YIN ADDU'A TSAKANIN SUJJADA GUDA BIYU

YIN ADDUA TSAKANIN SUJADA GUDA BIYU



Yana cikin Sunnar Manzon Allah SAW wanda mafi yawan mutane sun gafala daga aikin da su yin addua tsakanin Sujada guda biyu bayan yin hakan ya tabbata daga Manzon Allah SAW a hadisai masu yawa da Sigogi kala-kala ga kadan daga cikinsu;

*1-FADAR;RABBIGH FIR LEE,RABBIGH FIR LEE*
"رَبِّ اغْفِرْ لِي،رَبِّ اغْفِرْ لِ"

Huzaifata رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ yace;
"Manzon Allah SAW ya kasance yana fada a tsakanin sudajoji guda biyu;
*RABBIGH FIR LEE,RABBIGH FIR LEE*
*رَبِّ اغْفِرْ لِي،رَبِّ اغْفِرْ لِ*.
@صححه الألباني في صحيح ابن ماجه-رقم: (739)

*2-FADAR;RABBEGH FIR LEE, WARHAMNEE, WAJBURNEE, WARZUKNEE, WARFA'NEE*

"رَبِّ اغْفِرْ لِي،وَارْحَمْنِي، وَاجْبُرْنِي،وَارْزُقْنِي، وَارْفَعْنِي"
 
Daga Ibn Abbas رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُا yana cewa;
"Manzon Allah SAW ya kasance yana fadar;
*RABBEGH FIR LEE, WARHAMNEE, WAJBURNEE, WARZUKNEE, WARFA'NEE*
*رَبِّ اغْفِرْ لِي،وَارْحَمْنِي، وَاجْبُرْنِي،وَارْزُقْنِي، وَارْفَعْنِي*
A tsakanin sudajoji guda biyu".
@صححه الألباني في صحيح ابن ماجه -رقم : (740)

*3-FADAR;ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNEE, WAJBURNEE, WAHDINEE, WARZUKNEE*
"اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي، وَاجْبُرْنِي وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي".

Daga Ibn Abbas رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُا yana cewa;
Manzon Allah SAW ya kasance yana fadar;
*ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNEE, WAJBURNEE, WAHDINEE, WARZUKNEE*
*اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي، وَاجْبُرْنِي وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي*
A tsakanin sudajoji guda biyu".
@صححه الألباني في صحيح الترمذي-رقم: (284)

*4-FADAR;ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNEE, WA'AAFINEE, WAHDINEE, WARZUKNEE*
"اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي، وَعَافِنِي,وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي"


Daga Ibn Abbas رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُا yana cewa;
Lallai Annabi SAW ya kasance yana fadar;
*ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNEE, WA'AAFINEE, WAHDINEE, WARZUKNEE*
*اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي، وَعَافِنِي,وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي*
A tsakanin sudajoji guda biyu".
@حسنه الألباني في صحيح أبي داود-رقم : (850)


الإمام النووي رحمه الله تعالى:
Yana cewa;
*"Hadisin Ibn Abbas R.A an ruwaito shi daga Abu Dauda da Tirmizee da waninsu da Isnadi mai kyau,kuma Hakim ya fitar da shi acikin Littafinsa ALMUSTADRIK da Isnadi ingantacce ya kuma ambaci Lafuzzan hadisin mabambanta sai yace daga karshe"abinda yafi shine a hada laffuzan duka baki daya sai a zami kalmomin guda bakwai kamar haka:*
((اللهم اغفر لي وارحمني وعافني واجبرني وارفعني واهدني وارزقني)) 
*ALLAHUMMAGH-FIR LEE, WARHAMNEE, WA'AAFINEE, WAJBURNEE WAHDINEE, WARZUKNEE*
@المجموع(414/3)

Allah ne mafi sani


*Allah bamu ikon aiki da wannan Sunnah, karatun hadisi da aiki da shi,shine zaman lafiyar musulmi*.
Post a Comment (0)