CECE-KUCE DANGANE DA TSADAR AURE

*GASKIYAR LAMARI 👌*

*Dangane da ce-ce ku ce a kan tsadar aure.*

A dubi wannan a matsayin fahimtana, a yi min uzurin kura-kuran da za a iya samu a maganata, amma kuma a duba lamarin da idon fahimta.
.

Kalamai sun yawaita, rubuce-rubuce suna ta zagaye kafofin sadarwa a kan cewa *aure* ya yi tsada, wanda ake jingina laifin zuwa ga iyaye tare da yi masu tuhumar cewa suna tsawwalawa a harkar aure a dai-dai lokacin da zina kuma ta yi arha.
.

'Yan uwa! Ni a nawa fahimtar, aure yana nan kamar yadda aka san shi, dukkan wani tsanani da sauqin da za a fuskanta a cikinsa ya danganta ne da gidan da ka je neman auren da kuma manufar ka ta neman auren.

Abin mamaki, za ka samu matashi yana hawa babur ko yana rike wayar hannu ta fiye da dubu ďari biyu (₦200,000) amma ka ji yana complaining cewa aure ya yi tsada, to wai shin ina tsakanin yake?

Ba komai ya shigo da tsanani cikin neman aure ba illa kokarinmu na yin koyi da qazamai kafirai (yahudu da nasara) a yayin shagulgulan aure. Za ka samu mutum zai yi aure, amma sai an qirqiri waďansu shashanci an gayyato shaiďan ya ďebe albarkar, tun daga kan pre-wedding programs da ake shiryawa, irinsu pre-wedding pics, Fulani day, Qauyawa day, Arabian day, mother's night, etc day, abin dai kawai gashinan, wai mu dole sai mun yi koyi da kafirai sannan duniya za ta gane cewa lallai fa wannan biki ya shahara, adadin kuďaďen da ake 6arnatarwa a irin waďannan programs sun ishi mai hankali ya toshe wata kafar da su.

Addini ya yi mana sauki a harkar aure, amma mu kuma mun tsananta shi wa kanmu, burinka shi ne uban amarya shi zai yi maku komai, tun daga kan gadon kwanciya, katifa, cushion,.... Kai har cokalin cin abinci, duk an bar wa iyayen amarya aiki alhali a qa'ida miji shi ne zai tanadi waďannan abubuwa, to a yadda rayuwa ta yi tsada, mai zai hana uban yarinya ba zai buqaci sadaki mai tsoka ba don rage wannan ďawainiya? To amma da duk za a dawo kan tsarin addini, kun ga sai duka 6angare biyun su samu salama.

'Yan uwa babu wahala cikin neman aure ga dukkan wanda ya wanke zuciyarsa da tsoron Allah kuma ya nufaci auren da kyakkyawar manufa, haqiqa Allah Ya yi alqawarin arziki da samar da mafita ga dukkan wanda ya ji tsoronSa.


Mu guje wa qago sababbin al'amura a aure domin addini ne, sannan mu kama sana'a kuma mu nemi taimakon Allah.


Ya Allah Ka qara sauqaqa aure tsakanin musulmi sannan ka toshe hanyoyin 6arna a cikinmu. Allah Ya sa mu dace.
.


*Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
Post a Comment (0)