MUNGO PARK MABUDIN KWARA 25

25. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blospot.com
...


 
Ana zafi ran nan kwarai, ga jakunammu wadansu cikinsu ba su saba da kaya ba, saboda haka muka sha wuya a hanya. Tun fitarmu Kayi, ba mu fi mil biyu daga garin ba, jakuna uku suka kafe a tabo cikin wata fadamar shinkafa. Kafin mu fid da su, sauran mutanemmu da madugammu duk sun yi nisa, sun bace mana. Da muka fita da jakunan, sai muka kama hanyar Jonkakonda, ba mu sani ba ashe mun bace. Muka dai isa wani kauye wai shi Lamin Gotto da kyar, duk mun gaji. Muka sauke kayammu a gindin babbar itaciyar tsakiyar gari, wadda na ce ana ganin irinta a galibin garuruwan wannan jiha ta Afirka. Sarkin garin ya zo, muka gaisa. Sai ya ce mini kada mu kwana a gindin itaciyan nan, in kuwa mun ki, gobe da safe duk za mu tashi matattu. Da na ji haka, na dade ina tunanin abin da ya ke nufi, amma ban gane ba. Sai zuwa can ya kama hannuna, ya ja ni sai bakin wani kogo na saiwar itaciyar. Da na duba ciki, sai ga mashigu da uku, duk jini ya rufe su, ga tsiminsu cikin kasussuwa, ga wata konanniyar igiya ta kewaye su. Ganin haka, sai na ce mutanemmu su kwashe kaya, muka sake wuri.
Kashegari da safe, ran 28 ga watan Afril, muka tashi muka nufi Pisania, garin da abokina, mai taimakona Mr. Ainsley ya ke. Muna tafe har muka zo bakin Kogin Gambiya. Nan muka dan huta, muka yi ban ruwa, muka yi kalaci, wajen azahar muka yi gaba. Ran nan ba mu kwana ba sai a Pisania, a gidan Mr. Ainsley. Mutanen garin suka yi mamaki da suka ga na sake fitowa Afirka, don ba su zaci zan sake yarda, in shiga halaka irin ta da ba. A nan garin muka yi shirin kome na shiga cikin Afirka sosai. Aka dura ciyawa a akumaran jakuna, aka daddaura kaya. Kowane jaki aka yi masa alama da jan fenti maganin bata don fenti ba shi wankuwa ba shi yiwuwa kuwa a sausaye gashin wurin. Haka kuma kayammu duk an yi musu alama da fenti.
Ran 4 ga Mayu muka bar Pisania. A wajen shirya ayari kuma muka raba kammu kungiya kungiya, kowace da nata dabbobin da za ta kula da su. Mr. Ainsley da sauran manyan gari duka suka raka mu har Tendikunda. Nan muka yi ban kwana, muka rabu, su suka juya, mu kuma muka yi gaba. Jakuna suka yini wahalshe mu, wadansu suka rika tutsu suna zubad da kaya. Tafiya dai ta kasa yin sauri, sai da kyar muka ci mil takwas a ran nan, muka isa Kataba.
Da yamma ta yi, muka tafi gidan Sarkin Kataba da ni da Isyaku, jagorammu, don in gaishe shi. Muka same shi ya sha giya ya bugu tatil, bai san abin da yake yi ba. Da na ce na zo in gaishe shi ne, ammna ga gaisuwata ta kwalabar barasa guda. sai ya ce ba zam fita garinsa ba sai na ba shi kwalba goma, guda ta yi masa kadan. Muka fa shiga ja-in-ja da shi, yana kwalba goma, ina kwalba daya, da kyar dai ya matsa ya karbi biyu. Da gari ya waye muka kama hanya, muka yi ta fama da jakuna, har muka isa Jinde. A nan muka kwana biyu. Mutanen garin nan gwanayen aikin baba ne, suna yin rini mai kyau. A dan zaman da na yi har na koyi yadda a ke yin wannan sana’a.
Bayan mun huta kwana biyu a nan, sai kuma muka yi gaba. Ga mu nan, ga mu nan, har muka isa Tattikonda a kasar Wulli. A nan, dan abokina Sarkin Wulli mai mutuwa ya zo ya tarye ni. A cikin tadi ya gaya mini sai in mai da hankali, don kuwa dillalan bayi na Madina suna kwadayin kwashe mini kaya. Bayan mun rabu, kashegari sai ga mu a Madina, babban birnin kasar Wuili. Ba mu shiga garin ba, sai muka sauke kayammu a gindin wata itaciya daga bayan gari. Muka aika aka sanad da sabon Sarki saukarmu, muka kuma roki izni mu zo mu yi gaisuwa. Aka ce ba damar ganin Sarki sai da la’asar.
Da lokacin zuwa fada ya yi, na dauki kananan bindiga biyu, liyari goma, sandar amba goma, da dutsen wuya goma. Muka je aka yi mini iso, na shiga gaban Sarki. Bayan mun gaisa, na ba da gaisuwan nan tawa, aka ajiye masa a gaba. Sai ya dubi kayan nan a raine. Can an jima ya ce in kwashe abina, ba ya so. Ya ce ya ji wai na ba Sarkin Kataba gaisuwar da ta fi wannan sau nawa-nawa, yaya shi zam ba shi 'yar kyauta haka? Raini ke nan. Na ce masa ba haka ba ne, abin ma da na ba Sarkin Kataba ko kama kafar yawan nasa bai yi ba, amma ya ki yarda. Tilas dai sai da na kara wadansu liyarin guda goma sha biyar da wadansu duwatsun, sa’an nan da rarrashi, ya karba. Bayan wadannan kuma ya ce sai in ba shi bargo, ya rika rufa da damina maganin sanyi. Na aike masa da guda.
Bayan gaisuwar Sarki ga ta dansa, ga ta fadawansa ga ta dillalan bayin garin wadanda suka hada ni da Sarki, a zuwana na farko, aka kusa hallaka ni. Duk dai na dam ma kowa, kwalamarsu ta lafa. Muka sami iznin wucewa, muka tashi. A hanya muka wuce Barrakonda, har na biya ta gidan abokina Jemaffu Mammadu, muka gaisa. Daga nan sai Bamabaku, can muka kwana. Na sayi sa muka yanka, na sayi jakai biyu. Da muka tashi sai Kanife, wani kauye mai wuyar ruwa. Da isarmu muka ga mata sun rufe rijiyar tsakiyar garin, kowace tana saka gugarta, tana cika tulu. Ga shi kuwa mutanemmu da dabbobimmu duka suna fama da kishi. Sai na aiki wadansu sojana na ce su je su samo ruwa. Ko da suka isa, sai suka tarad da rijiyar kandar, sai jira ake yi ta gudano sa’an nan a diba. Ashe wai labari ne ya zo wa mutanen garin tun ba mu iso ba, aka ce musu a Madina kafin mu sami ruwa sai da muka ba da duwatsun wuya muka saya. Dalili ke nan su kuma matansu suka kwashe ruwan suka tara, don mu saya, su sami duwatsun, su yi ado.
Jin haka, don im ba su haushi, sai na tura wadansu mutanemmu can bayan gari wajen wata korama, suka debo ruwan da muka sha muka yi girki, muka kuma shayad da dabbobimmu. Kashegari fa muka sake komawa rijiyar, don waccan koramar ta yi nisa kwarai. Ko da muka je sai muka tarar gidan jiya ne, mata sun taru suna ta kwashe ruwan don kada mu samu. Sai wani cikimmu ya yi wata dabara, ya je bakin rijiyar, ya leka kamar zai duba zurfinta, sai ya saki goran ruwansa tsundum a ciki. Sai 'yan'uwansa suka ba shi sauran gorunan ruwansu, suka daura masa igiya a gindi, suka zurara shi cikin rijiyar wai zai dauko nasa goran. Yana shiga ya ciko gorunan duka da ruwa, aka jawo shi ya fito. Ganin haka matan suka ji haushi, don sun san tasu hajjar ba za ta sami kasuwa ba. Kowace sai ta koma gida da tulunta tana tsaki. Da kuwa sun zaro wuyansu za su sami duwatsun ado su daura!
Bayan mun bar Kanife da kamar mil hudu sai muka isa Kussai. A nan muka sauke. Muna cikin hutawa, sai wani soja ya tsinki sabadar dorawa ya ci. Yana cikin ci, sai Sarkin garin ya zaburo a guje, ya zo da hushi, ga wuka zare a hannu, ya fizge sauran dorawar, ya ce lalle sai mu tashi mu bar masa garinsa. Da ya ga ba mu firgita ba, sai ma dariya mu ke masa, sai ya lafa. Ya ce abin da ya sa ya yi hushi, wai ba don cin dorawar da aka yi ba ne, sai domin an ci a gaban mata. Dalilin da ba aso a ci dorawa a gaban mata da yara, don kasar ba ta rabuwa da yunwa, in ta zo kuwa ba wani abinci sai dorawa. Shi ya sa, in ana koshi, a kan hana mata da yara taba ta, a rika ba su tsoro ana cewa kowa ya taba wani mugun abu zai same shi. To, da ce yunwa ta auku, sai kuma a buda dibar dorawa. In aka bar ta ba a tsare haka ba, nan da nan sai mata da yara su hau mata, in yunwa ta zo a rasa abinci.
Daga wannan gari za mu shiga wani Kungurmin daji, wai shi Dajin Simbani. Isyaku, da ya ke shi dan kasa. ne, ya san dajin, kuma yana tsoron shiga cikinsa kwarai, ya ce da kyar ne ba za mu gamu da mutanen Bondu ba. Ya ce wai ’ya’yan Sarkin kasar suna basasa a kan maganar gadon sarautar ubansu. Labari kuwa ya watsu ko’ina, an san Nasara za su ratsa kasar dauke da dukiya takaka. Saboda haka ya tabbata ’ya’yan Sarkin nan za su yi rigen tare hanyarmu, don sun san cikinsu duk wanda ya sami kayan da mu ke dauke da shi zai ci nasarar yakin. Muna kara matsar dajin, Isyaku yana dada karya zuciyata. Ran da fa za a shiga, sai ya ka da wani bakin rago, ya tsaya ya ja doguwar addu’a a kansa tukuna, sa'an nan ya sa wuka ya yanka, ya bar shi nan, ya ce mu shiga.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
Post a Comment (0)