ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 02

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na biyu)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Faruwar wannan lamari yasa Gwamna Lugga ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da yake turawa gami da labarta musu abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shine har yake faɗa musu cewa ba lalle ne ace tafintan Kyaftin Moloney da gayya yayi wannan kasassaɓar ba, amma watakila hakan ta faru ne saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney yayi dangane da yaren hausa tayadda har ya kasa tantance tsakanin abinda yake karantawa da abinda tafintan sa yake faɗa.
Don haka a karshe Lugga ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari anan gaba shine turawan mulki 'yan uwansa su koyi hausa.
(D.J.M Muffet, concerning Brave Captain, London 1964.)
Ai kuwa hakan akayi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami'inta ya fara koyon harshen hausa, an buga sanarwar fara yiwa jami'an mulkin mallaka jarabawar auna fahimtar harshen hausa a jaridar Northern Gazette ta ranar 30 ga watan satumbar shekarar 1902.
Sai dai, abu ne mai matukar wuya a gane wanda yafara rubuta hausa da haruffan romawa (Rubutun Boko) kasancewar bauta ta sanya hausawa sun shiga kasashen larabawa lokaci mai tsawo daya gabata, daga can kuma an tsallaka da wasu izuwa turai da sauran sassan duniya masu nisan gaske duk da zimmar yin bauta.
Kowa yasan anyi zamunna na cinikin bayi a baya, sannan shaharar masautar Borno ba karamar aba bace. Itace akace sarakunan ta sun shahara, har ma akace a wajajen karni na goma sha É—aya suka fara hurÉ—a da larabawa, sannan kuma idan yakinsu ya motsa, mamaya suke kawowa dukkanin makwabtan kasashe, ciki kuwa harda kasar hausa. Tana iya kasancewa wani daga turawa ko girkawa ya taba jarraba amsar labaru daga wani bahaushe gami da rubutashi da romanci (boko) amma abin bai fito ga duniya har mun riske shi ba, amma dai mafi dadewar abinda aka samu shine wanda Marubuci Ibrahim Yaro Yahaya (Allah yajikansa da rahama) ya kawo a shafi na 74 na littafinsa mai suna 'Hausa A Rubuce..' inda yakecewa "Watakila za'ayi mamaki aji cewa a kasar Denmark ta turai aka fara samun an rubuta kalmomin hausa acikin rubutun boko tun a karni na goma shatakwas. Yadda abin yafaru shine a cikin shekarar 1772 sarkin Denmark ya tura wakilansa izuwa Arabiya don gudanar da bincike na kimiyya. Acikin wakilan harda wani mai suna B.G Neibuhr, wanda shine kadai ya tsira kuma har ya dawo gida kasarsa. To a wannan shekarar sai wani balaraben Tunis yaje Denmark ziyara, sunan sa Abdurrahman, a tare dashi akwai wani bawansa Bahaushe. Sai sarkin Denmark yasa aka kira Niebuhr domin ya zama tafinta tsakanin sa da balaraben nan kasancewar shi Niebuhr ya koyi larabci a tafiyar da yayi izuwa Arabia. To a wannan gamin ne har abota ta-kullu tsakanin Niebuhr da Abdurrahman, har kuma Niebuhr yayi sha'awar koyon Barbarci da Hausa daga wannan Bawa. Anan ya dukufa yana koyo, ana fada masa kalmomi yana rubutawa.
Ga wasu kalmomi da aka samu Niebuhr ya rubuta a hausar boko kamar yadda yaji daga bakin wannan bawa bahaushe.
Dudsji. Dutse
Ghaui. Gari
Dsjenari. Zinari
Ghurasa. Gurasa
Crua. Ruwa
Sirki. Sarki
Schensali. Shaidani
Berni. Birni
Baya da wannan kuma, sai rubuce-rubucen da J.F Schon yayi da hausa a wuraren 1856 lokacin daya roki Dr. Barth ya bashi aron Yaransa Dorugu da Abega don su taimaka masa wajen yin rubututtukan hausa.
A wancan lokacin ne Dorugu ya rinka faÉ—ar labarun hausa, shikuma yana rubutawa, har aka samu cewa J. F Schon din ya rubuta litttattafai misalin Magana Hausa, Letafin Musa na fari, Labari Nagari, Dictionary of the Hausa da sauransu.
Amma dai idan muka dawo maganar asalin soma rubuta hausa da boko irin wadda har yau muke amfani da ita, to zaifi kyau mu koma kan maganar mu ta sama cewa turawan mulkin mallaka ne suka assasa tare da tabbatar mana da ita.
Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar mana da hakan a shafi na 55 na littafinsa mai suna 'The Hausa factor In West African History'. Kuma ga kadan daga abinda yace :- Karatu da rubutu ta hanyar boko ya samu ga hausawa ne a farkon karni na 20. Saboda a shekarar 1900AD ne gwamnatin Ingila ta karɓe ragamar mulki daga hannun sarakunan hausawa, amma sai a 1903 sojojin Gwamna Lugga suka cinye Kano da Sakkwato a yaki, sanna suka buɗe makaranta ta farko a sokoto tare da malamai biyu watau Mr. Kurdan da mataimakinsa Malam Ibrahim, amma makarantar bata daɗe ba saboda iyaye sunki sanya 'ya'yansu don gudun kada acusa musu akidar kiristanci.
Tun kafin wannan ma, shi kanshi Lugga sai daya kalli Hausawa da yadda sukayi riko da addini tun a lokacin, sannan yayi amannar cewa bai yiwuwa ace za'a koyar dasu boko kamar yadda ake koyar dashi a kasarsu Ingila.
A wani kaulin kuma, cewa akayi tun sa'ar da Lugga yake yaki a kasar nan ya fara sanyawa ana rubuta hausa ta hanyar amfani da rubutun romawa (boko). Saboda kamar yadda muka faÉ—a tun a baya, Lugga ya fahimci tasiri da bunkasar yaren hausa a wannan yanki na arewa, amma kuma a wurinsa bai yiwuwa ya rubuta hausa da ajami kamar yadda ya samu hausawan lokacin sunayi. Dalilan yin hakan suna da yawa, daga ciki akwai fadin cewa idan za'a rubuta hausa da ajami, sai an koyi yare biyu maimakon É—aya, watau sai an koyi hausa, sannan kuma an koyi larabci. Amma watakila babban dalilin yafi ga kiyayyar su ga larabawa ko kuma ace kiyayyarsu ga musulunci (kamar yadda babban dalilin kin jinin boko daga hausawa shine kiyayyarsu da kiristanci). Wannan abune da ba sai an É“oye ba. Lugga ya faÉ—a cewa baya ganin rashin sanya musulmai a sojinsa a matsayin siyasa, amma a zahiri siyasar ne. Tunda dai kusan É—aukacin Sojojin nasa ba musulmai bane, mutane ne gwarawa da sauran kabilu marasa addini wadanda suke adawa da musulunci, waÉ—anda kuma yawa-yawansu suna da matsala daa musulmai tun a lokacin jihadi, don haka suna zucci-zuccin karya daulolin da musulmai suka kafa domin É—aukar fansa.
A ɗaya ɓangaren kuma, akwai kwatankwacin wannan kiyayyar a zukatan hausawa, kuma tana daga manyan dalilan da yasa hausawa suka kyamaci ilimin boko. Shiyasa sai da aka sha-burtu aka soma sanya yara a makarantun zamani a wancan lokacin, koda yake har izuwa yanzu (kusan shekaru 114 kenan) wasu daga cikin mu hausawa na kallon ilimin boko a matsayin haramtaccen abu kuma gurɓatacce.
Ai a zahirin yakin da turawa sukayi a zamanin mulkin mallaka da 'yan kasa akayi, domin mafi yawan dakarunsu 'yan kasa ne bakaken fata, tunda turawa ba yawa garesu ba a rundunonin, hasali ma wannan yanki namu kamar makabarta ya zamewa turawa saboda yawaitar cututtuka dake musu lahani a yankin.
Shi kuwa rubutun Ajami, turawa da waÉ—anda ba musulmai ba sna É—aukarsa a matsayin rubutu ne na Larabci kuma na musulunci, daman kuwa da tun da jimawa turawa da larabawa ba wata É—asawa suke ta azo agani ba. Idan kuma ba haka ba, to zamu iya cewa baya daga cikin manufar turawa a zuwan su wannan yanki su inganta addinin Islama. Dalili kenan da ba zasu yadda suyi aiki da rubutun ajami ba ballantana har su inganta shi.
Don haka akace babbar sadarwar da sojojin Lugga sukafi fahimta daga gareshi shine rashin sonsa ga musulunci. A zahiri, ban jin an taɓa ruwaito wata kalma ta ɓatanci da Lugga yayiwa Islama, amma a baɗini, ayyukansa nason ganin bayan addinin ne, shiyasa kuma sojojin nasa sukafi kaunar kome za'a rubuta musu, a rubuta musu shi ɗin da yaren hausa, yaren da sukafi sha'awar yarawaa sama da nasu, amma kuma cikin haruffan sabuwar wayewa da kiristocin mulkin mallaka suka kawo, watau romanci.
Bayan anci kano da sokoto da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa akayi masa hasashen É—aliban dake makarantun allo a wannan yanki, inda kintace yanuna cewa akwai misalin makarantun Allo da ake karantar da Addinin musulunci cikin rubutun arabi da ajami misalin dubu 25, sannan É—aliban dake cikin makarantun sun tasamma dubu 250. Wannan tasa Lugga fahimtar Cewa akwai aiki ja agabansa, amma dai ance da taimakonsa aka kafa makarantar mishan a Bidda a cikin shekara ta 1904, inda aka fara koyawa wasu mutane aciki harda tsirarun musulmai rubutun hausar boko, gami da harshen turanci. Ance ana koyar da daliban ne cikin harsunan mu na gida, watau hausa da nufanci. Gwamna Lugga ya sanar da Ingila yunkurin daya fara na juya rubutun ajami izuwa haruffan Rumawa (Boko) kamar yadda aka samu a kundin takardun dayasha turawa izuwa ingila (Annual Report, Northern Nigeria no. 476, 1903, 332-3)
Daga sanda aka fara samun gagarumar Nasara a fannin boko a kasar hausa kuwa shine wajajen shekara ta 1908, sa'ar da Lugga ya tura Dr. Hans Vischer wanda akafi sani da 'É—an Hausa' izuwa kasashen Sudan, Misira (Egypt) da Gwalkwas (Ghana) domin yin nazari akan yadda kasashen ke bayar da ilimi ga mutanensu waÉ—anda akasari musulmai ne, saboda kasancewar hausawa musulmai sunki tura 'ya'yansu a harkar boko. Bayan Dr. Vischer ya dawo gida ne akace ya bude makarantar elementary da ake kira Makarantar É—an Hausa a Nassarawan jihar kano, wadda akace da dalibai 30 ta soma, sai a hankali daliban suka rinka yawaita. Amma dai daga wannan lokacin ne aka samu cewar an fara fassara littattafai na ilimi wadanda aka rubuta su a wasu yarukan duniya izuwa hausa, aka rubuta su kuma da boko, a sannan gwamnati ta mayar da gausa a arewa a matsayin yaren sadarwa, sannan kuma a hankali har hukumar Norla tazo wadda itama ta bada gagarumar gudunmuwa wajen fassara littattafan ilimi izuwa harshen hausa.
Daga littattafan farko da aka soma fassarawa izuwa harshen hausa da rubutun boko akwai misalin :- Koyon Lissafi, Dare Dubu da É—aya, Tarihin Garuruwan Borno, da wasu littattafan da dama.
Post a Comment (0)