UKU BALA'I
NA
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA BIYU.
Awa daya tsakani amma shiru kake ji, ba wani cigaba wanda za ace na a zo a gani, har hankula su saka ran samun natsuwa.
Malam Bello zuciyarsa ta gama karaya matuka, ji da yayi shiru ba alamun haihuwar, anyi ta ko ba ayi ta ba, ya rasa matsayar da zai ajje zancen zucin sa.
Numfashi yake ta faman ajjewa, sai ka rantse shima nakuɗar ce akan sa, ya dubi Mariya wacce ta ke cikin yanayi na faduwar gaba da rikitar zuci da ruhi, duk hannaye biyu ta saka ta tallabe haɓarta, idanuwanta sun yi jajir hakan ya kara tsinke masa natsuwar zuciyarsa, sai faman bugu take yi tana yaso masa wani banzan zance wanda ba shi da muradin ace ya tabbata cikin duniyarsa, in kuwa haka ya tabbata ko shakka ba ya yi zai fi kowa ruɗewa cikin duniyarnan. a hankali ya shiga ajje numfashi, yana kallon dakin da Matar tasa take wanda ya tabbata izuwa wannan lokacin mutuwa ta zo kusa da ita. Da wannan zancen zucin ya kokarta mikewa yana faman hirji kamar zai ci babu, ya doshi dakin cikin bugun zuciya da ruhi.
Yaye labulan yayi cikin rashin tabbacin abin da zai gani, duk da dai zuciyarsa tana yi masa kuwwa akan ba sauki sai wajan Allah. idanuwa da numfashinsa gami da bugun zuciyarsa a lokaci guda suka shiga rudu, ganin yanayin da ya ga Habeeba a ciki, da hanzari ya fada dakin ya dubi Goggo Marka, wacce ke zaune can gefe ta zubawa Habeeba idanu, ba wani alamun tashin hankali tattare da ita, maganar Malam Bello ne ta dawo da ita duniyar rauni, da kokarin yafawa fuskarta yanayin tausayi, ta shiga duban shi.
"ka gani ko, har yanzu ba alamun haihuwar ina ga dai lokaci ne baiyi ba, ko kuma juyi ne".
Ta fadi cikin yanayi na kara narkewa a tausayi.
Gyada kai kawai yake yi, kamar wani kadangare yana faman jan numfashi yana ajjewa, idanuwansa da hankalinsa har da natsuwarsa duk suna kan matar sa, sake ajje numfashi mai kauri yayi.
"Goggo kawai mu tafi Asibiti".
ya dasa aya yana kokarin isa wajan Habeeba. Da sauri ta tare shi.
"a,a mana Bello, mai yasa zaka nuna gajen hakuri ne, na fada maka in haihuwar nan ta zo yin ta za ayi, amma na ga alamun taurin kai za kayi. haba don Allah ko fa Asibitin muka je hakance zata kasance".
Bai amince ba, bai yarda ba da maganar ta sam. bai hango É—a mai ido ba cikin wannan lamarin, don haka ya dube ta sosai, cikin karyar da murya.
"Goggo zuwa Asibitin shine ya fi dacewa, domin zaman gidan ba karimin hatsari zai farar ba".
Duban sa tayi, cikin shan kamshi.
"me ka ke nufi Bello, kana nufin a matsayina ba zan iya amsar haihuwar ba ne ko yaya?".
Girgiza kai ya shiga yi, cikin yanayi na rashin natsuwa.
"ba haka bane Goggo, ya kamata ki fahimta wani abu, kin ga can asibiti in muka je ko ba haihuwa ba ce su sun san abin da ya dace suyi mata, domin ganin komai ya zo yarda ya dace, amma zaman gidan ba abin da zai haifar sai dai ya je fa mu a ruÉ—u da rashin abin yi kawai, sai dai mu sata gaba muna kallo".
"ba in da za a kai ta Bello, na fada maka ka duba fa ka ga yanayin da take ciki, alamun ya nuna haihuwar gaf take da yin ta yanzu, in muka dauke ta cikin wannan halin komai zai iya faru a hanya, za ta iya haihuwa a titi me kenan akayi?".
ta fadi cikin yanayi na rashin jin dadin maganganunsa, ta yafa wa fuskarta yanayin kamar gaske ta shiga cizon laɓɓa, sai ka rantse zage ta yayi tas.
Wani marainin nishi Habeeba ta saki, wanda da kaji amonsa kasan wahala ce tsagwaronta ba mis a cikin ta, hakan ya kara ruguza 'yar natsuwar Bello, ya shiga dubanta sai faman fadin "Sannu" yake yana ji azuciyarsa har da can kasar ruhinsa kamar bai yi mata adalci ba, in har ya yarda da batun Goggo. sai dai kuma a wani bangaren in ya ki amsar maganar Goggo, kamar kin biyayya ce a gareta. duban Goggo yayi ya sake juwa wajan Habeeba, wanda ko tantama ba yayi mutuwa tana kurkusa da ita, in kuwa mutuwa ba ta zo ba to tabbas bakar izaya da wahala tana É—awainiya da gangar jikinta da zuciyarta.
"kiyi hakuri Goggo, mu kai ta asibiti...".
Wani kallo ta watsa masa, kafin ta fara magana cikin É—aci.
"wai shin in tambayeka yau ta fara haihuwa ne a duniyarta, na dauka ta haifi Mariya kuma a gidan nan ta haifeta, ba tare da zuwa wani waje ba. to bari kaji na fada maka ba in da zata, a gida zata haihuwa kana kallo fa na bata magani rage zafin nakuda, da zuwan komai a sannu kuma da ka kalle ta za ka san maganin yayi aiki..."
Da sauri ta katse batunta, lokacin da taga wani ruwa ya fara gangarowa daga kasan Habeeba.
"ka gani ko. har faya ta fashe haihuwar ma ta zo nan kurkusa, sai ka fice ka bamu guri ko a nace".
Ta kareshe tana galla masa harara. da sauri ya dubi Habeeba, yana kallon yarda ruwan da bai san na menene ba, yake zubowa daga jikinta wanda ya tabbatar da zancen Goggo din, amma bai amincewa kan sa ba, har can kasar ruhinsa. ba yarda ya iya haka ya fara jan jiki yana kallon Habeeba, yarda take wani irin nishi da murkususu kamar za a zare mata rai.
Zuciyarsa ta kara yin rauni, ganin yarda Habeeba ke shan wahala. in da yana da yarda zai yi da ya dauke mata wannan azabar ya daurawa kan sa, amma ina! ba hali, haihuwa mace ce kawai take da wannan alhakin nayin ta, wanda ba komai bane a cikin ta sai tsatsar azaba da wahala, tausayinta ya kara tsargar masa a jiki. da wannan yanayin ya isa inda Mariya take zaune, ta na ganinsa ta mike idanuwanta akansa, sai nar-nar suke alamun son zubda hawaye, tana kokarin yin magana ya yi saurin riketa ganin kuka na kokarin kufce mata, ya shiga girgiza kai kamar wani d'an kadangare.
"karki yi kuka Mariya, komai tsanani yana tare da sauki da yardar Allah, kuka sam bai ka mata ba..."
da sauri ta tareshi, tana mai gyada kai, hawayen da take boye su suka shiga zubowa, kamar an murde kan rubabben famfo.
"Abba Umma ta ina son ta, bana so na rasata don Allah ka taimaka mani ka taimaka mata, mu kai ta asibiti kar ta mutu ta bar mu cikin duniyar nan, ba zan iya rayuwa ba na rokeka".
Ta karashe tana mai zubewa a kasa, kamar wacce aka bugewa gwiwowi ta shiga sakin kuka mai cin rai da tsuma zuciyar mai sauraro.
Kallonta yake yi, cikin wani irin hali na tausayawa zuciyarsa gabadaya ta gama raunacewa ji yake yi kamar ya daura hannu saman kai, ya zunduma ihu. wani radadi da zafi gami da zugi yake ji suna taso masa, tun daga kasar ruhi har zuciya gabansa sai amsa wani irin bugu yake yi mai dauke da kayan tashin hankali cikin sauri-sauri. dafe kai yayi da duk hannayensa ya rasa mai ya kamata yayi, ya rasa mai ya dace yayi, domin samo mafita akan wannan lamarin dake kokarin janyo masa tashin hankali. ya rasa da mai zai ji, ya sani Habeeba na cikin halin wahala dole ya nemi mafita, dole ya kai ta asibiti, in da yake tunanin nan ne kawai ya dace ace a halin da take yanzu tana can. sai dai wani hanzari ba gudu ba, Goggo Marka ta hana yin haka, ya rasa mai yasa ta kasa fahimtarsa, ya rasa mai ya sa taki yarda ta amshi rokonsa, ya rasa mai yasa take kokarin janyo masa abin da zai haifar masa da tashin hankali, taki fahimtarsa, taki gane matsalar da yake hangowa za su fad'a, ya kamata ta fahimta zamanin da da yanzu ba daya bane, komai ya sauya kamar yarda komai na cikin duniya ya sauya, haka zamani yake sauyawa da abubuwa masu dauke da karin haske ga duniyar dangin rai sai dai taki amincewa da cewa ZAMANI YA CANZA.
"Abba don Allah kar ka bari maganar Goggo tayi tasiri a zuciyarka, har ta hanaka ceto rai".
Mariya ta fadi cikin rawar murya, tana duban mahaifin na ta, cikin kasalallan yanayi.
Gyada mata kai ya shiga yi, kafin ya ja jiki ya fice daga cikin gidan, ya bar ta nan tallabe da haɓa.
Bakin titi ya nufa, mai Napep ya dauko ya dire kofar gidan, ya ce dashi ya jira shi cikin gidan ya fada cikin jarumar zuciya, a daidai lokacin Goggo Marka ta fito daga cikin dakin a firgice saura kadan suyi karo, idanu ya zuba mata yanayin da ya ganta ya sanya gabansa tsananta bugawa, ita kanta Mariya ba karamar razana tayi ba da sauri ta bi bayan mahaifinta, ganin yanayin da yake ciki yana fadawa cikin dakin yayi daidai da karar da Habeeba ta saki, gami da bingirewa jini na malala ta karkashin ta, ga kan jariri ya yo waje bai san lokaci da ya isa gareta ya durkushe gami da tallabo haɓarta, zuciyarsa ta buga lokaci guda ganin da yayi ba alamun numfashi a jikin ta, hakan ya kara masa firgici, zabura yayi gami da ficewa waje, cirko-cirko ya tadda da su, Goggo Marka tallaɓe da haɓa kallo daya zakayi mata ka hango rashin gaskiya da firgici kwance a cikin idanuwanta, ita kuwa Mariya hannu ta daura akai ganin yarda mahaifinta ya fito, ta kurma ihu gami da zubewa kasa tana fadin.
"Shikenan rayuwa ta gurgunce a duniyata, shikenan na bani na lalace a rayuwar duniya, shikenan tsanin rayuwata ya karye...".
Da sauri ya isa gareta, ya dago ta.
"Mariya daina fadin haka, wa ya sanar dake ta mutu, ta na nan da ranta".
ya fadi yana mai juyar da kallon sa wajan Goggo Marka da tayi wuki-wuki kamar wacce tayi wa sarki karya, girgiza kai yayi, da sauri ya koma cikin dakin dalilin wasu lamura da zuciyarsa da kwakwalwarsa suka shiga sanar dashi, cikin jarumtar zuci da na jiki ya shiga gyara mata jiki, idanuwansa cike da hawaye ya dagota gabadaya ya rungume ta, ya fice daga cikin dakin cikin hanzari ba in da ya direta sai cikin Napep, shi kansa mai Napep din ya tsorata da yanayin da ya ganta aciki, da sauri ya shiga ciki gami da tayarwa, Malam Bello gabadaya ya gama ficewa daga hayyacin sa. kwalla da suka taru masa a idanu sai shatata suke kamar wani karamin yaro. har Napep ya fara kokarin tafiya, sai ga Mariya ta fallo a guje tana kuka, tana mai cewa da mai Napep din ya tsaya don Allah, amma Malam Bello ya ce su tafi kawai don yasan in har Mariya ta biyo su, kafin su kai sai hankalin su ya kara tashi musamman in da take nan a firgice, yana hangota tana daga masu hannu tana kiran su cikin muryar kuka. kai ya shiga girgiza mata, yana mai daga mata hannu alamun ta koma gida. amma ina kuka ta sake rushewa da shi gami da durkushewa, ta saki wani sabon kukan mai cin rai da tsuma zuciya, kuka take yi kamar ranta zai bar jikinta, wani zafi take ji tun daga kasar ruhinta har zuwa inda zuciyarta ke ajje. ta gama yanke tsammani akan sake ganin mahaifiyarta a duniyar rayuwarta dauke da numfashi, zuciyarta ta gama yarje mata sun yi rabuwa kenan har gaban abada, ba za su sake haduwa ba.
ta ji ma cikin wannan halin. kafin ta kokarta cikin jan jiki ta mike tana faman tangadi, duniyar gabadaya ji take tan juya mata, komai ya kwance mata, komai ya lalace cikin duniyarta, kayan farinciki tuni suka guje suka barta, ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, kwakwalwarta ta na faman kai kawo cikin duniyar tashin hankali da rashin tsammanin samun sa, sannu a hankali take tafiya idanuwanta a rufe jefa kafa kawai take yi a duk in da taji kafar ta ta, ta bata damar haka, cikin ikon Allah ta isa kofar gida, tana kokarin sanya kai cikin soron, sukayi karo wani irin zafi da raɗaɗi ta ji goshin ta ya dauka, da sauri ta buɗe idanunta tana dafe goshinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata. Goggo Marka. ta gani tsaye idanuwanta akan ta, sai faman tsume fuska take yi. kau da kai Mariya tayi, tana mai jin zafi rai suns dago mata da duk wani numfashinta, ta fara kokarin rakuɓeta za ta wuce, wani wawan cafka ta yi wa wuyanta, ta dawo da ita gabanta.
"ke mai uwa ko, shine saboda rashin sanin darajar kai, ki ka zube a titi kina kwarar baki. to dan uban ki in ba duniyar kika dauke da ihu ba, za a kashe miki uwa ba ki cika Mariya jikan LamiÉ—o ba shegiya bakar munahika kawai.
Girgiza kai ta shiga yi,hawaye na sake balle mata sam maganganun Goggo ba su taba mata zuciya ba, domin tashin hankalin da take ciki ya zarce duk wata bakar magana ko zagi da za ayi mata, hannu ta sanya ta dauke hawayen da suka cika mata idanu ba tare da ta sake bin ta kan Goggo ba, ta sake yinkurin shigewa cikin gidan. a wannan karon ba ta hanata ba, sai kwaɓa da tsaki da ta bi ta dashi.
Tunda suka dauki hanyar Asibiti, Malam Bello ke rungume da Habeeba. ba abin da yake yi sai zubar hawaye, har zuwa wannan lokaci jini bai daina zuba a jikinta ba, gabadaya shimfidar cikin Napep din ta baci shi kasan direban lokaci-lokaci yana juyowa ya dube su, domin ba karamar firgita yayi ba, sai faman zabga gudu yake yi kamar zai tashi sama, burin sa kawai su isa Asibiti, domin ceto ran Habeeba.
Mintina goma kacal ya kai su Asibitin baban alis, yayi Parking gami da direwa, da gudu yayi cikin Asibitin yana mai sanar da Nurses su taimaka wata ce ba ta da lafiya, yanayin da yake ciki na rashin hayyaci, sai ka rantse uwarsa ce ba lafiya amma Nurse din ba wanda ya bi ta kasan, kowa harkar gabansa yake yi, mutanan da suke zazzaune sai faman bin sa da kallo suke, cikin yanayi na tausayi, domin sun tabbata ba abu ne mai sauki zai firgita duniyar tunanin wannan matashin ba. tun yana neman daukin su, su kula shi amma ba wacce ta kulashi, sai da ya isa kusa da wani teburi ya shiga duban matar dake zaune, ta na ba da katin ganin likiti, ya dubeta.
"don Allah ku taimaka likita, haihuwa za tayi jini na ta zuba a jikinta".
dago kanta dake sunkuye tayi, tana dubansa cikin gilashin dake fuskarta.
"ka je ku shigo da ita, sannan kuma ku kawo katin da take zuwa awo dashi, domin ba za a taba ta ba, har sai an bada kati".
da mamaki ya shiga dubanta, ganin yarda ta nuna halin ko in kula akan lamarin. ji yayi kamar ya dauke ta da mari, amma ya kasa. da sauri ya juya zuciyarsa na zafi da radadi irin yanayin da ya ga Nurse sun nuna masa, da sauri ya isa wajan Napep, ya tarar Malam Bello, na kokarin fito da ita wacce a wannan lokaci kallo daya zaka yi mata, ka bawa zuciyarka amsa cewa ba ta da rai.
Cikin Asibitin yayi da ita tana rungume a hannunsa, mutane da yawa sun tsorota matuka da yanayin da suka ganta, suka shiga sallallami suna zaro idanu, Malam Bello, da ke rikice ya rasa ma in da zai yi da ita, sai faman zarya yake yi magana ma ta gagare shi, duk abin da yake da yawa Nurse na kallon sa, amma sai dai su ba banza ajiyarsa. ciki mutanan dake zaune a harabar asibitin wasu mata biyu suka iso gareshi,tare da taimaka masa, zuwa daya daga cikin dakin Asibitin. a daidai lokacin Nurse mai siyan da kati ta iso cikin dakin, tana duban Malam Bello. wanda gabadaya ya gama yin nisa da hayyacin sa. tambayarsa take, amma ya rasa bakin bata amsa, sai motsi yake yi da baki, daya daga cikin matan da suka taimaka masa ne ta dubi Nurse din.
"wannan ba fa shi ne mafita ba, ya kamata ko taimaka mata ki duba halin da wannan baiwar Allah take ciki, mana maganar kati duk ba shi da muhalli a halin da ake ciki, ceto ranta take bukata".
Kau da kai tayi, tana mai ya tsine fuska.
"ke ma kin san haka ba za ta taba yuwuwa ba, dole sai da katin ta na shaidar ta na zuwa ganin likita, sannan za a kula da ita".
Ta karashe maganar ta tana kokarin ficewa. da sauri dayar matar wacce da alamu haushi ya cikata, ta sha gabanta tana yi mata kallon na raina matsayin ki.
"wai ke kuwa kina da ita imani, baki san zafin da raÉ—aÉ—i bane a wajan haihuwa bane, ba ma haka ba, wannan fa yar uwarki ma cece, ya kamata ko don wannan matsayin da kuke daya ki taimaka mata".
Kallo uku ahu tayi mata, kafin ta gyara zaman gilashin fuskarta.
"karki jefe ni da wasu kalamai munana, karki ga laifi ne akan wannan lamarin, ke kanki sani, duk wata mace mai ciki in dai ta zo haihuwa sai an bukaci katin zuwa awonta, kafin a dubata...".
"wannan ba hujja mace malama".
Mai Napep ya katse mata maganar da take yi, cikin zafin rai ya dora da cewa.
"wannan maganganun da kike duk na banza wallahi, na lura ba ki da imani sam ke da wasu likitocin da kuke aiki, in har haka likitoci suke sam ba su yi ba a duniyar nan ko daya, ke ba zan musu kudin goro ba, dama komai na duniya akwai na gari akwai kuma bara gurbi, to ke ki na sahun bara gurbin wallahi".
Yanayin da yake maganar cikin zafin rai kamar zai rufeta da duka, ya fadar mata da gaba, nan ta shiga duban su daya bayan daya har takai ga Malam Bello, wanda idanuwansa gabadaya sun gama rinewa kamar wanda aka watsawa barkonon tsohuwa girgiza kai tayi gami da cewa daga dakin, adaidai lokacin Habeeba ta saki wani nishi wanda ya sanya gabadayansu suka dire akanta, numfashi take saki cikin wani irin wahalallan yanayi mai dauke da rashin hayyaci, idanuwanta a rufe amma hakan bai hana hawaye zubowa ba, Malam Bello ya isa gareta, gami da riko hannunta ya na ambatar sunanta, cikin murya mai taushi da tausayi, girgiza kai ya ga tana yi hawaye na kara balle mata, bakin sa na rawa ya shiga kokarin yin magana amma kamar wanda ka daurewa harshe maganar taki fitowa, ya shiga goge mata gumi dake ta faman tsantsafo mata a goshi. a daidai wannan lokaci wani dirkeken mutum, wanda da kallaeshi za ka gane babban likitane, yana gaba Nurse na biye dashi har ya iso inda Habeeba ke kwance, dubanta yayi sosai kafin ya komar da kallonsa izuwa wajan Malam Bello, wanda yake ta famam ajiyar zuciya.
"mai ya sa haka, mai yasa har kuka bari hakan ta kasance a gareta?".
ya fadi cikin murya mai nuna bacin rai. Girgiza kai ya shiga yi cikin rashin abin cewa, likita ya sake dubanta.
"ina katin ta wanda take zuwa ganin likita da awo dashi".
Nan ma girgiza kai yayi, alamun babu kenan.
Da sauri likitan ya dube shi cikin alamun zaro idanu waje, da madaukakin mamaki da kuma haushi.
"hakan da kuka yi sam bai da ce ba, ka ga yanzu kun haifar mata da matsala, domin duk wanda ya kalleta ya san tana cikin halin wahala, ya kamata kuke lura mace mai ciki tana bukatar taimako da kulawa da tattali, tun daga lokacin da ta samu ciki ya kamata ace tana zuwa Asibiti, a ko wani bayan sati uku tana ganin likita, hakan ne zai bata damar sanin halin da take ciki da abin dake cikin ta. kar ku ga laifin abinda wasu likitoci ke yi na rashin bada kulawa ga mai ciki, hakan na faruwa ne ta dalilin mai ciki da kum mijinta...".
"kayi hakuri likita don Allah, a bar zancen nan, ya kamata ace ku san abin yi akan wannan baiwar Allah, domin tana cikin hali mara dadi".
Daya daga cikin matan dake wajan ta fadi, cikin yanayi na rauni.
Murmushi likita yayi ,kafin ya shiga duban Habeeba, daga karshe ya umarce da su dauke ta domin zuwa dakin haihuwa, yana tsammanin haihuwar ce ta zo, cikin hanzari kuwa sukayi hakan. likitin ya kira Nurse uku, sukayi masa jagora domin kula da Habeeba, Malam Bello da sauran matan suka koma harabar Asibitin suka yi cirko-cirko, mai Napep nan yayi wa Malam Bello Sallama tare da fatan samun lafiya ga Habeeba ya tafi. ba tare da ya amshi ko sisin sa ba.
Sai da suka shafe mintina talatin, amma har zuwa lokacin ba alamun haihuwar za ta yiwu, tun likitar na tsammani har ya fara yanke tsammani. iya kokarin sa yayi amma bai kai ga ci ba, ga dai kan jariri a waje amma fitowarsa ya gagara, duk wani taimako yayi amma ina domin gabadaya jaririn ya cije ba alamun zai fito, dalilin kin buduwar kwankwason ta, yaki budewa balle jaririn ya fito, iya wahala Habeeba ta gamu da ita, shi kan sa jaririn wahala ta sheshi, ganin wanki hula na kokarin kai su dare, nan likiti ya fito ya ja hannun malam Bello, zuwa Office din sa, yayi masa bayani, ba karamar kaduwa yayi ba, nan likita yace in ya yarje ayi mata aiki, domin shine kadai mafita agareta, da ma jaririn domin kar azo ayi BIYU BABU.
Shiru yayi yana tunanin lamarin, ba wai aikin ne ba ya so ayi mata ba, a,a kudin aikin in da zai samo su, ita ce matsalar. domin kuwa a yanzu halin da ake ciki ko dubu biyu na sa takan sa ba shi da ita, balle wasu makudan kuÉ—aÉ—e da yake tsammanin za a nema a gareshi, numfashi ya ajje ya dubi likita wanda ya gama karantar halin da Malam Bello ya ke ciki.
"Likita ba wai ba zan iya sa hannu ba ne, a,a abin neman ne babu...".
Hannu likita ya daga masa, yana kokarin yin magana. kamar daga sama Nurse ta fado cikin office ta dubi likita.
"Sir ina tunani za ta iya haihuwa da kanta...".
Tun kafin ta dire, ya miki zumbur cikin hanzari, ya fice daga office din .Nurse ta biyo shi a baya tare da Malam Bello.
yana shiga dakin ya tadda sauran Nurse din akanta, yanayin da ya ganta da irin nishin da take saki ya kara sanya jin tausayinta, da sauri ya isa gareta, izuwa wannan lokacin kafaÉ—ar jaririn ta yo waje, hakan ya tabbatar masa za ta iya haihuwar da kanta, a hankali ya fara kokarin janyo jaririn a hankali a hankali yake bi har ya zo matakin tsakiya, wato saitin cikin jaririn. a lokacin ta yi wani nishi mai dauke da wata hargitsattsiyar kara, wacce ta amsa kuwa gabadaya dakin. a sa'ilin da shi kuma jaririn ya fado duniya gabadaya. zubewa tayi daga kan gwuiwowinta numfashin ta na fita, cikin wani irin yanayi...