UKU-BALA'I 22

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA BIYU.
Sosai da sosai zuciyar Mariya ta taɓu akan abin da Hafsi tayi mata na kulla sharri ba abin da ke kara sanya ta cikin bakin ciki in ta tuna kamar yarda ta tsinka ta a gaban Huzaif wanda sam ba ta so haka ba inda ta san abin da Hafsi za tayi mata kenan da bata tsaya ta saurare ta ba balle ta saka mata CIWON RAI.
Haka ta je makaranta har ta gama zaman ta ba tare da ta fahimci abin da aka koyar da su ba da wannan yanayi aka ta so su ta yo gida gabanta na tsananta bugu ba ta san ya Umma zata karbe ta ba, ba ta san da wata irin fuska zata kalle ta ba in abin da Hafsi tayi mata ya tabbata tabbas zata shiga yanayi mai taba zuciya sosai da sosai tana tsoron fushin Umma gareta sosai take tsoron abin da zai je ya dawo ta sani wannan halin da Hafsi ta jona mata yana cikin abubuwan da Umma ta tsana tsana kuwa mai tsanani domin a kullu yau min in tana yi mata magana akan abin da ta tsana dauke-dauke na sahun farko musamman akan abin da ba naka ba kuma ba tare da sanin mai shi ka dauka ba.
Sosai zuciyarta tayi rauni wasu hawaye masu zafi da taba zuciya da ruhi ta ji suna sauka saman fuskarta sosai take jin zafin su a fatar fuskarta tana jin wani raÉ—aÉ—i mai ciwo na bin ko wani sashi na jikinta.
Hannayenta ta saka duk biyun ta na shafe fuskarta ba abin da take ai yana wa a zuciyarta sai.
'Yaa Hayyu Yaa kayyum'.
Fatan ta Allah yasa kar wannan lamarin ya zama gaske domin ita kadai ta san tsananin da za ta shiga ta sani Umma Za tayi fushi da ita fushi mai tsanani ita kuwa ba abin da ta tsana a duniyar rayuwarta kamar Umma tayi fushi da ita sosai hakan ke jefa cikin tashin hankali da rashin natsuwa sosai take jin zuciyar da ruhinta na shiga yanayi na matukar ciwo da zafi gami da raÉ—adi.
Nisawa tayi akaro na ba adadi kafun ta sanya haɓar hijabin ta ta goge fuskarta sai da ta natsu sosai da sosai bayan ta kirayi sunayen Allah a zuciyar hakan ya rage mata faduwar gaba.
Da Sallama dauke a bakin ta ta shiga cikin gidan wani wawan faduwar gaba taji ya ziyarce ta zaune ta hango su sun kafa da'ira kamar ko yaushe yarda kasan ƙawaye haka suke daukar junansu sam! Goggo Marka bata rike girman ta ba ta tauna lafazi kafun ta furta a gaban Hafsi bata kunyar ta saki baki tayi ta ratata zance ko wani iri ne ya dace ko bai dace ba ita ba ruwanta.
Kasa tayi da kanta tana mai jan numfashi gabanta na cigaba da bugawa fata take yi Allah yasa har ta shige daki ba tare da sun tsinka mata ba domin ta sani in har su kayi magana to ba mai dauke da alheri bane mugun abu za su fadi akan ta ita kuwa ciwon da zuciyarta take yi a yanzu ya isheta ba sai sun dauko wani sun kara mata ba.
"Hehehehe an dai ji kunya wallahi an fita da sunan zuwa makaranta ashe halin bera akayi shiyasa ake ta É“arin jiki a je a turmushe kudin sai gashi da yake Allah ba azzalumin bayin sa ba ne a gaban saurayi ko nace abokin sheke aya asiri ya tonu".
Sautin muryar Goggo Marka ta doki kunnuwar Mariya da mugayen kalaman da take furtawa wata irin juwa taji ana yi da ita a filin duniyar rayuwarta ji tayi komai na kwance mata komai take ji ya na fadowa kanta da kayan tashin hankali wani bugu taji zuciyarta tayi kamar zata faso kirji ta fito wani makaƙi mai ɗaci gami da ɓauri taji suna yawatawa cikin makoshinta zuwa saman harshenta.
Cak! ta tsaya waje guda tana faman jan numfashi don ji take numfashin na kokarin ficewa gabadaya daga gangar jikinta yake yi a hankali ta fara taka kafafuwanta da take ji suna lauyewa kamar roba suna kokarin watsar da ita.
"wai mu za a nuna wa son addini da tsoron Allah bayan ko an fita ba can wajan neman ilmin ake yi ba sa dai yawon ta zubar".
muryar Goggo Marka ta sake fadin haka kafun Hafsi ita ma ta caɓe.
"rungume da juna fa na tadda su cikin mota yana faman laguda ta ita kuwa sai faman yashe mssa baki take yi".
'A'uzubillahi minal shaiÉ—anir rajim'
Zuciyar Mariya ta shiga ambata tashin hankalin da take ciki ta ji yana daÉ—uwa komai taji yana juya mata kanta da gangar jikin ta sai majajjawa suke yi da ita cikin wannan yanayi ta ja jiki kanta rike a hannayenta wanda take jin sa kamar zai tarwatse saboda tsabar daukar zafi da taji yayi.
Shigar ta dakin ke da wuya ta zube tsakar dakin wani kuka ne mai É—aci a zuciya taji ya kufce mata sai dai ba hawaye kukan zuciya ne kawai wanda ke kokarin yayyaga mata ko wani fili da zuciyarta da kirjinta HAWAYEN ZUCIYA da take jin suna zuba kamar za su kashe mata zuciya da ruhi.
Girgiza kai kawai take faman yi jin lamarin take kamar ba gaske ba jin komai take kamar a duniyar mafarkinta jin komai take yi kamar duk kuncin duniya akanta a sauke mata a duk sassan jikinta wani fili taji a zuciyarta yana kamawa da wuta ya na babbakewa lokaci guda.
Lokaci mai girma ta shafe cikin wannan yanayin kafun zuciyarta ta sarara mata dalilin ambaton sunan Allah da take faman yi cikin wani irin yanayi mai girma da tashin hankali a cikin sa sosai idanuwanta suka sauya kala kamar wacce akayi wa hayaki da barkono mai tsananin zafi.
A hankali ta dago kanta tana yawatawa da idanuwanta cikin dakin gabanta na tsananta faduwa sake ware idanu tayi ganin ba Umma a cikin dakin da sauri ta zabura ta mike tana kara buÉ—e idanuwanta sosai kafun ta furta
'Yaa Rabbi'.
Laɓɓanta na rawa cikin yanayi na firgata ganin Umma bata cikin dakin hakan ba karamin fadar mata da gaba yayi ba da sauri ta yo waje tana yawatawa da idanuwanta tsakar gidan ba ta ga kowa ba da sauri tayi hanyar bandakin su mai dauke da langa-langa ta shiga kwalawa Umma kira amma ina babu ita babu dalilinta hakan ya sanyata sauri karawasa cikin bandakin ba kowa a ciki da sauri ta yo waje tana duban su Hafsi so take yi ta tambaye su amma tana tsoro ta san dole sun fadi kalma mara dadi ko da kuwa za su bata amsar in da Ummanta tayi ita dai ta san Ummanta ba ma'abociya fita ba ce domin za ta iya tunawa tun da suƙa dawo daga asibiti tsayin wannan lokaci Umma ko kofar gida ba ta leka ba dole hankalin ta ya tashi tana tsoron Abin da zai je ya dawo.
Zuciyarta taji tana sanar da ita kawai ta tambayesu kar ta tsorata da abin da za su ce da ita wanda zai bata mata rai domin ko mai su kayi mata baya yake da ace bata ga Umma ba da wannan shawarar tayi amfani ta dago rinannun idanuwanta ta na saukewa akan su kafun ta shiga motsa laɓɓanta gabanta na wani iri bugu mai girma gareta.
"Uhmm...Goggo don Allah Umma ta ina ta je...?".
Muryarta da rawa a ciki duk kalmar da za ta fadi a dandatse take ajje ta.
Duban shekeke sukayi mata su duka kafun Hafsi ta saki shewa suna tafawa tare da Goggo Marka.
"mu kika ba ajjiyar ta da za ki zo kina tambayar mu ki fita mana ai gari da yawa maye baya cin kan sa itama ta fice yawon ta kamar yarda ke ma ki fic...".
"Hafsi!!!".
Mariya ta buÉ—e muryarta sosai ta ambaci sunan da wani irin bacin rai mai girma dubanta take cikin yanayi na gargaÉ—i da karki sake tafka irin wannan kuskuren sosai bacin rai ya wadatu a cikin muryarta hannu ta daga tana nuna Hafsi wacce muryar Mariya ita ce ta sanya ta tsaida da maganar take yi domin sosai taji faduwar gaba ganin yanayin da Mariya ta nuna.
"Hafsi ya kamata ki san irin maganganun da za ki dinga fadi a kan Umma ta komai za kiyi ko wani irin cin kashi zaki yi ya kamata ki sauke a kaina ba wai sai kin sako Umma ta ba".
Ta karashe da gargaÉ—i mai girma muryarta.
Tana gama fadin haka tayi hanyar waje cikin yanayi da zafin zuciya da raÉ—aÉ—i a kasan ruhi.
Duk kan su sakin baki sukayi suna duban juna kafun Goggo tayi kwaɓa tana girgiza kai gami da cizon yatsa.
"ji tsinanniya mai kalar muciya da zani aiko zata ci dangin uwarta bari ta dawo ita da uwar ta ta mai shegen kalan dangin tsiya da shisshigi gami da kwala kai a faranti in ban da haka uban meye hadinta da gidan kultum daga 'yarta ta haihuwa shine ta kwashi jiki zuwa barka za su zo su tadda ni sai sun ga ne shayi ruwa ne ba komai ba ".
*******
"Alkawari nayi maka Alhaji Abdulwahaab don haka ka saka zuciyarka cikin ruwan sanyi kamar kayi amarya ta mutu A DAREN FARKO".
Areefa ta karashe tana mai kai glass cup da ke zaune a tsakar hannunta mai dauke da tataccen lemon kankana da ya sha kayan hadi sai tashin kamshi yake yi da rangwamin sanyi idanuwanta take juyawa akan Alhaji Abdulwahaab dake zaune yana dubanta da wani irin yanayi mai girma kafun ya saki wani shu'umin murmushi yana gyaÉ—a kai bayan ya kurbi lemon da ke hannunsa.
"Ba ki da dama Areefa. Na sani za ki iya yin koma me nene don ganin cin ma burin ki dama nawa amma kuma ya kamata ki sani Dr.Erena ba saukin kamuwa yake a hannu ba ya kama ta ki san wannan karki yi saurin sakin jiki dashi domin ba karamin NAMIJIN DUNIYA bane da kike ganin sa nan ba ko wacce mace ba ne take samun abin da take so game dashi ya san hannunsa sosai da sosai don haka sai kin yi shiri sosai kafun ki aikata komai karki ga lokaci guda yana rawar jiki akan ki kiyi zaton tarkon ki ya kama miki giwa to wallahi a,a ni nasan halin sa ni zan fada miki waye Dr.Erena ni zan fada miki irin shu'umancin sa".
Murmushi a fuskarta take kallon sa dashi sosai take raina maganar ta sa a ranta har yanzu ta lura bai san wacece Areefa ba bai san salon hannnun na taba zata ba shi mamaki za ta nuna masa sabon jini da tsohon jini akwai bambanci a tsakanin su ba kadan ba za ta nuna masa zamanin Dr.Erena gaf! yake da shuÉ—ewa ko ma tace ya shuÉ—e yanzu kuwa zamanin ta ne ita ce dashi dole kuma tayi amfani da damar ta sannan kuma ta nuna wa Dr.Erena har da shi Alhaji Abdulwahaab din wacece mace za ta nuna masa zamanin da Dr.Erena yayi rayuwarsa bai samu mata irinta ba a duniyar rayuwar tasa dole duk su biyun ta ba su mamaki za su san wacece Areefa.
"Ban san da me zan sanar da kai wacece ni ba amma dai zan barka da lokaci shine zai mana Alkalanci a tsakanin ni da kai kawai kai dai ka zuba ido kayi kallon wannan GAME din da za a buga".
Ta karashe tana kara sakin wani shu'umin murmushi wanda daka kalle shi zaka san akwai tarko mai girma da aka É—ana cikin sa kafun a sake shi.
GyaÉ—a kai yake yi yana yawatawa idanuwansa a nata ba tare da fargaban komai ba sosai da sosai ya hango tsantsar rashin tsoro ko SHAKKA cikin idanuwanta sosai da sosai ya hango gaskiyar kalaman da suke fitowa daga bakinta amma duk da hakan bai gasgata ba domin shi ya san Dr.Erena kuma ya san wanene shi a cikin wannan harkar dole Areefa tayi taka tsantsan domin wannan wasan da take ganin shan ruwa ya fishi wahala to tabbas zai iya juyewa a ko wacce dakika ba tare da ta fargaba ya zame mata katon aiki mafi girma da wahala a filin rayuwarta.
"Ba wai ina raina yanayin ki ba ne a,a ko daya ina dai so na sanar dake wanene Dr.Erena...".
"Ya isa haka!".
Areefa tayi saurin tare shi cikin kakkausar muryar kafun ta mike kan kafafunta ta fara taku a hankali tana mai gyaÉ—a kan ta juyowa tayi a hankali ta dube shi bayan ta tsaya cak! da takun da take yi.
"Me yasa zakayi mani haka mai yasa ba zaka barni na karanci wanene Dr.Erena AKARAN KAINA ba mai yasa kake son ka cusawa zuciyata shakka ko wani fargaba akan sa bana zaton wannan zuzutawa da kambawa da kake yi masa zai samu muhalli a zuciya ta ba na tunanin yarda zuciyarka ke shakka a kan sa nima ta wa za tayi haka zuciya ta da taka suna da bambanci sosai da sosai don haka ka kula".
Ajje Cup din da ke hannun ta tayi kan table din dake gaban su ta sanya hannu ta dauki jakar ta da mukullin motarta bayan ta watsa masa wani kallo na gargaÉ—i ta fara taka kafafuwanta domin fita daga cikin Office din ranta a jagule domin kuwa sosai taji raini a maganar Alhaji Abdulwahaab sosai ta hango ya raina ta ya raina yanayin ta amma ba komi zata ba shi mamaki wanda zai jima yana taba masa zuciya da ruhi.
"Areefa!".
Ya fadi yana mikewa kan kafafuwansa a hankali ya fara takawa domin isa wajanta tsaye take rike da Handle din kofar tana faman jujjuyashi.
"Ban san mai yasa kika fiye daukar zafi akan abin da bai taka kara ya karya ba, Ban san wacce irin zuciya gareshi ki wacce take saurin daukar abu da girma ko da kuwa bai kai a dauke shi din ba".
A hankali ta juyo tana sauke idanuwanta cikin nashi kafun taja numfashi tana gyara zaman glass din da ta daura a fuskarta a wannan lokaci mai taken 'No respect' wanda yayi matukar karawa fuskar ta ta kwarjini da kyau sosai.
"A rayuwa na tsani a raina kwazo na ko ya ya ne shiyasa nake so mutum ya rike duk wasu kalaman sa akai na har ya ga in da zan tsaya da kwazon nawa sai ya bashi Mark daidai dashi".
Yanayin da take ajje kalamanta da dakewa a ciki ya sanya shi kara gasgata ta akan kwazon nata da take kambawa amma kuma ba wai fadi a baki ba a,a gani a aika ce shine sahihin aiki inji kare yace 'mu gani a kasa' ana biki a gidan su.
Shirun da taji yayi ne ba tare da ya ce komai ba ya sanya ta nisawa domin har yanzu ta lura akwai kokwanto a zuciyarsa murmushi tayi kafun ta juya tana murÉ—a Handle din tana fadin.
"Uhmmm...kar fa ka saka zuciyarka cikin tunanin lamari na kawai ajje shi gefe ka yi kallo kawai kamar yarda na fadi maka a baya".
Tana gama fadin haka ta sake sakar masa murmushi tana ficewa daga Office din da hanzari.
Sosai yake murmushi shima yana kallon yanayin Areefa da yanayin da take kokarin ya yarda da maganarta zai iya yarda sai sai wani sashi na zuciyarsa yana tuno masa da Dr.Erena yana hango wanene shi a duniyar filin rayuwarsa da irin gamzuwa da yake yi da mutane yana zubda su sosai yake samun nasara kafun a samu kan sa wanda ya tabbatar wannan a jinin sa yake.
Juyawa yayi ya koma tsakar Office din yana safah da marwa hannayensa harÉ—e a bayan sa.
*****
April 2000.
Sosai garin ya haÉ—e da wani irin haÉ—ari mai matukar razanar wa wanda a ko wani lokaci zai iya zubda ruwa mai karfi gaske gami da iska.
Dr.Erena tsaye bakin kofar dakin wani hotel dake tsakanin Abuja da Suleja kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da akwai abin da ke damun sa a ransa sosai da sosai bi sa yanayin da fuskarsa ta nuna na tsananin bacin rai.
"Mr. Ekele na lura har yanzu ba ka san wanene ni ba a fadin duniyar nan har kake tunanin yaudarata ka hada baki da wasu wajan cuta ta".
Wani murmushi ya ajje a fuskarsa yana kai hannunsa zuwa haɓarsa dake cike da suma kamar wanda yayi shekara ashirin bai bi ta kan ta ba.
Mr.Ekele da ke tsaye sai faman rarraba idanuwansa yake yi a tsakanin na Dr.Erena ya shiga sharce gumin da ke tsatsafo masa a ko ina na kofar gashin dake jikin sa na fuskarsa yake saukewa duk da iskar ake yi a wannan lokacin bakin sa na rawa cikin gurbatacciyar hausar sa ya shiga magana.
"aleji ke yi hakuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba na rantse miki".
Wani wawan kallo Dr.Erena ya watsa masa kafun ya dungule hannu kamar zai sakar masa naushi a fuska hakan da Mr.Ekele ya gani ya sanya shi ja da baya yana kiran.
'Jesus'.
Bakin sa na É“ari jikin sa sai karkarwa yake yi kamar wanda aka jonawa wayar wuta.
"Get out now!".
Muryar Dr.Erena ta karaÉ—e wajan da amo mai zurfi da bacin rai a cikinsa.
wata irin zabura yayi har yana kokarin haduwa da bango da sauri ya juya duk da hakan bai hanashi haÉ—e hannayensa waje daya yana bashi hakuri ba cikin tsananin tashin hankali.
Fitar Mr. Ekele ke da wuya Dr.Erena ya juya cikin dakin sa da sauri fuskarsa kunshe da bakin ciki da bacin rai mai tsanani ga kuma wani murmushi da ya dauko yake ajje a fuskar tashi gefen gadon ya zauna yana mai janyo na'urar sadarwa ta waccan zamanin talfon a hankali ya ja abin sanya wa a kunne ya na mai kai dayan hannun nasa zuwa madannan jikin talfon din dakikun kadan a ka daga cikin yanayi na umarni da nuna isa akan wanda ake waya dashi ya fara magana.
"Yanzu nan nake so ku isa titin da zai shigar da ku Abuja Mr.Ekele nan akan hanya ina so cikin mintina goma ya bar filin duniyar nan bana so ko gawarsa a gani balle a shaida shi da cewa ya bar duniyar nan".
Yana gama fadin haka kamar da minti daya ya sauke wayar yana faman sakin wani murmushi mai razanar da wanda ya gani kafun ya saki wata mahaukaciyar dariya yana mai bajewa gabadaya kan gadon.
Gudu yake yi cikin motarsa zuciyarsa sai faman tsalle-tsalle take da tashin hankali mai girma a wannan lokacin kuma a ka saki wani ruwa mai karfi da iska ga tsawa da ake ta kwaÉ—awa gabadaya Mr.Ekele ya gama tafiya cikin duniyar tashin hankali jikin sa faman karkawa yake yi ga wani gumi dake karyo masa duk da feshin ruwan da dake shigowa ta cikin glass din motar da bai rufe duka ba.
Zuciyarta ba abin da take zaryar dauko masa sai a rangamar su da Dr.Erena ya sani sosai zai shiga cikin matsala tun da har ya san da hannunsa cikin wannan yaudarar da aka shirya yi masa duk da dai shi akaran kan sa ba a son ran sa wannan lamarin ya afku ba takura masa akayi ba yarda ya iya ga shi yanzu ya shiga hali wanda Allah kadai ne zai iya fiddo shi daga hannun wannan mutumin mara imani da tausayin a zuciyarsa ya sani sai wani ikon Allah zai bar shi ya cigaba da rayuwa a duniyar nan ya sani koma ya cigaba da rayuwa to lokaci kalilan ne zai yi ko da kuwa be bar duniyar ba to tabbas zai shiga halin ƙaƙani kayi...
Wani iri bugu yaji an yiwa bayan motarsa wanda sanadiyyar haka sai da ta tuntsiya ta shiga katantanwa a tsakiyar titi ga ruwa da ake ta mamakawa dakiku masu yawa ta dauka tana katantanwa kafun ta tsaya waje guda bayan ta dawo daidai gabadaya glass din jikin motar su yi kwatsa-kwatsa ita kanta motar duk ta gama molewa Mr.Ekele da ya gama rikicewa gabadaya kansa da fuskarsa jini ne sosai gabansa sai bugawa yake yi da sauri sauri a hankali ya fara kokarin tayar da motar don ya gama tabbatar wa kansa ba wanda zai yi masa wannan aikin sai Dr.Erena tuni ya tabbatar wa kan sa ba zai bar shi da numfashi a doron duniyar nan ba key ya shiga juya a mazauninsa cikin iko na Allah motar ta dau wuta ganin ta tashi yayi mata birki gami da fizgarta kamar daga sama yana yin gaba yaji ya doku da katon abu wanda ya sanya motar sake wuntsulawa baya can bayar ma karo ya sake yi da wani abu mai girman gaske kafun motar tayi sama ta dawo kasa lokaci guda.
Izuwa wannan lokaci ya gama fita daga hayyacin sa ba abin da yake ambata sai 'jesus' ya ce ce shi daga wannan halin da yake ciki na tashin hankali.
A hankali yaji a na bugun motar tasa kamar daga sama lokaci guda ya ji an balle murfin wani irin haske ya ga an dalle masa idanuwa dashi wanda hakan ya karasa rufe masa ganin nasa da jini ya wanzu a fuskar sa gabansa ne ya cigaba da faduwa yana ji ya na gani aka fizgo shi waje aka watsar tsakiyar titi kamar wani kayan wanki sosai ya bugu a bayansa wanda hakan ya sanya shi sakin kara mai sauti bai kai ga dire karar ta sa ba yaji an kwaɗa masa wani abu mai girma a tsakar kai wanda hakan ya kara sanya shi bajewa a tsakiyar titi yana mai sakin numfashi wahalalle wata tsawa kayi mai dan karan haske hakan ya baiwa Mr.Ekele damar ganin mutanan dake tsaye akansa gabza gabza har su biyar ko wanne rike da mugun makami a hannunsa hakan ya kara tsinkar masa da gaba ya sadakar shi tashi ta kare a filin duniyar nan a hankali ya mai da kansa ya langwaɓar jira kawai yake yi yaji saukar wani makamin wanda zai tafi masa da rai daga gangar jikinsa.
"Kai dan uban baban ka shine don ka raina wa oga sense shine zakayi masa eya ne ko to yau zaka bar duniyar nan dan kundun uba jikan oduduwa mai katon ciki".
muryar dake wannan zantukar kadai in ka saurara zaka gane tsantsar rashin imani da tausayi daga ji kuma zaka gane ma'aboci zuke-zuke ne zauna gari banza da ake amfani da su wajan cutar da jama'a da ba su ji ba su gani ba.
"Bobby kawai yi masa eya ne kamar yarda ya yi wa Oga shi ya yaji inda dadi".
Wata muryar ce ta daban ta sake fadin haka.
A wahale Mr.Ekele ya motsa yana mai sakin numfashi mai tsananin ciwo.
"ki taimake ni kin ji karki kashe ni zan baki duk abin da kike so Allah...".
Wani bugun bazata yaji ya saukar masa a baki wanda ya sanya shi zubewa a kasa yana kiran jesus ya cece shi za su kashe shi.
Wata irin shaka ya ji anyi wa wuyansa kafun lokaci guda a durkusar dashi a dage masa kai yana ji yana gani aka daura masa wata irin sharɓebiyar wuka wanda walwalin ta ke haske duhun daren da suke ciki kafun yayi wani yinkuri tuni an sauke kan sa a kasa yabi titi yana ta tintsirawa yana tsartuwar jini gangar jikin kuwa nan suka yi cilli da ita kafun daga bisa suka dauke ta sukayi cikin motar shi da ita suka banka masa wuta lokaci daya kamar an kunna wutar auduga haka ta kama ranga ranga.
A hankali suka shiga motocin su fuskar su na bayyanar da tsantsar murna da farincikin samun damar cika wannan aikin domin sun tabbata da ba su samu wannar sa'ar ba Allah kadai ya san abin da Dr.Erena zai musu domin sun lura sosai Mr.Ekele ya bata masa rai wanda ya kasa boyewa har sai da ya fiddo a muryarsa suka fahimta kuma yayi musu gargaÉ—in kar su sake a samu akasi akan aikin nan sannan ga kudin da ya saka musu masu auki wanda tun da suke yi masa aiki bai taba basu kudi haka ba.
*****
"Yaa Allah! Dr.Erena kasan me ke faruwa kuwa yanzun nan muna kan hanyarmu ta dawo wa daga Abuja mu kayi kaci É“us da wani abun tashin hankali Mutumin ka Mr.Ekele an kashe shi an kona gawarsa har da motarsa sai dai kuma kansa da aka yanke kafun a ko ne shi shine yasa muka gane shi ne".
Numfashi mai karfi yaja kafun ya saki Murmushi mai cike da mugunta har sai da Alhaji Abdulwahaab yaji sautin.
"Ni na sanya aka kashe shi?".
"What! kai fa kace akan mi?".
"wannan ba damuwar ka bace abin da kake bukata na fadi maka don haka ka rabu dani kawai a wuce wajan domin ni har na manta da wani mai irin wannan sunan a filin duniyar nan".
"Yaa Salam! Me ya sa kayi haka Dr.Karami haka sam bai dace ba Mr.Ekele komai yayi maka bai dace ace ka sanya anyi masa wannan mugun aikin b...".
"Ya kamata ka kiyaye lafazun ka Alhaji Abdulwahaab na rantse da Allah ko kai ne kayi mani abin da Waccen mataccen yayi mani sai na sanya a kau da min da kai a filin duniyar nan wallahi don haka ka kiyaye lafazinka".
"Dr.Erena ni ka ke wa ikirari haka Allah ya baka hakuri ban san lamarin zai taba maka zuciya har haka ba".
"Da dai yafi haka wallahi don haka mu yi wani batun na daban in kana dashi in kuma babu mu sauke wayar".
Murmushi Alhaji Abdulwahaab ya saki mai zafin gaske kafun ya nisa.
"Ni ba ni da wani abin cewa dama akan waccan maganar ce kuma kace ba ka so komai ya wuce".
Bai jira cewarsa ba ya sauke wayar yana mai mamakin Dr.Erena da irin rayuwar da yake yi wa kansa tanaji ko da yake bai kamata ya zauna tunanin sa har haka ba tun da shi ma akwai tasu a tsakaninsu....
 Nisawa Alhaji Abdulwahaab ya yi sosai lokaci guda gumi ya karyo masa duk da sanyin A-c dake busawa cikin Office din tausayin Areefa yake yi akan yarda lokaci guda ta daukar wa kanta wannan aikin mai cike da hatsari da tarin kalubale shi kansa tsoron Dr.Erena yake yi kuma yana tsoron ranar da zai san yana bibiyarsa ya san tabbas shima wani abu zai faru dashi sai dai zai wa kansa Alkawarin ajje duk wani fargaba da tsoro akan Dr.Erena ya fuskance shi ya marawa Areefa baya domin ganin sun cin ma abin da suke bukata akan sa sosai yake jin zafi da raÉ—aÉ—i a zuciyarsa duk lokacin da ya tuno da kunci da bakin cikin da Dr.Erena ya cusa masa a zuciya dama filin duniyar rayuwarsa gabadaya.
*KAMALA MINNA*😘😘
Post a Comment (0)