WANI KAMFE DA BA'A TABA YIWA BUHARI BA DAGA BAKIN SHEIKH JA'FAR MAHMUD ADAM (R)

WANI KAMFE DA BA'A TABA YIWA BUHARI BA DAGA BAKIN SHEIKH JA'FAR MAHMUD ADAM (R)


Kuji daga bakin Malam:

"Ba mu da wani mutumin da muke sa masa rai wajen dawo da tsari da farfado da tattalin arzikin kasa da gyara harkar ilimi, noma tabbatatar da tsaro a mukamin shugaban kasa da ya wuce janaral Buhari.

Don haka ya zama dole a gare mu, ya zama wajibi akan mu, ya zanto tilas a kowanne daya daga cikin mu, mace ko namiji ya tabbata amana ce tsakanin sa da ubangiji ya jefa ma wannan bawan Allah kuri'a dan ya samu damar hawa mataki na shugaban kasa ya zama wajibi akan kowane daya daga cikin mu ya dage da addu'a ya kashe wani bangare na kudin aljihun sa daga yanzu har ya zuwa lokacin da za'a kada kuri'a wajen tallafa ma tafiyar, kokarin, yunkurin tabbatar da cin nasarar janaral Muhammadu Buhari.

Ubangiji muna rokon ka da sunayen ka, muna rokon ka da siffofin ka, Ya Ubangiji ka damka masa amanar shugabancin kasar mu, ya ubangiji ka bashi nasara. 

Ya ubangiji duk wadanda suka tsaya wajen suga sun kadar dashi ya ubangiji ka tade kafafun su, ya ubangiji ka gadar masu da tabewa da hasara, wannan shine abunda ke wajibi akan mu , mu sani cewa kasar mu tana fama da matsaloli: Matsaloli ta fuskar tsaro, matsaloli ta fuskar koma bayan ilimi, matsaloli ta fuskar tattalin arziki, matsaloli ta fuskar wargajewar al'amura, rashi zaman lafiya.

Kashe kashen da akayi cikin shekaru uku ko hudu kadai na wannan gwamnati irin wadanda ba'a taba yin su ba tun daga lokacin da akayi yakin BASASA a Nijeriya, kudaden da Najeriya ta samu a wannan lokaci na cikin shekaru hudu kudadden ba'a taba samun irin su bane tun daga lokacin da aka kirkiro nigeriya.

Amma kuma shine lokacin da mutane suka fi zama cikin halin kunci da shiga halin kakani kayi, don haka ya zama wajibi a gare mu muyi kokarin kawo canji, ubangiji ta'ala ya jarrabe mu da shugabanin da basa jin tausayin mu, ya jarrabe mu da shugabanni masu fasadi wadanda basa tunani cikin duk abunda yake gyara ne, wadanda zuciyar su babu wani gurbi na tunanin talaka mai karamin karfi a cikin zukatan su, in ba yan kadan ba can da can.

Don haka sai ya zama dole akan dukkan wani mai hankali, masanin ya kamata, mai tunani nagari ya ga yaya zaiyi yayi yunkuri da an kawo canji a cikin wannan lokaci".

Allahu akbar! Gwani na ba'a bin ka bashin hujja.

Allah Ya jikan Malam, Ya kai haske kabarin Sa.
Post a Comment (0)