19. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Ina cikin tafiya a cikin kungurmin daji, na tasam ma wani gari wai shi Sibidulu, sai na ga mutum ya fito daga sagagi ya kama linzamina. A jima kadan sai ga wadansu ’yan’uwansa. Suka ce sai in sauka. Na sauka, suka caje jikina kaf, @bukarmada suka tube ni tsirara, suka tafi da kayana duka, har dokina. A haka suka bar ni tsirara haihuwar uwata. Amma ni duk wannan bai taba mini rai ba kamar hulata da na rasa, domin duk takardun da na rubuta labaran tafiyata a ciki su ke. Zuwa can sai na ga sun jefad da hular. Na yi gudu na dauko. Can kuma, ko tausayin tsiraicina suka ji, ko mene ne oho, kawai dai sai na ga daya ya komo mini da tsummar kwalashat din da wani tsohon wando. Na dauka na sa, na zauna a wurin, na shiga sakar zuci. Me zan yi, ban sani ba. Amma ko da wannan abu ya same ni, zuciyata ba ta karai ba. Na tabbata Ubangiji mai rahama zai fisshe ni daga dukan hadari.
Ina cikin tunani haka, sai idona ya kai kan wani dan tsiro kankane, mai kyaun fure, a gefen hanya. Sai na ce a zuciyata, “Sarkin da ka halicci wannan tsiro, ka rene shi, ka ba shi ruwa, ka raya shi, ka sa masa wannan furen ado, lalle ba za ka kyale halittar mutum, mafificiya cikin halittarka duka, ta halaka ba!" Sai na ji sabon karfi ya zo mini, na tashi na dauki hanya a kasa ni kadai, sai Sibidulu. Na tafi wurin Sarkin garin. Na rattaba masa duk irin abin da ya same ni, ina magana yana amsawa da kai, yana ta shan tukunyar taba. Da na kare, ya ce in zauna. Ya rantse zai samo masu fashin nan, kuma sai ya kwato mini dokina da kayana. Ya nuna mini daki a gidansa, ya sa aka kawo mini abinci. Ya shiga binciken ’yam fashi.
Aka kwana biyu babu labarin doki ba na kaya. Da na ga haka, na ga kuma wahalar abinci ta yi yawa, sai na ce ina so in yi gaba. Ya ce in na isa wani gari wai shi Wonda in dakata a can, za a tarad da ni da kayana. Haka kuwa aka yi, don ran nan ina zaune tare da Sarkin Wonda, sai ga dokina da 'yan tarkacena. Na yi murna da samun tufafina, doki kuwa na ba Sarkin Wonda, da sirdi da linzami na aika wa Sarkin Sibidulu wajen taimakon da ya yi mini.
Kwanana tara a gidan Sarkin Wonda, amma babban abin da na gani cikin kwanakin nan shi ne kullum matan garin za su zo da yamma su karbi hatsi a wurinsa. Da ya ke ana faman yunwa ne, sai na zaci taimako ne Sarkin ya ke yi wa talakawansa. Na tambaye shi don in tabbatar, sai ya ce, “Don me zan ci da @bukarmada mutane kyauta? Dubi yaro ga shi can, uwarsa ta sayar mini da shi don in rika ba ta mudun dawa daya har kwana arba'in." Da na ji haka, sai hantata ta kada, don kuwa na san wuyar da ta matsa uwar har ta sayad da dan da ta haifa a cikinta, ba karamar wuya ba ce. Amma hankalina bai kara tashi ba sai da yamma ta kewayo, matan nan suka zo karbar dawa. Bayan uwar yaron ta kunso nata rabon, sai da ta zo wajen danta ta dafa shi, tana shafarsa a kai, tana yi masa magana. Abin tausayi. Da na dube ta, sai na ga ta zama kashi da fata kurum don yunwa.
Na tashi Wonda a kasa, ga ruwa ko yaushe, ga duwatsu a hanya da tsakuwa, ga takalmana sun kare, har na mai da su sambatsai. A kan hanya wani dutse ya buge ni a idon kafa, kafin kwana biyu ba na ko iya takawa sai da kyar da sanda. Da haka dai har na kai wani gari wai shi Kamaliya. Wannan gari ne na Arna da Musulmi. Da na isa aka kai ni gidan wani Musulmi, ana kiransa Karfa Taura. Tajiri ne. Babbar safararsa kuwa bayi ya ke saye yaransa su kai Gambiya su sayar wa Turawa. Na same shi a gida, ga fataken bayi sun kewaye shi, shi kuwa yana @bukarmada karanta musu wani littafin Larabci. Ya tambaye ni ko ina ji, na ce a'a. Sai ya tashi ya shiga gida, ya fito da wani dan littafi, ya mika mini. Ko da na bude, me na gani? Sai ga littafin addu'o'i irin nama na Kirista, an rubuta shi da Turanci. Na shiga karatu ra ra ra da karfu, kowa kuma sai ya bude baki yana kallo. Ashe da su mutanen da ke tare da Karfa Taura sun ce masa karya na ke yi, ba Bature ne ni ba. Suka ce su ba haka suka saba ganin Turawa a Gambiya ba. Amma karanta littafin nan sai ya wanke ni.
Bayan mun gaisa da Karfa Taura, na kwashe labarina duk na fada masa, na kuma gaya masa cewa yanzu na gaji, gayar gajiya. Ga yunwa, ga ciwo, ga huntanci, ga rashin guzuri. Duk bayan wannan ga mil wajen dari shida a gabana wanda lalle in yi kafin in isa Gambiya, sa'an nan kuwa da kafa, kuma a cikin bakuwar kasa da miyagun dazuzzuka. Da fada masa sai tausayi ya kama shi, @bukarmada saboda haka ya daura niyyar taimakona. Ya ce lalle ba shi yiwuwa in wuce ni kadai, sai in zauna a gidansa har kaka, sa’an nan im mutanensa za su tafi Gambiya su kai bayi, zai hada ni da su. Ya sa aka gyara mini wuri a gidansa, ya shiga jiyyata, yana ba ni abinci dare da rana a kullum.
Wata rana muna zaune sai aka kawo bayi, duk an yi musu kangi da sarka. Sai daya daga cikinsu ya dube ni, ya ce, “Sannu!”
Na ce, “Yawwa. Sannu kadai."
Ya ce, "Don Allah, ba ni wani abu in ci, yunwa ta dame ni."
Na ce, “Wayyo, ai ni ma bako ne, cishe ni a ke yi, ba ni da kome.“
Sai ya ce, “Ni na ba ka abinci lokacin da ka ke da yunwa, daidai ne yanzu kai kuma ka hana ni? Ko ka manta da wanda ya kawo maka madara a Karankalla? Amma fa a lokacin nan ba na cikin sarka, shi ya sa yanzu ba ka gane ni ba."
Nan da nan sai na gane shi, na tafi wurin Karfa, na roko ’yar gyada na kawo masa. Na tambaye shi yadda ya zama bawa yanzu, ya gaya mini 'yan hari ne suka zo garinsu, suka kama shi, suka sayar.
Ran nan sai Karfa ya ce zai shiga cikin kasa, ya sawo bayi wadanda zai aika da su Gambiya da kaka. Ya danka al’amarina duka a hannun wani malami wanda ke karantad da yaran Kamaliya sha’anin Addinin Musulunci da Alkur’ani. Muka yi sallama da Karfa. Ya bar ni, ba yunwa ba kishirwa. Saboda haka na sami damar zama cikin tsanaki, na rubuce duk irin abin da na gani a Afirka game da halayen kasar da halayen zaman mutane. Don haka yanzu sai mu jingine labarin tafiya, da sauka da tashi, mu ji yadda yanayin kasar Afirka ta ke, da irin zaman @bukarmada mutanenta. Maganar tafiya kuma sai kaka ta yi, Karfa ya dawo da bayinsa, an shirya ayarin da za su tafi Gambiya tare da ni, sa’an nan mu ci gaba.
KASAR AFIRKA DA ZAMAN MUTANENTA
Babban abin da na gani game da kasar Afirka ta hanyar da na bi, shi ne kasa ce mai zafi kwarai da gaske. Amma misali tsakiyar watan Yuli akwai ruwa, kuma akwai iskar hadari mai karfi ko yaushe. Tun daga lokacin nan har watan Nuwamba duk damina ce. Yadda daminar ta kan fara, sai ka ga iska ta tashi mai karfi. Kwana kadan kuma sai walkiya, sai kuma ruwa ya fado. Iskar damina daga yamma-maso-kudu ta ke busowa, watau wajen fuskar teku. In damina ta fita, sai kuma iskar hunturu ta tashi. Ita kuwa tana busowa daga arewa-maso-gabas ne, ta ratso Hamada. Da ce wannan busasshiyar iskar ta fara hurowa, nan da nan sai yanayin kasar duk ya sake. Ciyawa ta kan bushe, itatuwa su kan kakkabe ganyayensu, rafuka su kan kone nan da nan. Da ya ke iskan nan ta ratso ta Hamada ne, akwai garin rairayi da ta kan kwaso wanda ke dushe hasken rana. Saboda haka a lokacin hunturun nan a kullum akwai buda. A wurin Turawa sanyin hunturun nan ya fi zafin bazara dadi, da karin karfi da lafiya. Amma wurin Bakar Fata ba su sonsa, domin a lokacin nan kurar da iskar ta kwaso tana damfare mnsu a jiki, fatarsu ta kan yi kaushi, idonsu ya yi ta zubar hawaye, leben bakinsu ya farfashe.
In ciyawa ta bushe, mutane su kan sa wa daji wuta. Amma a wadansu wurare kamar Ludamar shari'ar kasar ta hana @bukarmada kona daji, don ciyawa nan ita ce abincin dabbobi. Da ce an kona daji haka sai ka ga sababbin ciyayi da kananan tsiro suna hudowa, nan da nan sai ciyawa sabuwa ta rufe kasa.
Na ga mutanen Afirka suna amfani da 'ya'yan kadanya wajen yin wani irin mai fari, mai gardi a baki. Amma a dajin Afirka babu itatuwa da a ke cin saiwoyinsu da yawa, yadda na gani a wadansu wurare na duniya. Sai dai na ga 'yan tushen ayaba kadan da kuma lemo mai zaki a Gambiya. A zatona kuwa wadannan asalinsu ba itatuwan Afirka ba ne. Lalle Turawa masu cinikin bayi suka kawo su suka shuka.
Kasar tana da yalwa. Ko'ina mutum sai ya sheme daji ya yi gona. Amma a zatona dai duk kasar ta Sarki ce, saura im mutum yana noma ta ta zama tasa. Yana iya ya sayar, ko ya bar wa 'ya'yansa su gada. In an shiga can cikin kasa, akwai duwatsu da tuddai manya-manya. Akwai kuma karkara da fadamu masu kyau.
Na shiga cikin kabilu iri iri. Akwai abubuwa da dama wadanda suka hada kabilun nan. Babbansu shi ne fatar jiki, don duka bakake ne. Na biyu, kusan duk Bakin Mutum yana biyayya mai kyau ga Sarkinsa. Yanayin zamansu duka daya @bukarmada ne, haka fasalin garinsu, da na gidajensu. Akwai masu son mutane, akwai marasa so, akwai masu kyakkyawan hali, akwai masu mugun hali. Amma duk kabilun da na gani, babu masu taushin hali da son zama lafiya kamar Mandingo. Ga su da fara’a, da son mutane, da son gane kome, ga saukin hali, da neman a yaba musu.
Babban mugun halin mutanen wannan kasa daya ne, watau sa idonsu a kan kayana, suna kwadayin sacewa ko yaushe. Amma in an dubi sahihiyar gaskiya, bai kamata ba a zarge su saboda kwadayin kayana, tun da ya ke ko a wurinsu sata babban laifi ne. Kuma babu barayi da yawa a cikin kabilarsu. Saboda haka, kafin mu yi hanzarin kiransu barayi, sai mu duba mu ga in ’ya‘yan banza a kasashen Turai suka sami hanya irin ta mutanen Afirka, ashe su ma ba za su yi wa bako abin da Mandingo suka yi mini game da kayana ba? Sai mu tuna a Afirka Sarakunan kasar babu ruwansu da kiyaye lafiyar bako, al'adarsu kuma ba ta hana wa mutanensu tare bako su kwace kayansa ba. Kayan nan nawa kuwa a wurin Bakar Fata darajarsu kamar ta yakutu da lu'ulu'u ne a wurin Turawa.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada