'YANUWANTAKA A MUSULUNCI

*'YAN UWANTAKA A MUSULUNCI*
______________
Manzon Allah (S.A.W) yace: "Dangantaka da take tsakanin mumini...
kamar gini ne wanda sashe yake karfafa sashe." (Bukhari/Muslim)
An karbo daga 'Dan Umar (R.A) cewa Manzon Allah (S.A.W) yace: "Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya mika shi ga abokin gaba.
Wanda ya tsaya da biyan bukatar dan uwansa, to, kuwa Allah zai tsaya masa (da biyan bukatarsa). Wanda kuwa ya yaye wa Musulmi wani abu da yake damunsa, to, Allah zai yaye masa wata damuwa daga damuwar ranar Alkiyama.
Kuma wanda ya suturta Musulmi, to, Allah zai yi masa sutura ranar Alkiyama." (Bukhari/Muslim)
Manzon Allah (S.A.W) yace: "Misalin muminai a cikin soyayyarsu da jin 'kansu da tausasawarsu a tsakaninsu, kamar misalin jiki ne. Idan gaba daga cikin ta yaji ciwo, sauran jikin sai rashin bacci da zazzabi ya same shi." (Bukhari/Muslim)
Ya Allah muna rokonka ka hada kan dukkan musulmi baki daya.
 ka bamu ikon yin soyayya da tausayin juna saboda Allah.
Allah yasa mudace.

*Zauren Sheikh Ja'afar*
Post a Comment (0)