BINCIKE A LUPUR

BINCIKE A LUPUR, TSOFFIN TSAUNIKAN DA MAGUZAWA SUKA TAƁA KAFA DAULA.
DAGA
SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
Lupur, wani ɗan ƙauye ne dake daura da sabon garin Rano, koda yake ana iya cewa manyan tsaunikan nan masu tarihi ne suka raba ƙauyen da garin na Rano, watau duwatsun Ƙurƙubu, Ƙurgum, Damusu, da Mairamu.
Manyan ababen ƙayatarwa a ƙauyen sune duwatsun Jidal da kuma Tsiriri dake can ƙurya dashi, dukkaninsu kuwa suna da tsohon tarihi.
Don haka sai na yanke shawarar ziyartar gani da ido zuwa garin.
Kafin zuwana, na saurari labaru kala-kala game da waɗancan tsaunika. Daga ciki akwai masu cewa Fadar sarakunan farko na maguzawa na cikin tsaunikan Lupur ne, akwai koguna masu duhu da kuma ababen tsoratarwa aciki.
Ibrahim Haladu, shine matashin daya amince yayi mini rakiya zuwa cikin surƙuƙin waɗannan duwatsu. Haka kuma mahaifinsa Mallam Haladu tsoho ne, masanin tarihin wannan yanki, wanda har Maimartaba Sarkin Rano kan aiko mutane gareshi domin jin abinda ya sani game da tarihin tsohuwar Rano.
Bayan mun gusa nesa da gari, sai gamu daf da sashen ganuwa ginin dutse, wajen ya zama gomaki amma dai ana iya ganin ɓurɓushin duwatsu da akayi alamomi dasu tun abaya, muna tsallakata kuwa sai yace mini yanzu mun shigo asalin garin daya fara kafuwa kafin komawa Rano.
Wurin kewaye yake da manyan tsaunikan can dana faɗa a sama, watau Ƙurƙubu, Mairamu, Ƙurgum, Damusu, da wasunsu, amma Jidal da Tsiriri na can ciki.
A saman waɗannan duwatsun na hango birrai farare suna ta kaikawo, shigen jikinsu yaso yayi kama dana kyanwa. Ɗan rakiya ta yace mini sun fito shan ɗorawa ne, kuma sun saba ganinsu suna fitowa gungu-gungu. Wani sa'ilin ma har ƙasa suke saukowa takalar faɗa.
Ibrahim ya nuna mini gonakinsu a ƙasan waɗannan duwatsu, kuma ya sanar mini cewa birrai na zuwa suyi musu ɓarna lokaci zuwa lokaci.
Da muka yi gaba daga nan, akwai wani sashen gini da aka nuna mini na duwatsu. Wajen ance tsohuwar fada ce, mai ɗauke da zauruka da manyan ɗakuna, har ma da inda ake zama don yin fadanci.
Ban samu labarin sunayen sarakunan da sukayi mulki acikin wannan fada ba, amma dai ance mini wannan waje ya girmewa tsohon garin Rano dake can tsallaken duwatsun, inda shima ake iya ganin sashen gini na ƙasa da sarakunan zamanin suka rayu a ciki.
Sai dai kuma ana tsammanin sai da wayewa ta zowa waɗannan maguzawa sannan suka sauko daga kan tsaunika tare da soma yin bukkoki a dandamarin ƙasa. A zamanin ance Sarki kaɗai ake ginawa gida da duwatsu.
Babu kuma takamaimen bayani game da hanyar zaɓen shugaba a wancan tsohon zamani, amma dai kamar yadda aka sani, bata wuce gado ko kuma fin ƙarfi.
Daga can ƙurya kuma akwai sashen ƙofofin shiga gari masu suna ƙofar Ƙahu da Ƙofar Bezo, ance mutanen da suka zauna a wurin sun samar dasu ne domin sanya ƙarin tsaro kafin a riski inda suke.
Baya da nan kuma sai wani babban dandali, inda aka asanar mini cewa ainihin wajen matattara ce, kasancewar akwai mutane zazzaune a kusan kafatanin tsaunikan, don haka suna samun lokacin da suke haɗuwa don yin bautar gumakansu misalin gunki Darmo, har ma da yin wasanni.
Daga wasannanin da akace suna yi baya da kaɗe-kaɗe da raye raye irin na maguzanci, akwai wasan Ƙwado da ayanzu akafi sanin mata dashi. Don haka har yanzu ana iya ganin wani dutse da suka ƙwaƙule, suka yi masa ramuka kamar tandarun waina, wanda suke wasan ƙwado a kanshi.
Ance wani sarkin Rano ya taɓa zuwa ya umarci a haƙe shi a mayar dashi inda masarautarsa take, amma duk tsawon haƙan da akayi sai dai aga dutsen na ƙara zurfi, daga ƙarshe sai aka haƙura ba tare da angano cibiyarsa ba.
A gefe ɗaya kuma akwai tsaunikan Tsiriri da Jidal waɗanda ana iya cewa sune sukayiwa wannan farfajiya ƙawanya.
Shi tsaunin Tsiriri anan ne kogo yake, watau inda Zamna Kogo ya samo asali, inda akace anan ainihin maguzawan suka rinƙa zama tare da iyalansu.
Na samu hawa saman tsaunin tare da shiga kogon, na ganshi da faɗi, da kuma duwatsun zama barbaje a ciki, harda wani faffaɗa da akace anan shugabansu yake. Sai kuma wasu lunguna da suke sadarwa izuwa gareshi..
Akwai kuma wata rijiya mai suna Kurfafiya a saman tsaunin wadda ruwa mai haske yake tsatsowa daga tsakankanin duwatsu, wadda kuma akace tarihi ya nuna cewar daga gareta mazauna duwatsun ke samun ruwansha, haka kuma bata taɓa ƙafewa ba.
Ance maguzawan da suka rayu a wajen basa sanya tufafi, sai dai su rufe tsiraicinsu da ganyaye.
Haka kuma farautar namun daji ce babbar sana'ar su, gasu karfafa, don haka suna yawan fita yaƙi ga maƙwabtan birane, suma kuma ana yawan kawo yaƙi izuwa garesu.
Post a Comment (0)