GARGAƊI NA MUSAMMAN

*GARGADI NA MUSAMMAN*
****************************



Assalamu alaikum Jama'a! 
Zauren Fiqhu ya Lura da cewa akwai wasu Sakonnin Barkwanci (Wato JOKES) masu mutukar Hatsari da suke yawo a Social Networks. 
Mutane suna ta turawa a cikin groups suna ganin kamar wani abin gwaninta ne, in mutum bai kiyaye ba xai kai mutum Ga halaka.

Ire iren wadannan JOKES din suna kunshe da Barkwanci ga Allah ko Annabawansa da Manzanninsa (Allaihimus salam) Ko kuma Littafin Allah (Alqur'ani) ko hadisan Manzon Allah (S.A.W). 

*GA MISALIN IRIN SU NAN*
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
TURKASHI! Wani yaro👳 ne ya dawo daga Islamiya🏡, sai babansa👨 ya tambayeshi 'me aka koya maku yau? Sai yaron yace: 'sunayen annabawa' sai baban yace: 'to karanta inji'. Yaro ya fara... Annabi Tukur, Annabi Sanusi, Annabi Dan'asabe, Annabi Shehu... sai baban ya shara wa yaron mari! Yaro yace:' baba me nayi? Sai baban yace: 'kana ta kiran sunayen annabawa baka cewa Sallallahu alaihi wasallam ba!....
wai a cikin su waye jahili???
*****************************

*GA MISALI NA BIYU* :
👇👇👇👇👇👇👇
A Fulani man went to hajj,sitting in front of d hotel in d afternoon,he saw👀 a beautiful arabian lady👰 passing through,seeing her extrim beauty,d Fulani man said
"HODIJAM"kaga wadanda ALLAH yayi da hannun shi mukam duk 'yan kwangila sukayimu"
👆👆👆👆👆👆👆👆👆👆👆👆👆

Hakika Kalmar kafirci ta tabbata ga duk wanda ya dauki Annabawan Allah a matsayin ababen wasansa..

Kalli nan yadda wani ya tsaya ya bata lokacinsa yayi wasa da ayar Qurani da sunan barkwanci
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
 
Wani mutum ne ya yi sabuwar amarya, Bayan kwana biyu sai su ka gamu da abokan shi, su ka tambayeshi "Bala ya amarya?", sai ya ce "kai ai ni ana cewa mata tara suke basu cika goma ba amma ni tawa matar ta cika goma cif, dan matata ita muslimatin, muminatin, kanitatin, sadikatin, sa'imatin kai har zuwa karshe." Sai suka ce" kai Bala ka yi sa'a. Allah ya bada zaman lafiya."
Bayan yan watanni kadan sai su ka hadu da abokan na shi, sai suka ce "Bala ya muslimatin?". Sai yace "ai yanzu ta zama muguwatin, munafukatin, kazamiyatin, makiratin, shegiyatin, azzalumatin."kuma saura kiris tazama bazawaratin.....😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😊🙂😊😂😂😂😂😂

Kuma idan an dubi Labarin ma, za'a ga cewar bai faru ba bisa hakikarsa. 
Kawai dai Wasu 'Yan iska ne suka zauna suka kirkiro. Kuma gashi Manzon Allah (S.A.W) ya fada a cikin Sahihin hadisi cewa:

🔥🔥 *"RIJIYAR A ZABA (WAILUN) TA TABBATA GA WANDA YA QIRKIRI WANI LABARI DOMIN YA SANYA MUTANE DARIYA*. 

🔥🔥 *RIJIYAR A ZABA TA TABBATA GARESHI, SANNAN RIJIYAR A ZABA TA TABBATA GARESHI"*


Mu a wajen mu duk wanda yake Qirkira/forwarding irin wadannan abubuwan akwai alamar cewa bai damu da lamarin addininsa ba. 

Duk wanda ya Muzantar da sunan Annabawa (as) to kai-tsaye kamar ya chutar da Manzon Allah ne (S.A.W). 
Kuma kalmar kafirci ta tabbata a kansa. 

Don Allah jama'a ku taimaka ma Zauren Fiqhu wajen isar da wannan gargadin zuwa ga sauran al'ummar Musulmai.
Post a Comment (0)