ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na É—aya)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, É—aukacin masana sun haÉ—u akan cewa babu rubutun AaBaCaDa a kasar hausa, rubutun hausa da larabci (Ajami) kaÉ—ai aka sani.
Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki ya faÉ—a mana cewa yaji kaka-da-kakanni cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka kawo musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa a rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani É—an uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faÉ—i masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naÉ—e sakon ka turawa É—anuwan naka ta hanyar fatake. Shima É—an uwan idan ya samu sakon, haka zaije ga malami wanda ya iya karatun larabci ya karanta masa sakon gami da fassarawa.
Sai Alhaji Muhammad Koki yace:- sai a wajajen karni na sha shidda zuwa na sha bakwai wani Sarki a Zaria ya kirkiro da dabarar rubuta zantukan hausa da haruffan larabci domin saukakewa da kuma bunkasa harshen na hausa.
Watakila kafin wancan lokacin, malumman bogi sunyi sharafi masu fassara sako gwargwadon abinda suka ga mutum yanaso, ko kuma muce karancin fahimtar wasu kalmomi na larabci sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile harkar sadarwa a kasar hausa, amma samar da ajami sai ya kawo sauyi a harkar.
John Edward Philips ya rubuta a littafin 'Hausa in the Twentieth century' cewa: Fara Rubuta É—ai-É—aikun kalmomin hausa da haruffan larabci ya samo asali ne tun lokacin da aka fara rubuta littafi da larabci a yankin. Tund a cewar sa Littattafan da aka rubuta na kunshe da sunayen Hausawa kamar misalin Muhammad Rumfa, sarkin kano dayayi mulki a karni na goma sha biyar.
Amma dai, littafi mafi daÉ—ewa da aka samu wanda aka rubuta da Ajami shine littafin 'Riwayar Annabi Musa' da akace wani bakano mai suna Abdullahi Suka ya rubuta tun a wajajen karni na goma sha bakwai.
Daga nan kuma sai wakokin da aka samu Malaman nan na katsina sun rubuta, watau Dan Marina da Dan Masani, waÉ—anda suma ake hasashen anyi rubutun a zamani É—aya da wancan na Abdullahi Suka, ko kuma wasu shekaru kaÉ—an baya da nashi. Daga nan ne kuma littattafai suka rinka samuwa da hausar Ajami, ta inda ake kara bunkasa rubutut-tukan da abubuwan da abaya babu su tun usuli, tun daga karni na sha takwas har zuwa na ashirin.
Marubuci John Edward Philips yayi hasashen cewa hausar boko ta fara ne a lokacin da turawan mulkin mallaka suka iso kasar hausa. A cewar sa Sa'ar da Fredrick Lugard ya zama shugaban 'Royal Niger Company' a ranar É—aya ga watan janairun 1900, kaÉ—an daga sojojinsa ke jin yaren Ingilishi, tunda an samu cewa ana fassarawa sojojin Jawabin da Sarauniyar Ingila Victoria ta aiko a karanta musu da yaren Hausa dana Nupe ne.
Tun alokacin, ance Lugard ya fahimci nisan da yaren hausa yayi a zukatan kabilu dake zaune a arewacin Nigeria. Tunda an samu cewa zaka riski mutum yana magana da harshen kabilar sa, yana kuma magana da harshen hausa. Har ma takai jallin da idan hurÉ—a ta haÉ—a wasu mutane masu mabam-bantan kabila da harshe, sai kaga sun ajiye harshen su sunyi amfani da hausa wajen sadarwa.
Ga abinda aka taba jiyo Lugard yana cewa dangane da wannan batu:-
Na gamsu matuka wajen samar da daidaito a É—ibar sojoji ba kawai tsakanin kabilu ba, sai dai tsakanin mabiya addinin (Annabi) Muhammad da kuma sauran mutane marasa addini. Ina matukar girmama addinin (Annabi) Muhammadu, don haka bana É—aukar rashin sanya mabiya addinin na (Annabi) Muhammadu a harkar soji a matsayin siyasa.. A yanzu mun fahimci cewar Kabilu marasa addini irinsu Gwari, Kedar da sauransu duk suna iya magana da harshen hausa, don haka zanfi so nasanyasu a aikin da zarar babban wurin atisayen mu ya Kammala..
Amma dai, duk da kasancewar Lugard yafi son É—aukar sojoji daga kabilun da bana Hausa ba, ko kuma ace yafi son É—aukar mutane marasa addini sama da mabiya Addinin musulunci, amma sam-sam baya koyar da sojin sa harshen su na Ingilishi.
Wannan kuma wani wayo ne da masu dabarar yaki suka nakalta. Domin shi yare ai kamar sirri ne, idan har baka jin yaren da ake yarawa, ba zaka iya fahimtar sirrin da ake tattaunawa ba. Wayon anan kuwa shine, su turawa da sojojin su suna jin harshen hausa, harshen da mafi yawan waÉ—anda suke yak'a ke fuskanta, amma kuma sunki bada wata kafa dasu waÉ—anda ake yaka zasu koyi turanci balle har su san wani abu daga sirrikan da turawa ke yaÉ—awa a tsakanin su.
Da wannan Lugard ya nunawa 'yan uwansa turawa muhimmancin kowannensu yakoyi harshen hausa. Ance ma shine asalin wanda ya kirkiro da jarabawar auna fahimtar hausa ga ma'aikatansa turawa kwatankwacin wadda akace Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya kirkiro ga ma'aikatan gwamnati a zamaninsa. Sai dai turawa da yawa sunga baiken Lugard, sai sukayi turjiya kuma akan wannan bukata.
Daga cikin futattun su akwai Kyaftin C. W Moloney, wanda akace ya nuna kyamar sa a fili ga yaren hausa tunda acewar sa Larabawa masu yaÉ—a addinin Islama ne suka kafa shi, ai kuwa shine wanda akace ya haÉ—u da hatsarin rashin koyon hausa a Fadar sarkin zariya.
Yadda abin ya auku shine, ance Kyaftin Moloney na gabatar da Jawabi ga jama'ar Zazzau ne a fadar sarkin Zariya a ranar uku ga watan oktoba na shekarar 1902 (tun kafin turawa su gangaro Kano da yaki) shikuma mai tafinta yana fassarawa ga jama'a. Sai rashin fahimta ta dabaibaye tafinta, inda ya rinka sauya zantukan da Kyaftin Moloney ke karantawa da wasu zantukan na daban gwargwadon fahimtarsa. ( Watakila saboda tsauraran kalmomin dake cikin jawabin ko kuma saboda karancin ilimin fassara ga tafintan) A ciki ne yake nunawa jama'ar zazzau cewa Matayensu mallakin turawa ne, kuma turawa na matukar bukatar su, duk wanda yaki amincewa da hakan kuwa zai haÉ—u da fushin turawa.. Haba, kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney akayi yana mirgin-mirgin a kasa, wani zakakuri ya sare shi saboda bacin ran abinda yaji... Nan take kuwa sai faÉ—a ya kaure...