TUNATARWA GA MASU HANKALI

TUNATARWA GA MASU HANKALI


Shugaba Buhari yace: "Allah Ya sani bisa kokarin tunanina shine in tabbatar na daura Nigeria kan mizanin da zakuyi alfahari da ita a nan gaba, akwai wahala cikin kawo sauyi a 'Kasa , amma muna jureshi iyakar iyawar mu, ko makiya sun tabbatar mun dauki saiti kan makomar Kasar mu Nigeria.

Amma 'yan jari-hujja munyi musu laifin da bazasu yafe mana ba, laifin shine rufe musu kofofin sata, su ba damuwarsu bane Nigeria ta 'kone ta babbake su sayar da tokanta su gudu,
sun sako mu a gaba yanzu da dukkan karfinsu suna bukatar a 'kyalesu su wargaza 'dan abinda muka fara gyarawa.

Basa fatan alheri ko miskala-zarratin wa Nigeria da al'ummar ta, babu wani za6i garemu, za6i yana gareku al'ummar Nigeria, idan kun gaskata kokarinmu ku sake zabanmu a karo na biyu mu dora daga inda muka tsaya, hakan zai zama alheri gare ku, idan kuma kun karyatamu ku koma gare su ('Yan jari hujja) su lalata makomarku da Kasar ku.

Amma tabbas watarana zaku tuna na fada muku gaskiya, kuma na doraku akan gaskiya, kuma na rikeku da gaskiya, zabi naku ne, a batun makomar Kasarku ba batun siyasace a raina ba, face makomar ku nan gaba.." ~Jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gabatar kwanaki a ziyaran da ya kawo jihar mu Bauchi

Wannan jawabin iyakar gaskiyar kenan, ya kamata a sake yadashi zuwa inda ya dace ko wawaye da masu cutar mantuwa daga cikinmu zasu hankalta

Alherin Allah Ya kai ga shugaba Buhari
Allah Ka tsare manashi daga dukkan sharri
Allah Ka daukaka darajarsa duniya da lahira
Allah Ka bashi dukkan nasara da yake nema
Allah Ka zama jagoransa Amin Summa Amin
Post a Comment (0)