MUNGO PARK MABUDIN KWARA 24

24. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
TAFIYA TA KARSHE
BAYAN MUNGO PARK ya koma Ingila, ya kai labarin duk abin da ya gano a Afirka, an kare masa godiya sai ya koma gonar ubansa a Fowlshiels ya zauna. A can ya shirya irin zaman da zai yi, da sana’ar da zai kama. Da farko abin da ya fara yi shi ne aure. Ya auri wata yarinya 'yar wani dattijo da a ke kira Mr. Anderson a Selkirk, ran 2 ga Agusta 1799. Duk zaman nan yana tare da uwarsa ne da kanensa guda. Bai kama wata sana'a musamman ba, don yana ta samun kudin littattafansa da ya rubuta na tafiyarsa, ga kuma @bukarmada jakakkunan da aka biya shi ladan wahalarsa. Amma daga baya sai ya nemi aiki a wurin Gwamnati. Da abin bai yiwu ba, tilas ya kama sana’arsa ta aikin Likita. Ya tashi ya koma wani gari ya shiga warkad da masu ciwo. Kafin dan lokaci, ya kusa kwace wa Likitocin garin kasuwa, domin duk ya fi su tausayin marasa lafiya, da matalauta, da talakawa. Ku san kuwa wannan yana cikin manyan abubuwa da a ke bukata ga mai aikin jiyya.
Amma a wurin mutum irin Mungo Park wanda ya ga duniya, ya saba sauka da tashi, a kullum yana ganin wani abu sabo, zama wuri daya haka ba zai yi masa ba. Wata rana suna tadi da wani dan'uwansa, sai ya dauko maganar komawa Afirka. Dan'uwan ya ce ya kamata ya fid da wannan mafarki daga zuciyarsa. Ya ce masa mutumin da ya ga hadari irin nasa a cikin bakin dajin Afirka, Allah ya @bukarmada taimake shi ya fito lafiya, yaya har zai yi kwadayin komawa? Mungo Park ya ce gaskiya ne, amma yadda zafin Afirka ya ke kisa, haka sanyin Ingila im babu wani aikin da zai sha'awartad da zuciya, zai kashe mutum. Ya ci gaba da sha'aninsa, amma ko dare ko rana ba shi da wani tunani sai na komowa Afirka.
Ran nan, cikin 1803, sai ga takarda daga London, aka ce Gwamnati tana kiransa ya zo maza. Da zuwansa aka ce abin da ya sa a ke kiransa ana shawarar za a aika da wadansu ne su ci gaba da binciken Kwara, ana so ya zama shugaba. Da jin haka sai zuciyarsa ta yi fari, don ya tabbata akwai babban aiki wanda zai yi wa kasarsa da sauran 'yan Adam duka, yana nan yana jiransa can a cikin Afirka. Nan da nan ya amsa, ya koma gida ya shirya sha'aninsa. Ya yi sallama da abokansa, ya taso daga Scotland ya zo London cikin Disamba 1803. Amma da zuwansa sai ya tarar duk shirin da ya bari ya watse. Aka ce ba zai sami tashi zuwa Afirka ba sai cikin Satumba 1804. @bukarmada Hankalin Mungo Park ya tashi ainun, ga shi ya yi sallama da gida, da 'yan'uwa, da abokai duka, ga kuma tafiya tana neman fasawa. A cikin haka sai wani cikin manya ya ba shi shawara mai amfani. Ya ce kafin Satumba ya zo, ya kamata Mungo Park ya koyi duban taurari, yana sanin matsayinsu a kowane lokaci na shekara, maganin bata a cikin daji, ya kuma koyi Larabci. Saboda haka ya sami wani Balarabe wanda ke zaune a London wai shi Sidi Omback Bombi, ya dauke shi suka koma Scotland, ya koya masa Larabci. Duk lokacin nan babu abin da ya ke jira illa ya ga takardar kira.
Kwaram sai ga takarda, ya taso sai London. Da zuwa aka ce ya shirya, aka kuma hada su da Mr. Anderson surukinsa, kanen matarsa, da Mr. Scott, aka ce su tafi tare. Aka shirya musu kayan guzuri da na tsaraba. Ba abin da ya rage sai iznin tashi, amma kuma sai izni ya ki samuwa. Mungo Park ya fi kowa kosawa, don ya san in aka ja tafiyan nan har damina ta zo, za su wahala kwarai da gaske.
Bayan ya gaji da jira, ran nan sai Gwamnati suka aiko masa da wannan takarda ta iznin tashi, da nuna masa abin da su ke bukata ya yi in ya je Afirka. Ga takardar :
Downing Street,
2 ga Janairu, 1805.
Zuwa ga Mungo Park,
A sanad da kai Gwamnatin Ingila ta ga ya kamata a aika da 'yam mutane kadan cikin Afirka, don su gani ko akwai damar kafa ciniki tsakanin Ingila da mutanen kasar. Sarkin Ingila ya umurce ni in gaya maka, saboda sanin Afirka da ka yi, da irin himma da kokarin da ka nuna a tafiyarka ta farko, ya zabe ka kai za ka tafi.
Sarki ya ba ka daraja ta kyaftin a Afirka Mr. Anderson kuma am ba shi Laftana. Kuma an yarda Mr. Scott ya raka ka. An kuma ba ka iznin ka debi soja har arba’in daga sojan Sarkin Ingila da ke zaune a Gori, gwargwadon yadda ka ga za su ishe ka, amma kada su wuce arba'in da biyar. In ka zo diba, ka rarrashe su yadda za su bi ka zuwa cikin Afirka da karfin zuciya. An kuma yarda ka sayi bayi Bakar Fata a Gori, wadanda suka iya sana'o'i da za su taimake ka a tafiyarka. In kun tashi ku biya ta Jago, ka sayi jakuna hamsin saboda daukar kayanku. @bukarmada
Da ce ka kare shirinka a Gori, sai ka shiga jirgin ruwa ka bi tsawon Kogin Gambiya, har ka kai kasar Senegal. Daga nan sai ku bi kasa, kai kuma za ka nemi hanyar da ta fi muku kusa zuwa Kogin Kwara. Babban dai abin da a ke nufi da wannan tafiya, shi ne ka bi tsawon Kwara har iyakarta, ka kafa amana da ciniki tsakanin Ingila da kabilun da za ka tarar a hanya cikin Afirka, ka nemi sanin tarihinsu da bukatarsu.
In ka sami wannan, sai ka komo gida ta hanyar da duk ka ga ta fi maka lafiya. Ko ka sake ratso Afirka, har ka kawo bahar ta Atlantic, ko ka nufi Alkahira a Masar, ka bi ta Tarabulus.
Am ba ka iznin ka karbi kudi ko nawa, amma kada su wuce jaka hamsin. Kana iya karba a Baitulmalin Ingila, ko a kowane banki na Ingila. Shi ke nan.
Ni ne
CAMDEN
Daya daga cikin Waziran Sarkin Ingila.
Yana karbar takardan nan sai tashi. Sai dai kamar yadda muka bar Mungo Park ya fadi labarin tafiyarsa ta farko da bakinsa, ko a wannan ma ya kamata mu bi shi da kunne. Bismilla, Mungo Park.
NA SAKE KOMAWA AFIRKA
MUN taso Ingila, da ni da Mr. Anderson da Mr. Scott, ba mu zame ko’ina ba sai Jago. Muka sayi jakuna hamsin, muka wuce sai Gori. Na debi soja, na kuma debi mutanen garin wadanda za su @bukarmada taimake mu a hanya. A nan garin ne na fara rubuta wa matata takardar farko a wannan tafiya. Ga abin da na rubuta :
Gori.
4 ga Afril, 1805.
Zuwa ga masoyiyata,
In sanad da ke na iso Gori Iafiya. Yanzu na sami labari akwai wani jirgin Amirka wanda zai tashi daga nan zuwa Ingila yau, shi ya sa na ce bari in rubuta wasika ga matata da ke kaunata, ni kuma ina kaunarta. Muna nan lafiya, tun ran da muka tashi daga Ingila ko ciwon kai ba wanda ya yi, sai Alexander da amosaninsa ya dan tashi masa a Jago, ya kuwa sake shi yanzu. Jiya da dare ma rawa ya yi ta yi a wurin wasa. George Scott lafiyarsa lau.
Na yi sa’a babu wata wahala wajen dibar soja. Kusan duk babu wanda ba ya son tafiya, na kuwa zabi samari karfafa. Don rashin tsoro, da rashin kula da hadari da ke cikin wannan tafiya, har Hafsoshi da dama sun ce za su bi ni. Kila ran @bukarmada Jumma’a ko Asabar mai zuwa za mu tashi zuwa bakin Gambiya. Na sami labari wai abokin nan nawa Karfa wanda na ke fada miki, an ce yana nan a Jonkakonda. Ina so zan roke shi ya yi mana ja gora. Ina zato, kai, kusan ma in ce na tabbata, Ubangiji zai danne fushin mutanen wannan kasa ta Afirka, mu bi har mu wuce, ba abin da zai taba mu.
Masoyiyata, na tabbata kin san yadda kullum zuciyata ke wurinki, ba sai na fada miki ba. Yadda duk ki ke ji a zuciyarki game da ni, haka ni ma na ke ji game da ke. Ba abin da na ke bukata a duniya kamar in ga na zauna ga ni, ga ki, ga ’ya’yana cikin farin ciki. Kwadayin wannan shi ke karfafa mini rai yanzu, kuma ina so ki tabbata ba zan kutsa kai cikin wata halaka yadda zan rasa raina ba, don na san da ke da ’ya’yammu zaman duniya ba zai muku dadi ba, im ba ni. Ina fata tsohuwata ba ta damuwar kanta, tana karya zuciyarta bisa sha’anina. Wani lokaci na kan rika tunanin yadda @bukarmada zukatanku ku biyu su ke saka, kila suna nuna muku kamar ina cikin wata wahala. To, in sanad da ku ku karfafa ranku, don ni har yanzu ban da sa’a ban taki kome ba, kuma ina fata kome zai kare cikin wata shida.
Ni ne mijinki, masoyinki.
Af, na manta im fada miki, yau mun hau dawaki da ni da Alexander mun tafi kilisa. Ya ji dadin kilisan nan kwarai, don babu zafin rana sai iska mai lafiya ke busawa.
MUN SHIGA CIKIN AFIRKA
Da muka tashi daga Gori, sai Kayi a bakin Kogin Gambiya. Ran 27 ga watan Afril, 1805 muka tashi daga Kayi. Jiragen ruwa uku, da Crescent da Washington da jirgin Mr. Ainsley, duka suka yi ta rusa @bukarmada bindigogi, suna yi mana ban kwana. A nan Kayi na yi hayar wani malami wai shi Isyaku, muka yi jinga zai raka ni har bakin Kwara. Shi Mandingo ne, saboda haka zai zama jagora, ya kuma zama tafinta.
Ana zafi ran nan kwarai, ga jakunanmu wadansu cikinsu ba su saba da kaya ba, saboda haka muka sha wuya a hanya. Tun fitarmu Kayi, ba mu fi mil biyu daga garin ba, jakuna uku suka kafe a tabo cikin wata fadamar shinkafa.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)