21. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
....
Akwai madinka da yawa, akwai dukawa da makera. Kuma akwai lokaci musamman na farauta, don kusan ko wane mutum ya iya harba kibiya. Duk aike-aiken nan da 'ya'ya da bayi su kan taru wurin yinsu. Irin sana'ar ubangiji ita zai koya wa bawansa.
Bai kamata ba mutum ya ba da labarin halin zaman mutanen Afirka, ba tare da ya taba maganar bauta ba. Lalle an sani a zaman dan Adam ba shi yiwuwa kowa da kowa a zama daidai, lalle wani ya fi wani daraja ko arziki. Amma im fifikon nan ya hana mutum ikon yin kome sai da yardar wani, al'amarin ya zama bauta ke nan. To, a cikin wannan hali mutanen Afirka su ke zaune tun farko.
Yawan bayi a Afirka sun riba yawan 'ya'ya. Ba a bukatar kome da su sai aiki. Shi a ke sa su kullum, kome dari, kome rana, kome ruwa. Ba su da ikon zaben lokacin farawa, balle na tashi. In sun duka sun duka ke nan, sai an ce su bari. Kuma duk abin da suka yi sun yi wa bauta ne, ba su da ikon tambayar wata lada ko biya. Amma duk da haka, a shari'ar kasar, akwai wadansu abubuwa na wahalarwa wadanda ubangiji ba shi da ikon yi wa bawansa. In ya yi, tilas za a sa ya sayad da bawan. Akwai bayi iri uku bayin yaki, da kuma 'ya'yan da bayi suka haifa a gidan ubangijinsu, da bayin bashi. Na karshen nan su ne wadanda suka ci bashi suka kasa biya. Al'adar Afirka kuwa, mabarci yana iya kama mai bashinsa ya zama da shi bawansa. Im bai same shi ba, ya kama dansa, im ba da ya kama wani cikin danginsa, har ma im ba dangi ya kama mutumin garinsu. Ban da su kuma, akwai wadanda yunwa ta kan sa su mai da kansu bayi bisa tilas. Su kan tafi wurin wani mai abinci su sayar masa da 'yancinsu, don su sami abin da zasu ci. Ko da ya ke sun san bauta mugun abu ne, amma sun fi tsoron mutuwa da ita.
Yadda sha'anin bauta a Afirka ya ke, ke nan, amma na tabbata babu masu kara wa wannan mugun abu karfi kamar Turawa da su ke zuba kudinsu don su sayi bayi. Ba don kasuwar da suka bude ba, da cinikin bai kasaita haka ba. Amma kuma inda za a ce a kashe bauta yanzu, a ganina, kashewar ba za ta yi wani babban amfani ba ga ainihin su bayin, don kuwa galibinsu ba su iya komawa garinsu, tilas su tabbata a gidan iyayen gijinsu.
KAYA MASU DARAJA WADANDA A KE SAMU A AFIRKA
Tun shekara aru aru sunan Afirka ya shahara a duniya wajen samun zinariya da hauren giwa. Su duka kuwa abubuwa ne masu daraja kwarai da gaske. Kusan duk inda aka tona a kasar Mandingo da Jallonkadu za a sami zinariya. Maza su ke haka zinariya, amma mata ke wanke ta. Amma ni ban taba shiga cikin ramukan nan ba, balle in san zurfinsu, da irin yadda a ke hako zinariya daga cikinsu. Abin da ya hana ni kuwa, don kul bako ya yi karambanin wannan sai su kore shi. Balle ni ma, wanda a ke yi wa zaton dan rahoto ne ?
Galibin zinariyar kera ta su ke yi, suna yin kayan ado kamar su abin wuya da ’yan kunne, da warwaro, da mundaye. A cikin wadannan duka abin wuya ya fi su kyau. don kuwa shi ba zinariya ce zalla ba, su kan zura shi tare da wadansu duwatsu masu kyau. Im mace mai sukuni ce, kudin kayan adonta na zinariya ya kan yi kamar fam hamsin. Bayan sun kera kayan ado, sai su sayad da sauran wajen fatake su sayi gishiri.
Hauren giwa kuwa ba shi da wani amfani gare su, ba su san darajarsa ba. Babu abin da ke ba Bakin Mutum mamaki kamar ganin yadda Turawa ke wasoson hauren giwa. Ko da ya ke a kan nuna musu kotocin wuka da su matsefi, da abubuwa da yawa wadanda a ke yinsu da shi, amma ba su yarda. A zatonsu Turawa suna maishe shi wani abu ne mai daraja a Kasarsu, saboda haka suna boye wa Bakin Mutum don kada ya sani, balle ya sayar musu da tsada. Sun ce don yin kotar wuka kurum ba shi yiwuwa a yi tafiya tun daga Turai a zo Afirka a sayi haure.
Na ga Afirka kasa ce wadda ke cike da arziki, amma galibin kayan amfanin da ke ciki har yanzu mutanen kasar ba su san su ba. Bayan zinariya da hauren giwa, akwai su zuma da kakinta, da kirgi, da fata, da karo, da sauran irinsu. Wadannan ga su nan ko'ina a kasar, kuma a yalwace. Akwai kuma taba, da baba, da auduga, amma ba su sayad da wannan. Hajja iri uku kadai aka fi fita da su da yawa daga Afirka, da zinariya, da haure, da bayi.
Kun ji yadda mutanen Afirka su ke zaune. Kun ji irin al’adunsu da sana‘o’insu. Kun ji irin dukiyar da ke dankare cikin kasarsu, da wadda suka san da ita, da wadda ke boye gare su, ilminsu bai kai su san ta ba. Kun kuma ji irin masifar da ’yan Adam dubbai, wadanda a ke kira bayi, su ke sha. Mutane ne kamar kowa, ba su yi laifin kome ba, ba su taka ba, ba su zubar ba, amma an hana musu ’yancinsu. Aikin da dabba za ta yi shi za su yi. Yadda ba a biyan dabba ladan aiki, haka su ma ba a biyansu. Yadda a ke sayad da dabba, haka a ke sayad da su. Ni a ganina, babu abin da wannan kasa ta Afirka ke da kishinsa sai a waye kan mutanenta, a yaye musu duhun jahilci yadda za su gane daidai da rashin daidai. In na dubi arzikin kasar, ga shuke-shuke iri iri, ga kasa mai nagartar noma, ga dabbobi ba iyaka, ga koguna manya wadanda za a yi ciniki a kansu da manyan jiragen wuta, ga karafa a cikin kasa, sai in ga ba daidai ne al’umman da idonsu ya waye su kyale mutanen kasan nan cikin duhu da talauci da masifa haka ba.
Wannan shi ne abin da idona ya nuna mini game da Afirka da mutanenta.
Zaman da na yi a Kamaliya ya amfane ni kwarai, don na sami damar rubuce irin abin da na gani da wanda na ji. Ba ni da yunwa, ba kishirwa, domin lokacin da Karfa zai tashi ya sa ni a hannun mutumin kirki ne, mai kyakkyawar dabi’a. Sunansa Fankuma. Kuma ko da ya ke Musulmi ne tamman, amma bai damu da addinin kowa ba. A kullum ba shi da wani aiki daga karatun littattafai sai karantad da yara. Yana da almajirai goma sha bakwai, daga ciki biyu mata ne.
Bayan Alkur'ani, na yi mamakin ganin yadda mutanen Afirka ke son karanta Attaura da Zabura da Linjila. Ban taba zaton littattafan nan sun ketaro wannan jiha ta Afirka ba. Mutanen sun gaskata littattafan duk zancen Allah ne. Sun ce Attaura Allah ya saukar wa Annabi Musa, Zabura ya saukar wa Annabi Dawuda, Linjila ya saukar wa Annabi Isa, Alkur'ani ya saukar wa Annabi Muhammadu. Na lura lalle Bakin Mutum yana da kishin ilmi, yana kuwa da himmar nema in ya sami sarari.
A kwana a tashi, ran nan sai Karfa ya komo. Kwana biyu tsakani kuma watan azumi ya kama. Kashegari kowa ya tashi da azumi, amma Karfa ya ce tun da ya ke ni ba Musulrni ba ne kada im matsa wa kaina in ki cin abinci da rana. Ya ce a ma kawo mini abinci sau biyu kullum. Amma don in nuna musu na girmama addininsu, ni ma sai na yi rikon baki na kwana uku, daga nan na shiga ci da rana. Aka shirya cewa in watan azumi ya mutu za a tashi zuwa Gambiya, tun da ya ke kaka ta yi, ruwa ya janye a koguna. Ko da ya ke wata da watanni abin da na ke jira ke nan, amma ban gaskata wannan alkawarin tashi ba, don kuwa an dade ana sa rana ana dagawa. Kuma a ganina akwai wani hali na Bakin Mutum wanda ba shi da kyau, shi ne rashin sanin darajar lokaci. A wurinsu bata lokaci ba kome ba ne. Im mutumin Afirka yana wani abu muhimmi wanda lalle ya yi shi yau, shi bai kula ba ko ya yi abin nan ko ya bari sai gobe, ko ma watan gobe, ko na jibi. In dai zai sami hutawa a yanzu, bai kula ya sha wakala in an jima ba.
NA TASHI DAGA KAMALIYA
Ran nan watan Salla ya tsaya, azumi ya kare. Da Karfa da manyan fataken bayi duk suka taru, aka hada shawara za a tashi bayan kwana uku. Na yi murna da jin haka, domin ko da ya ke Karfa ya yi mini riko mai kyau wata da watanni, amma makiyana sun yi yawa. Duk fataken bayin nan babu mai kaunata, kowa sai zagawa ya ke yi yana ce da Karfa abu-kaza-shi-yai-kaza, suna bata ni, suna bata daukacin Turawa duka. A kullum wayewar gari sai Karfa ya ji wani mummunan labari game da ni. Mutum kuwa duk ajizi ne, tara ya ke bai cika goma ba. Ina tsoro tun yana kin yarda da abin da ke zuwa kunnensa har dai ya kare ya yarda wata rana, ya juya mini baya. An ce fa zuciya ba ta da kashi. Amma ko fuska bai taba sake mini ba.
Da ranar tashi ta zo, Karfa da sauran duka, kowa ya fito da bayinsa. Aka cire musu sarka a kafa, aka yi musu kangi da kiri a wuya. Aka rarraba su hudu, ko wadanne kanginsu guda. Bayan kangin nan, ko wane bawa yana dauke da kayan ubangijinsa. Nan da nan ayari ya hadu, mu duka mutum saba'in da uku. Daga cikin talatin da biyar bayi ne, shida maroka ne masu waka. wadannan hayar su aka yi musamman, don wakarsu tana kara karfi a zuciya, yadda za a manta da gajiya. In an zo wani gari kuma, da shiga sun dinga yi wa mutanen garin kirari ke nan, yadda za su ji dadi su ba fataken nan masauki.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada

Instagram: @bukarmada