________________________________
Ya kamata maigida ka zama Mai kwalliya da caba ado ga matarka, kamar yadda kake so itama tayi maka kwalliya da caba ado a gareka.

_Kamar yadda ya kasance Daga koyarwa Abdullahi bin Abbas (R.T.A) cewa shi ya kasance yana cewa:_
*"Ni ina son in yi ado ga matata,kamar yadda itama take so tayi ado a gare ni"*
To,a nan sau tari wasu mazaje sun wajabtawa matansu suyi musu kwalliya da ado, Amma hakikanin gaskiya su mazajen ba sa yi musu kwalliya ko gyaran jikinsu.

To irin wannan lamari shi ke haddasa kiyayya da kyamar miji a wajen mace, domin duk irin son da take yi masa sai ta kasance kwata-kwata taji bata son sa, domin irin bugawar da yake yi na tsamin Dauda da warin baki, sai ta so ina ma ya sake ta.

To ya kamata dan'uwa ka zama Mai kwaikwayo Daga ma'ikin Allah.
*_Domin manzo Allah ( S.A.W ) ya kasance Mai tsabta kuma yana son tsabta._*

Domin yana:
✎ taje gashinsa.
✎ yana tsabtace rigarsa.
✎ yana sa turare.
✎ yana gyaran jikinsa kamar mafi kyan yadda yake

❀ ya kasance yana cewa:
" hakika Allah kyakkyawa ne, yana son Mai kyau. ❀
*_"Tsabta tana Kira zuwa imani"To, a nan mafi muhimmanci tsabta itace tsabta baki da hakora , domin manzon Allah ( S.A.W ) ya kasance yana ba da muhimmanci a kan wanna bangare._*

"Kuyi asuwaki hakika asuwaki Abin tsarkake baki ne, Abin so ne ga ubangiji.

Ka Sani dan'uwa, ba wai yin wanka da tsabta da gyaran jikinka don matarka ta gani kawai ba, a a yin hakan ma wani imani ne a gare ka.
Post a Comment (0)