KA NEMI SOYAYYAR ALLAAH TA ISHE KA

*KA NEMI SOYAYYAR ALLAH YA ISHEKA !!!*
.
Yazo cikin hadith cewa: Wani mutum yazo wajen Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Ya Rasulullah shiryar dani ga wani aiki da zanyi wanda idan nayi shi ALLAH zai so ni, Mutane ma zasu so ni? Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Ka guji duniya ALLAH zai soka, kuma ka guji abun hannun mutane, mutane zasu soka.” [Ibn majah da wasunsu suka ruwaito shi.]
.
→Kada ka sanya soyayyar mutane itace agabanka, saboda mutane zukatansu na jujjuyawa yau su soka gobe su qika.
.
→Kada ka qwallafawa ranka kwad'ayin abun hannun mutane, domin ba zasu qare ka da komai ba haka kuma baza su rage ka da komai ba face abunda ALLAH Ya rubuta maka.
.
→Ka kau da kai daga kwad'ayin Abun duniya na hannun mutane, ka dogara ga ALLAH su ma ALLAH ne ya basu kuma bai manta da kai ba, ka gode masa acikin duk yanayin da ka tsinci rayuwarka, hakan zaisa ya qara maka ya kuma kaika inda baka yi zato ba.
.
→ka sanya soyayyar ALLAH a gabanka saboda idan ALLAH ya soka zai sanya zukatan mutane su karkata zuwa gareka.
.
→ka nemi Yardar ALLAH, Idan ALLAH Ya yarda da kai ya isheka.
.
Ya ALLAH Ka so mu ka yarda damu (Ameen)

Post a Comment (0)