MUNGO PARK MABUDIN KWARA 20

20. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...


 
Babban mugun halin mutanen wannan kasa daya ne, watau sa idonsu a kan kayana, suna kwadayin sacewa ko yaushe. Amma in an dubi sahihiyar gaskiya, bai kamata ba a zarge su saboda kwadayin kayana, tun da ya ke ko a wurinsu sata babban laifi ne. Kuma babu barayi da yawa a cikin kabilarsu. Saboda haka, kafin mu yi hanzarin kiransu barayi, sai mu duba mu ga in ’ya‘yan banza a kasashen Turai suka sami hanya irin ta mutanen Afirka, ashe su ma ba za su yi wa bako abin da Mandingo suka yi mini game da kayana ba? Sai mu tuna a Afirka Sarakunan kasar babu ruwansu da kiyaye lafiyar bako, al’adarsu kuma ba ta hana wa mutanensu tare bako su kwace kayansa ba. Kayan nan nawa kuma a wurin Bakar Fata darajarsa kamar ta yakutu da lu’ulu’u ne a wurin Turawa. Kamar mutumin Hindu ne ya zo Ingila da jakarsa cike da yakutu, ya rike ta a hannu yana yawo a titi. A ce kuma shari'ar Ingila ba ta hana taba bako ba, kowa ya ga dama yana iya kwace kayansa, ba kome. Ashe zai yiwu mutanen Ingila su bar masa ko fatar jakar ma, balle su rage masa wani abu a ciki? Saboda haka, ni a ganina, ba niyyar mugun abu, ko son sata ya sa Mandingo suka rika washe ni ba. Aikin zuciya ne, wadda ba ta da kashi. Ko da ya ke sun yarda sata mugun abu ne, amma zuciyarsu ta kasa daure bari na da kaya masu kyau wadanda ba su taba gani ba. Kin umumin zuciya kuwa abu ne mai wuya.
In kuma na dubi yadda mutanen su ke galibinsu Arna ne, ba su da wani addini tsattsarka mai tsawatarwa, amma duk da haka sun ji tausayina, sun taimake ni, sai in yaba taushin zuciyarsu. Ba na manta kyautar da Sarkin Sego ya yi mini ta farin kudi, balle fa matar da ta kai ni dakinta bayan na rasa wurin kwana, ta ba ni abinci bayan yunwa ta kusa kashe ni, ta nuna tausayi gare ni, ta taimake ni cikin wahalata, ta fisshe ni daga halakar namun daji !
Abin mamaki kuma shi ne duk cikin tafiyata mata sun fi taimakona da maza. Kwadayi da muguwar zuciya sun rufe wa galibin mazan ido wajen tausayi da imani. Amma ban ga mace guda wadda ta wulakanta ni ba. Saboda haka abin da na gani game da halin Bakar Fata shi ne yana da tausayi, da son taimako, in dai ba ka raina shi, ko ka ci fuskarsa ba.
Bisa ga al'adar Bakar Fata, su kan goya 'ya'yansu a baya, su kan ba su mama sai sun shekara biyu da rabi, ko uku, kana su yaye su. A ganina, wannan al'ada ta goyon shekara uku ita ke hana wa matansu haihuwa da yawa. Galibin iyakar yawan 'ya'ya daga biyar ne zuwa shida. Kadan ne su ke haura haka. Lokacin da 'ya'yansu mata suka girma, su kan koya musu kadi da aike-aiken gida, mazan kuma sai a tura su gona. Da Musulminsu da Arnansu duk suna yi wa yaransu maza kaciya, amma sai sun girma, sun tasam ma shekara bakwai zuwa goma. Arnan su kan yi biki kwarai a lokacin da ’ya’yansu ke cikin kaciya.
Idan saurayi ya ga budurwa yana sonta da aure, ba lalle ne ya nemi yardarta ba, sai iyayensa su shirya da iyayenta kurum. Su za su fada musu kudin da zai biya, saboda raba su da ’yar. Galibin bayi biyu a ke biya, sai ko in yarinyar kyakkyawa ce kwarai. Bayan sun shirya, sa'an nan ne zai yi magana da yarinya. Amma ba lalle ne sai ta yarda ba, don in dai iyayenta sun ci goron da ya kai musu sun yarda ke nan, lalle kuwa a yi auren, ko yarinyar ba ta so. In kuwa ta ki, sai ta zauna muddin ranta ba aure, don ko ta kawo wani masoyi iyayen ba sa yarda.
Mutanen Afirka su kan auri mata da yawa, da Musulminsu da Arnansu. Amma Musulminsu ba su ajiye mata fiye da hudu, Arnan kuwa ba iyaka, gwargwadon arzikin mutum. Maza suna da iko mai yawa a kan matansu, umma duk da haka ba su yi musu azaba.
Bakar Fata ba shi da wata hanya ta raba lokaci. Damina ita ce abin kirgar shekaru. Shekara kuma suna raba ta da wata irin na sama. Da ya ke ba su da agogo, ba su iya ambatar karfe kaza, sai lokaci kaza. Misali, ba su iya ce karfe bakwai, sai wayewar gari, karfe goma hantsi, sha biyu rana tsaka, karfe biyu azahar, karfe hudu maraice, karfe bakwai faduwar rana. In kuwa suna ambaton lokacin da ba ya cikin wadannan, misali tsakanin karfe goma da sha biyu, ko tsakanin karfe biyu da hudu, sai su nuna da hannu daidai wurin da rana ta ke a lokacin da su ke bayyanawa. Na tambaye su ko sun san inda rana ta ke zuwa bayan ta fadi, kuma ko ita mu ke sake gani gobe ko wata ce dabam. Sai suka ga wautata game da wannan tambaya, wai wannan ya fi karfin dan Adam ya sani. Haka wata in ya tsaya, suna zaton wani sabon wata ne aka halitta dabam, har su kan yi addu'a.
A ganina, Bakar Fata bai cika yawan rai ba. Galibinsu su kan fara tamoji a fuska tun suna ’yan shekara arba’in, kansu ya yi fari fat da hurhura. Kadan ke haye shekara hamsin sai su mutu. Amma kuma da kyar su kan iya lissafin shekarunsu daidai, tun da ya ke ba su da hanyar kirga shekaru sai da ruwan sama, ko wani muhimmin abin da ya faru a shekarar. Saboda haka ko wace shekara tana da sunanta game da babban abin da ya faru cikinta. Misali, shekarar yakin gari kaza, shekaran da aka kone gari kaza, shekarar da aka nada Sarkin gari kaza, da sauransu haka. Na tabbata ba za su manta da shekara ta 1796 ba, domin kuwa za su rika kiranta “shekarar da Bature ya wuce."
Amma ko da ya ke ba su dadewa a duniya sai su mutu, duk da haka ba su cika yawan cuce-cuce ba. Dalilin wannan ina tsammani saboda cin abinci iri daya ne kowane lokaci, da kuma aike-aike masu motsa jiki. Zazzabi da atini su suka fi yawa, suka fi kashe su. Babban maganinsu game da wadannan shi ne rataya layu, da sauran magunguna na camfi. Amma na ga wani irin magani nasu mai amfani. Watau da ce mutum ya sami zazzabi, sai a yi masa surace. Yadda a ke suracen nan, sai a share kasa, a zuba garwashin wuta mai yawa. A kan garwashin sai a kakkaryo ganyaye danyu a shimfida. Sai mara lafiyan ya hau kai ya kwanta, sai a rufe shi da zane duk jikinsa. Sa’an nan sai a malala ruwa cikin garwashin nan. Tururi mai zafi ya kan tashi sama ta cikin ganyayen nan zuwa jikin mara Iafiyan. In tururin ya kare, wutar kuma ta mutu, sai a bude mutumin. Sai a ga kamar ya yi wanka ne, zufa ta keto masa ko'ina a jiki. Ya kan wartsake nan da nan. Amma ba su da maganin atini sahihi, sai bawon itatuwa iri iri su ke hadawa da abincinsu suna ci. Suna kuma da yawan cutar fata ta kuraje, suna yin tindimi, da kuturta mummuna. Saboda rashin maganin kuturta su kan ce ba ta warkuwa, har su kan bar ta ta ci karfinsu, ta guntule musu yatsun kafa da na hannu.
Akwai kuma kurkunu a kasar kwarai da gaske, amma ya fi kama mutane da bazara in ruwa ya fadi. Amma ko su sun tabbata daga ruwa su ke daukarsa. Sun ce kuma a ruwa su ke shan gansakuka wanda ke sa musu makoko. Na ga masu ciwon sanyi dai dai, amma ban ga wanda ciwon ya kama shi da kyau ba. Bakaken mutane sun iya dorin karaya, sun kuma iya gyara targade, kuma su kan yi kaho in jiki ya yi musu nauyi, don su rage jini.
In wani babban mutum ya mutu, danginsa su kan taru su yi ta kuka. Su kan yanka saniya ko akuya, su yi wa masu zuwa jana'iza abinci. Ran da mutum ya mutu ran nan su ke rufe shi, sai ko in cikin dare ya mutu. Ba su da wurin rufe matattu musamman, galibi ma a tsakar dakin mamaci a ke haka masa kabari, ko a gindin wata babbar itaciya mai inuwa. Su kan rufe jikin mamaci duk da farin zane kana su sa shi a kabari. Ba su yin wani gini ko wata alama a kan kabari, sai in a bayan gari kabarin ya ke, su sa kaya da ganyaye don kada kura ta tone.
Mutanen Afirka mutane ne masu son waka, mazansu da matansu. Akwai masu waka musamman, wadanda ba su da wata sana'a sai yawo gari gari suna waka. Su kan kada ganga, wani lokaci molo, ko goge, ko su busa sarewa. Akwai wadansu Musulmi kuma masu zuwa wuri wuri suna rera karatu na waka, da murya mai taushi da dadin ji.
Akwai abinci iri iri, amma galibi, in safiya ta yi, kowa ya kan sha kunun tsamiya ne. In rana ta yi tsaka, su ci wani irin abinci da a ke zuba masa man kadanya. Da yamma su ci wani abin da su ke kira alkuskus. Da Musulmi da Arna duk abincinsu ke nan, kuma da hannun dama su ke ci, su zauna bisa tabarma. Arna su kan sha giya, amma Musulmin ba su shan kome sai ruwa. Dukansu suna shan tukunyar taba. Amma can cikin kasa gishiri ne abincin nishadi saboda wuyarsa. Su kan tsotsi gishiri zallarsa, kamar yadda a ke tsotsan sukar.
Babbar sana’arsu ita ce noma. Da rani matansu suna kadi, mazan kuwa su yi saka. Su kan rina tufafinsu da wani irin shudi mai kyau, wanda su ke shiryawa da ganyen baba game da toka. Irin baban nan nasu, ko a kasar Hindu ko a Turai ba a samun shudin da zai fi shi. Akwai madinka da yawa, akwai dukawa da makera. Kuma akwai lokaci musamman na farauta, don kusan ko wane mutum ya iya harba kibiya. Duk aike-aiken nan da 'ya'ya da bayi su kan taru wurin yinsu. Irin sana'ar ubangiji ita zai koya wa bawansa.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)