ABIN MAMAKI


ABIN MAMAKI
1. LOKACIN DA JAMI'AN LAFIYA SUKA CE A DENA
GAISAWA SABODA KIYAYE LAFIYA, DUK MUN
YADDA MUN DENA, AMMA LOKACIN DA
MUSULUNCI YA HANA GAISAWA DA MATAR DA BA
MUHARRAMAKAR KA BA, IDAN KA KI GAISAWA SAI
ACE BAKA WAYE BA.
2. LOKACIN DA JAMIAN LAFIYA SUKA CE A DINKA
RUFE HANCI DA BAKI, DON KIWAN LAFIYA MUN
YARDA, AMMA LOKACIN DA MUSULUNCI YACE
MACE TA RUFE FUSKARTA DA NIKABI, SAI AKA CE
RASHIN WAYEWA.
3, LOKACIN DA JAMI'AN LAFIYA SUKA CE MU
RAGE CUDANYA DA MUTANE SAI MUKA YARDA,
AMMA LOKACIN DA MUSULUNCI YA HANA
GAURAYA TSAKANIN JINSI SAI AKA CE WANNAN
RASHIN WAYEWA NE.
5. LOKACIN DA MUSULUNCI YACE IDAN ANA CUTA
A GURI KADA A SHIGA, WASU BASU YARDA BA SAI
YANZU DA JAMI'AN LAFIYA SUKA FADA.
6. MUSULUNCI YACE IDAN KA FARKA DAGA BARCI
KA WANKE HANNU SAU UKU, DOMIN BAKA SAN A
WANE HALI HANNUN KA YA KWANA BA. SAI
YANZU AKA GANO HAKA.
7. LOKACIN DA MUKA YI TA KIRA A GYARA
ASIBITOCIN KASA WATARAN FITA WAJE ZAI
GAGARA SAI YANZU AKE TA YIN NA GAGGAWA,
8. LOKACIN DA MUKA CE A GYARA MAKARANTUN
GIDA NA GWABNATI SUYI DAIDAI DA NA WAJE AKA
KI, YANZU MAFI YAWAN WADANDA SUKA SHIGO
DA CIWAN NAN KASAR NAN, DAGA WAJE SUKA
KAWO SHI,
ALLAH KA YIWA NIGERIA ALBARKA.
KADA KA JARRRABEMU DA ABINDA YAFI KARFIN
MU.
RUBUTAWA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA
Post a Comment (0)