LOKUTA GUDA-(5) BIYAR DA AKE BUDE KOKOFIN SAMA.

LOKUTA GUDA-(5) BIYAR DA AKE BUDE KOKOFIN SAMA.

 


 
  
1-Kafin Sallar Azzuhur.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Lallai ana bude kokofin sama lokacin da rana tayi zawali ba'a kullesu har sai anyi Sallar azzuhur, shi yasa nake so aiyukan alkhairi nawa ahau sama dasu a wannan lokacin).
@صححه الألباني في
صحيح الجامع - رقم: (1532)

NB
"Shi yasanya Annabi s.a.w ya sunnan ta mana yin nafila raka'a hudu a awannan lokacin kamar yadda yazo a cikin"
@Saheeha.

2-Lokacin kowane kiran sallah.
Manzon Allah s.a.w yace:
(Idan kayi kiran Sallah ana bude kokofin sama,kuma sai a amshi adduar wanda yayi addua a wannan lokacin).
@الألباني في صحيح الترغيب - رقم: (260) صحيح الجامع - رقم: (818).

NB
"Dan haka mu yawaita rokon Allah bayan kiran sallah lokacine na amsa addua kamar yadda Annabi s.a.w yace".

3-Lokacin jiran sallah a masallaci bayan an gama wata sallah,kamar tsakanin magariba da Isha'i ko tsakanin La'asar zuwa Magariba.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Kuyi albishir,wannan Ubangijinku ne ya bude wata kofa daga cikin kokofin sama,yana alfahari da ku a wajan mala'ikunsa yana cewa:ku kulli bayina sun gabatar da farilla dana dora masu kuma amma suna jiran wata sallar).
@صححه الألباني في صحيح الترغيب - رقم: (445) صحيح الجامع - رقم: (36)

NB
"Wanda ya zauna a wajan sallarsa yana jiran wata sallah mala'iku sunayi masa addua kuma ana rubuta masa ladar yana cikin sallah sannan ana bude masa kofar sama dan amsa adduarsa".

4-Idan dare yayi Rabi Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Idan dare yayi rabi ana bude kokofin sama,sai wani mai kira yayi kira yace: Shin akwai mai rokon Allah a amsa masa?akwai mai roko abashi?akwai mai da damuwa a yaye masa?babu wani musulmi da zai roki Allah a wannan lokaci face Allah ya amsa masa,sai dai mazinaciyar da take amfanuwa da zinar ko kudin zina....).
@صححه الألباني في صحيح الترغيب - رقم: (786)
صحيح الجامع - رقم: (2971)

5-Lokacin yin addua da wadan nan kalmomi:
[ *اللهُ أكبرُ كبيرًا والحمدُ لله كثيرًا وسبحان اللهِ بكرةً وأصيل*ًا]
[*ALLAHU AKBAR KABIRAN WALHAMDU LILLAHI KATHIRAN WA SUBHANALLAH BUKRATAN WA ASILA*]

Daya daga cikin sahabban Manzon s.a.w yana cewa:
"Wani lokaci muna sallah tare da Manzon Allah s.a.w sai wani mutum daga cikin mutane yace:
[ *اللهُ أكبرُ كبيرًا والحمدُ لله كثيرًا وسبحان اللهِ بكرةً وأصيل*ًا]
[*ALLAHU AKBAR KABIRAN WALHAMDU LILLAHI KATHIRAN WA SUBHANALLAH BUKRATAN WA ASILA*]sai Manzon Allah s.a.w yace:
(Wanene ya fadi wadan nan kalmomin??) Sai wani mutum yace nine ya Manzon Allah. Sai yace:
(An amsa adduarka kuma an bude maka kofofin sama,saboda da wadan nan kalmami).
Ibn Umar R.A yake cewa:
"Ban taba barin fadar wadan nan kalmomin ba lokacin addua tun daga lokacin da naji Manzon S.a.w ya fadi haka".
@صحيح مسلم (601). 

Mu hada wannan muyi turawa yan uwan mu domin amfanin juna duniya da lahira.
 
ابن المبارك رحمه الله :
Yana cewa:
"Ban san wata daraja mafi falala da daukaka bayan Annabta kamar yada Ilimi mai amfani".
@تهذيب الكمال (٢٠/١٦).

Allah ya sanya mu cikin wadan da ake amsa adduar su.
Post a Comment (0)