UKU-BALA'I 01




UKU BALA'I

   NA.
KAMAL MUHAMMAD LAWAL.
    (KAMALA MINNA.)
  07039355645
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.


  BABI NA DAYA.
2018.

Jikinta ba abin da yake yi sai rawa kamar wacce ake kaɗawa gangi, ko wacce ruwan sama yayi wa dan karan duka na kin karawa.

 A hankali ta isa kofar dakin, kallo daya za ka yiwa fuskarta, ka tabbatar akwai kayan damuwa a tattare da ita. ba ma na damuwa kadai ba, har da na tashin hankali. idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir. kamar wacce kayi wa surace da hayaki kwalla sun cika su.

 A hankali ta sa hannunta mai kyarma ta yaye labulan dakin, gami da sallama da fadawa cikinsa.

 Goggo Marka dake zaune tana faman kaɗin zare. da sauri ta dago ta dubeta, cikin yatsine fuska da tukuicin harara, ta mai da kanta ga kaɗin ta. Mareeya dake tsaye cikin rawar jiki, ganin irin kallon da Marka tayi mata ya fadan mata da gaba, ta san dama a yi haka. harara da yatsinar fuska a wajan Goggo Marka tamkar a jininta yake, in dai ta zo wajanta sai tayi mata haka, ta rasa dalili? tunaninta dai ya tsaya a haka yanayinta yake. amma in tayi duba sai ta ga ita kadai da Ummarta take yi wa haka. nisawa tayi, a lokacin kwallar da ta taru mata a idanu ta zubo.

 "Goggo. Umma ta ba ta da lafiya tun jiya da dadddare...".

Wani kallo ta watso mata, kafin ta saki zaren kaɗin da take yi. ta zabga tagumi kamar wacce akayi wa mutuwa, ta kure Mareeya da kallo kafin ta numfasa.

 "sai kuma aka ce maki don bata da lafiya ni ce zan bata lafiya ko?. wai ke Mareeya wacce irin dakikiyar yarinya ce? ke a kullum sai kin nuna duhun kai irin na uwarki da kakanninki. in dai za kiyi abu ko".

Kwalla ta ciko mata, cikin nisawa.

 "kiyi hakuri Goggo...".

"...ke dalla rufe mani baki, kuma kiyi maza ki fice mani daga daki, kafin na tashi na mangare ki. ban za kawai, jikan yar masu duhun kai, kai jama'a! Allah ya wadaran naka yalalace. nikam! Marka ina ganin kuturun kinibibi wajan nan, yarinya ki marere ce sai faman ɓari kike, ke mai uwa, kin zo sanar dani bata da lafiya, ko uban me zan mata ban sanin miki ba".
kara narkewa tayi, kamar zata zube mata a kasa. izuwa lokacin hawaye sun fara zubo mata, ta shiga hada hannayenta waje guda bakinta na rawa.

 "Ki taimaka Goggo na rokek...".

Mahucin da ke kusa da ita ta dauka ta cillo mata shi, bai dire a ko ina ba sai saitin bakinta, hakan ya sanyata gimtse sauran maganarta ta. jin zafi da tayi ya sanyata saurin kai hannu ta dafe bakin ta wani zugi da raɗaɗi take jin laɓɓanta sun dauka, kamar za su fice daga mazauninsu.

 Da sauri ta juya ta fice daga cikin dakin, cikin yanayi na raɗaɗin zuci da na laɓɓa. ta rasa abin da tayi wa Goggo Marka, take nuna mata halin-ko-in-kula, ta rasa mai ta tare mata cikin duniyarta, ta rasa mai yasa ta ke nuna musu kiyayya ita da uwarta. tun da take da ita daidai da rana daya bata taba jin ta furta kalma daya akan taba ko uwarta, mai dauke da Alheri. kullum aikin ta kenan nemo inda aibu yak,e ta makalawa rayuwarsu. ita dai tunda ta taso ba ta ga uwarta na nunawa Goggo Marka, wani halin rashin girma ko na cin mutunci ba. kullum cikin biyayya da girmamwa take. amma duk wannan bai hana Goggo Marka ci mata mutunci ba a gaban kowa, ko da kuwa gaban Babanta ne.

 Kuka takeyi wanda bashi da sauti ko kadan, illa hawaye da suke fitar burgu daga idanuwanta, tana faman dauke su amma kamar kara tunkudosu ake. tana jin zafin zuciya da yarda kasar ruhinta ke raɗaɗi, idanuwanta in da sabo ya ci ace sun saba da halin da Goggo Marka, ke nuna mata ita da uwarta.

 A hankali ta karasa dakin mahaifiyarta. kafin ta shiga sai da ta dauke hawayen fuskarta kaf. domin bata bukatar mahaifiyarta ta taga halin da take ciki, hakan zai kara tayar mata da hankali sosai. kofi ta dauka bisa randar ruwan dake kofar dakin, ta debo ta wanke fuskarta, sannan ta sanya haɓar zaninta ta tsane fuskarta tas. amma hakan bai hana a gane tayi kuka ba, domin idanunta sun kaɗa sunyi jajir, murmushin yaƙe ta kalato ta yafawa fuskarta, sannan ta shiga cikin dakin bakinta dauke da sallama.

 Tsaye ta hango uwarta ta, sai faman hada gumi take yi tana kai kawo. kallo daya zakayi mata ka tabbatar tana cikin matsanancin yanayi, lakari da yarda take cizon laɓɓanta kamar zata cizgesu daga mazaunansu. fuskarta ta rine tayi jajir abin ka da farar mace. kallo daya Mareeya tayi mata ta kau da kai, jin kuka na shirin kawo mata ziyara, zuciyarta ta shiga bugu. ta sani uwarta na cikin yanayi na matsaninin ciwo, amma ta rasa mai ya kamata tayi domin taimakon, ta a matsayinta na 'yarta wacce ta haifa a cikinta. waje daya taje in da take tunanin za ta samu waraka, amma anyi mata korar kare tare da bakaken maganganu.

 "Mareeya ya akayi na ganki haka, mai ya sameki?".

Habeeba ce ta fadi haka, cikin karfin hali da na zuciya. sai faman numfarfashi take, gumi na cigaba da karyo mata, kamar wacce ake juyewa bokitin ruwa.

 yanayin sautin muryar Habeeba da maganarta, ba karamar rauni suka kaiwa zuciyar Mareeya ba. ji take kamar ta rushe da kuka saboda tsananin tausayin uwarta. jin amonta ya tabbatar mata tana cikin wani mataki mai tsananin wahalar da rai da ruhi, ta sani uwarta tana hakuri tana da juriya, da alamun a wannan fikirar hakurinta da juriyarta ba za su samu muhallin zama ba.

 Juyawa tayi, ta fuskanci mahaifiyarta sosai. tana faman gyaɗa kai cin yanayi na tausayawa.

 "lura da nayi da halin da kike ciki, ya sanya ni zuwa neman wani taimako daga wajan Goggo. amma hakan bai samu ba".

ta karashe tana goge hawayen da suka zubo mata, tana jin yarda zuciyarta da kasar ruhi ke tsalle-tsalle cikin yanayi na tausayi da neman wata hanya domin samun mafita.

Habeeba ta gyada kai, tana mai sakin murmushi wanda daka kalla zaka san na dole ne, ba wai don wani farinciki akayi sa ba ko na tsuwa. to ina ma natsuwar take wacce ta rigaya ta falle da gudu ta bar duniyarta.

 "Hmmm Mareeya kenan. kuma don kin je ba ta aminta ba shine ki kayi kuka?".

Ta karashe tana mai kafe da kodaddun idanuwanta, wanda suke cikin hali na rashin nutsuwa.

Girgiza kai Mareeya tayi kafin ta dubi uwarta ta, murya da salon rauni.

 "Umma gani nayi ita ce kusa damu shiyasa na yi tunanin ita yafi dacewa aje wajanta, ba wai aje waje ba. kuma gata a cikin gida, sai nake tunanin in har aka je waje aka nemo a matsayinta na babba ba za ta ji dadi ba. ashe ba haka bin yake ba, tunani na daban da hasashena akanta".

ta karashe cikin rawar murya, mai son fashewa da kuka. a daidai lokacin ta ga uwarta ta, ta saki wani nishi wanda ya taho da wasu tawagar hawaye, da hanzarinta ta isa gareta, ta riko mata hannu.

 "Umma ko Asibiti zamu tafi, Umma ko naje na kira Baba ne?".

Abin da ta shiga fadi kenan, cikin yanayi na bugun zuciya, mai tattare da tsoron halin da ta ga uwarta ta aciki. bata tanka mata ba, illa numfashi da take ta faman ajjewa. lokaci lokaci hannunta na kan turtsetsen cikinta, wanda take jin duk wani hali da take ciki na wahala shine sanadi. shine yake rangwantar mata da jarumtar ta, ya ke rangwantar mata da kumajinta, da duk wani azanci nata.

Girgiza kai ta shiga yi, alamun a,a ba sai ta je ba. hakan ya kara rudar da 'yar natsuwar Mareeya, nan ta shiga girgiza kai, ita ma tana sakin nishi mai dauke da son fashewa da kuka.

 "a,a Umma. karki ce haka don Allah, kina bukatar taimako a halin da kike ciki, don Allah ki yarda a nemo mai taimaka miki ko kuma mu tafi asbiti"..

 Girgiza mata kai ta cigaba da yi, tana jin wani irin ciwo mai tsananin karya jarumtar numfashi na kawo mata farmaki, ji take kamar numfashin ta zai katse, duniyar taji ta shiga juya mata kamar zata jirkitar da ita, ba abin da take ambato a ranta da kasar ruhinta sai 'Innalillahi wa inna ilahir raji'un'.

Hawaye suka shiga digo mata wanda take jin su kamar garwashin wuta ne ake goga mata a fuska, hannun Mareeya ta rike gam! kamar zata tsinke shi, ita kanta Mareeya taji rikon da uwarta ta tayi mata, sosai da sauri ta dago kai ta dubeta, idanuwanta sai hawaye da suke digo.

 "Umma ki ce wani abu nasan kina jin zafin ciwo sosai, don Allah ki bani izinin zuwa nayi wani abu, rayuwarki tana da matukar muhimmanci a duniyata".

 Izuwa lokacin Habeeba hayyacinta ya fara raguwa da ga gareta, kafafunta da take kansu suke taimaka mata wajan tsayi, ji tayi suna karkarwa alamun sun fara gajiya da rikita.

 Da sauri ta ja jiki zuwa kasa, tana dafa Mareeya ta zauna kan lamusshasshiyar katifar dake yashe tsakar dakin, har zuwa wannan lokaci idanuwanta a rufe suke, ita kadai ta san irin raɗaɗin azabar da take ji, ita kadai ta san irin zafin da take ji yana ziyarta ta.

 ɗan dake cikinta tana jin yarda yake juyi cikin wani irin yanayi na hanzari, yana tunkuɗo mata gurbin zuciya, ji take kamar zai tarwatsa mata kirji, zillo yake yi ta ko ina yana bugun ko wani sashi na cikin ta, ba abin da take hasashowa kanta a wannan matakin sai ficewar rai, domin ta gama yarjewa zuciyarta SILAR AJALINTA ya zo cikin duniyarta, matakin daukewar numfashinta ya iso rayuwarta, barin duniyar rayuwarta cikin yan dakiku take hangowa, lahirarta tana yi mata maraba lale, duniyarta nayi mata ban kwana.

Wani zillo da taji ɗan cikin nata yayi, da sauri ta durkushe bisa gwuiwowinta, tana faman sakin wahalallan numfashi wanda take jin fitar sa ma, wani raɗaɗi yake haifar mata a ruhi.

Sake damke hannun Mareeya tayi, wacce a wannan lokacin hawaye kawai take saki, tana kallon yarda mahaifiyarta ke yi cikin wahalallan yanayi ba abin zuciyarta ke hasaso mata sai uwarta ta mutuwa zata yi.

 "Umma sakar min hannu don Allah, naje na nemo mai taimaka miki kinji".

ta fadi cikin murya mai dauke da rawa da kuka a jikinta, ta shiga faman jan hannunta, domin kwacewa amma ina!. rikon da tayi mata ba mai sauki bane, kuka ta saki sosai tana jinjiga uwarta ta, tana rokon ta da ta sake ta, domin zuwa kiran wani ya taimaka mata.

 A hankali taji hannun uwarta ta na buɗewa daga rikon da tayi mata, cikin yanayi na rashin karfi jikin. sagalo tayi tana kallon hannun nata wanda cikin dakiku ta sakar mata shi, hakan ya kara mata jarumta, da sauri ta mike har tana cin tuntube zata zube kasa, ta fice daga cikin dakin. ba in da ta dosa sai dakin Goggo Marka, ko sallama ba tayi ba, ta fada dakin ta zube a gabanta, har wannan lokacin ta nan tana aikin ta na kaɗi. ganin Mareeya zube a gabanta ya sanyata tsayawa cak! da abin da take yi. tana dubanta cikin haushi ji take kamar ta kwasheta da mari, hannu ta shiga nuna mata.

 "Mareeya so ki ke yi ki nakasta ni, zaki fado min kai haka kamar buhun maiwa".

cikin kuka Mareeya ta dago kai, gami da riko kafafuwanta.

 "kiyi wa Allah Goggo ki taimaki Ummata karta mutu, na roke ki".

Fincike kafarta tayi, gami da mikewa tsaye tana gyara daurin zaninta.

 "kar uwarki ta mutu ko? wai shin in naje ni zan hanata mutuwa, ko ce miki akayi ni ce mala'ikan daukar rai ga mutum, kisan Allah in har baki tashi kin fice daga cikin dakin nan ba sai na karyaki, banza 'yar masu duhun kai".

 Kuka take yi na zuciya har izuwa kasan ruhi, ji take yi zuciyarta na raɗaɗi gami da zafi, idanuwanta suna zugi gami da zubda zafafan hawaye. jikinta na rawa da karkarwa duniya gabadaya taji tana kai kawo da ita, ba abin da take hasasowa sai yanayin da mahaifiyarta take ciki, ta tabbata a wannan yanayin da take ciki bashi da maraba da hanyar mutuwa, duk da dai ba ta san ya ake mutuwa ba, amma ta san hanyar mutuwa ba dadi gareta ba.

 Mikewa tayi tana duban Goggo Marka cikin hawaye.

 "Goggo na roki da Allah da Annabi ki taimaka ma Mahaifiyata. ina rokonki ko da wani abu tayi miki wanda kike ganin ba zai sa ki taimaka mata ba, to ina so duk wani hukuncin da zuciyarki ta yarje miki kiyi akan ta to ya komo kai na. ni dai alfarma nake nema ki taimaka mata ba don halinta ba".

 Sagalo tayi da baki tana kallonta, in ka ganta sai ka rantse tausayi da jin kai ne ya sanyata haka. amma saboda rashin sanin daraja sai ta sake kwaɓe baki gami da kau da kai.

 "ina gani bariki yau, ke yanzu Mareeya har kin yi girman da zaki sakar min magana haka to bari kiji ko Malam Lamiɗo (tana nufin kakan Mareeya) bai isa ya zo ya sani abin da ban yi niyya ba, don haka maza ki tashi ki fice mani daga daki, tun kafin na yi kutubal dake".

Hannu ta sa tana dauke hawayen da suke zubo mata, wasu na biyo bayan su tana kallon Goggo Marka kallo ne take yi mata na bakinciki, tausayi da imani sam babu su zuciyarta. gyada kai tayi tana nufi kofar ficewa daga cikin dakin, ba tare da ta sake kallon inda Goggo take a tsaye ba, ta yi sagalo sai faman watsa mata kallon banza take yi.

Zuciyarta tayi matukar yin baki gami da kuntata, zafin rai da take ji yana ziyartatta ya sanyata sakin wani kuka mai dauke da tashin hankali da takaici da baki ciki.

 Tsakar gidan ta tsaya, ta durkushe tana faman rerashi wanda ba shi da sauti, in ba kana kusa da ita bane ba za ka taba gane kuka takeyi ba. ta jima durkushe a wajan, domin rashin abinyi gabadaya kwakwalwarta ta cushe, ta rasa ina zata dosa, ta rasa meye abin yi, za ta so ace asibiti suka tafi kila can su samu taimako, sai dai ba anan gizo ke saƙar tasa ba, domin zata iya ratsewa rabon da suga naira biyar cikin dakin su mallakinsu ko ta ajiya sun fi karfin mako daya, to ina batun in sukaje asibiti ta sani kudi za a nema kafin ma akula mahaifiyarta ta shi kuma mahaifinta ba ta san inda zata same shi ba, rabon ta dashi yau kusan kwana uku kenan. ba ta san gun wanda za ta ba, ba su da yan uwa nan kurkusa balle taje domin su share musu hawaye, ba dangi wanda za ta ce gashi anan kusa wanda zai taimaka musu, ba ta san kowa ba, ba ta san gun wanda zata je ba, tunaninta ya tsaya cak ba ta da wata mafita.

 Kamar daga sama taji an dafa mata kafada, cikin hanzari ta dago fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye, mahaifinta ta gani wata irin zabura tayi, ta mike tana kallonsa. hannunsa ta rike jiki na rawa.

 "Baba Ummata ka taimaka min, za ta mutu na roke ka".

Yanayin da ya ganta ya san shi saurin riko mata kafadu yana girgizata.

 "mai ya sameta, tana ina?".

baki na rawa ta nuna masa daki. da hanzari ya nufi dakin yana mai rike da hannunta suka yi dakin.

 duk abin da suke yi Goggo Marka na kallo, tana laɓe jikin labulan dakin ta tun da taji muryar Adamu ta leko tana ganin sun shiga dakin, ta fito tana murmushi ita ma dakin ta nufa, cikin hanzari yanayin da ta nuna a jikinta sai ka rantse da gaske taimakon za ta je yi.

 Yana shiga ya tadda ta durkushe ganin haka, ya isa gareta da sauri yana ambaton.

 "innalillahi Habeeba meke faruwa ne, ko haihuwar ce?".

ya rikota yana mai girgizata idanuwanta a rufe, ya durkusa gabatan ya tallabo haɓarta.

 A daidai lokacin Goggo Marka ta iso tana marere cewa kamar gaske, ta isa garesu tana tafa hannu gami da salallami.

 "me nake shirin gani haka Habeeba meke damuki, baki da lafiya amma ki ka ki sanar dani, haba habeeba sam haka bai dace ba".

ta karashe cikin yanayi na rauni da tausayawa, rikota tayi tana mai cewa Adamu.

 "ina tunanin haihuwa ce ta zo mata".

gyada kai kawai yayi cikin yanayi na tsoro da halin da ya ga matar ta shi a cikin, tausayinta ya gama mamaye masa zuciya ya tabbata Habeeba tana cikin mawuyacin hali, lakari da yarda ya ganta aciki, wanda bai taba gani hakan ta faru a gareta ba, zuciyarsa ta shiga bugu da sauri ya dubi Goggo Marka.

 "ko dai Asibiti zamu wuce da ita".
Wata irin zabura tayi jin ya ambaci Asibiti.

 "haba Adamu haihuwar ce sai mun tafi asibiti, ai ko can muka je in dai lokaci bai yi ba haka zamu ta zama har lokaci yayi, ko kuma su saka karti su ta jagwalgwalata har su yi mata illa ko kuma su dakusar mata da karfin nata, su saka ta haihuwar dole tun lokaci bai yi ba, kadai mu bi komai a hankali, in lokaci yayi zata haihu".
ta fadi kamar gaske, tana faman rike Habeeba sai faman sannu take yi mata, sai ka rantse har kasar zuciyarta haka ne.

Ba yarda ya iya, haka ya gyada kai shi ma yana faman yi mata sannu. ita kuwa Mareeya mamaki da tu'ajibi ne suka cika ta, ta ma rasa abin cewa, ganin yarda Goggo Marka ta zage tana faman narkar da murya ita ala dole tausayi take ji, kamar ba ita bace ta gama kwashe mata albarka ba yanzu. girgiza kai tayi cikin yanayi na tsanar halin Goggo Marka.

 "Maza ke kuma ki tashi ki fice daga dakin, kin zauna kin kure mutane da idanu".

Goggo Marka ta fadi tana mai duban Mareeya tana galla mata harara ta gefen ido, ba wanda ya kula da hakan sai ita kadai kau da kai tayi, tana duban mahaifin nata wanda hankalinsa gabadaya yana kan matarsa, yana dubanta yana kallon yanayin da take ciki na tsananin wahala, zai so ace sun tafi asibiti da ita yana ganin haka shine kawai yafi dacewa, sai dai maganar Goggo Marka tayi masa katanga da hak,a ba don ya so ba ya dubi Mareeya da take ta faman ajiyar zuciya, hawaye sun cika mata idanu ya ja hannunta suka fice daga cikin dakin, zuciyarta sai faman azalzala take yi da tsoro don tana fargaban barin Goggo Marka da Uwarta ta kar tayi mata wani abu, domin irin kiyayyar da ta hango a idanuwanta komai za ta iya aikatawa.

 Can nesa da dakin ya ja ta ya zaunar da ita, yana mai rarrashinta da ta bar kuka In Sha Allah uwarta za ta samu lafiya, ita dai gyada masa kai kawai take yi, amma ba ta hango hakan ba. hankalin ta gabadaya ya karkata izuwa wajan uwarta da kuma Goggo Marka da aka bari tare da ita, tsoro take ji.

 Ba su jima da fitowa ba, Goggo Marka ta fito daga cikin dakin duk ta hada gumi kamar gaske. dubansu tayi gami da rausayar da kai ta wuce dakin ta, an jima kadan ta fito hannunta dauke da kullin abu, ba tare da tayi wa kowa magana ba ta samo kwano ta kwance kullin da ta ɗanko daga dakinta, wasu sauyoyi ne a ciki kwasa tayi ta zuba cikin kwanon mai dauke da ruwa ta shiga jujjuyawa, gaban Mareeya ya yanke ya fadi, ta zaro idanu tana kallon abin da take yi gabadaya hankalinta bai gamsu da abin da take yi ba, nan ta dubi Babanta, shima Goggo Marka yake kallo. sai da ta gama motsawa sannan ta mike ta nufi cikin dakin. da sauri ya tare ta da cewa.

 "Goggo wannan kuma menene?".

Murmushi tayi gami da margaya kai.

 "magani ne mace dake kan gwuiwa ake baiwa, domin samun sauki da kuma haihu sumulkalau ba tare da an samu matsala ba, yanzu ina bata shi in dai haihuwar ta zo to nan da nan zaka ga ta haihuwa abinta".

Ba ta tsaya jin abin da za su ce ba ta fada cikin dakin. izuwa wannan lokacin Habeeba sai faman numfashi take yi da nishe-nishe lokaci lokaci, gumi ya gama game mata jiki gabadaya. isa tayi gareta ta rangwafa gami da tallabo haɓarta dake kasa, ba tare da komai ba ta tura mata kwanon mai dauke da jikanken sauyoyin, wani hamami ne da daci suka dake hancinta da harshenta da sauri ta kau kai, duk da tsananin da take ciki bai hana ta tsanar wannan abin da ake kokarin ba ta ba.

Goggo Marka ta na ganin haka ta sake kakaba mata tana mai kashe murya.

 "hakuri zakiyi ki sha Habeeba, shi zai taimaka maki wajan samun saukin nakudar. duk wani ɗaci nashi daure wa zakiyi haka".

ta sake kai maka shi baki nan ma kau da kai ta sake yi, cikin tsananin kin abin ta shiga numfarfashi, a lokacin nakuɗar ta sake motsa mata ji take yi kamar bayanta da kwankwasonta za su karye, ta dago da jajayen idanuwanta cikin rashin hayyaci ta dubi Goggo Marka wacce ta ke ganinta tana kasuwa gida bibbiyu a gareta, ta mai da kanta kasa tana mai sakin numfashi. ita kadai ta san halin da take ciki, ita kadai ta san azaba da raɗaɗi da take ji a kowa ni sashi na jikinta...
Post a Comment (0)