SHARHIN FIM ƊIN DEVDAS
Devdas fim ɗin soyayya ne da aka shirya shi a cikin Shekarar 2002, Sanjay Leela Bhansali ne ya bada umurnin shirin kuma wannan shi ne karo na uku da aka yi irin fim ɗin sai dai shi kaɗai ne mai kala, Kasancewar sauran duk an yi su ne gabannin bayyanar Fina-Finai masu kala.
An tsara wannan shiri ne a yanayi irin na shekarun 1900, kuma labarin ya biyo rayuwar Jarumi Shah Rukh Khan a matsayin Devdas, wani Lauya mai kuɗi wanda ya dawo daga birnin Landan domin ya auri masoyiyar sa na yarinta watau Paro.
Hana wannan aure da ahalin sa suka yi ne ya jawo faɗawarsa cikin Shaye-shaye wanda ya kaishe ga ɓalɓalcewa tare da macewa a Ƙarshe.
MA'AIKATAN SHIRIN
Bada Umarni: Sanjay Leela Bhansali
Ɗaukar Nauyi: Bharat Shah & Red Chillies Entertainment
Tsara Labari: Prakash Kapadia
Labari Daga: Sarat Chandra Chattopadhyay
Sautin Shiri: Ismail Darbar & Monty Sharma
Jami'in Shiri: Binod Pradhan
Tacewa: Bela Sehgal
Kamfanonin da suka Shirya:
Mega Bollywood Pvt.Ltd
Red Chillies Entertainment
Kamfanin Da Suka Yaɗa:
Mega Bollywood Pvt.LTD
SLB Films
Red Chillies Entertainment
Ranar Fita: 12 July 2002
Tsawon Shiri: Minti 185
Ƙasa: India 🇮🇳
Harshe: Hindi
Kasafi: ₹500 million
Asusun Kasuwanci: est. ₹1.02 billion
Alokacin da shirin Devdas ya fita, babu wani fim da aka kashe masa Kuɗi kamar sa, domin an kashe masa zunzurutun Kuɗi kimanin dala miliyan $10.3. Shirin ya samu kasuwa sosai a harkar kasuwancin gida da waje har sai da ya zama shirin da yafi kowanne kawo kuɗi a Ƙasar Indiya a wancan lokacin.
Jarumi Shah Rukh Khan ya siye haƙƙin mallakar wannan shiri a ƙarƙashin Kamfanin sa mai suna Red Chillies Entertainment.
Devdas ya samu karɓuwa a wajen masu sharhin cikin gida da na waje, domin masu sharhi da dama sun yarda cewa shirin yana ɗaya daga cikin hamshaƙan Shirye-shiryen da ba'a taɓa yin kamar su ba a duniya. Shirin ya samu shiga gasar BAFTA Award a gurbin Best Foreign Language Film kuma shi ne shirin da India 🇮🇳 ta miƙa domin shiga Gasar Academy Award for Best Foreign Language Film. Bugu da ƙari wannan Fim shi ne na 74 daga cikin Fina Finai guda ɗari wanda Mujallar Empire Magazine ta ware da cewa su ne gawurtattun Fina Finai Ɗari da babu kamar su a duniya a cikin Shekarar 2010. Haka nan kuma Jaridar TIME magazine ta bayyana shirin Devdas a matsayin fitaccen shirin da babu kamar sa a duk faɗin duniya a cikin shekarar 2002. Bada Jimawan nan ba kuma har wa yau, shirin ya samu damar shiga jerin Fina-Finai goma da babu kamar su a dukkan zamunna. An haska wannan shiri a 2002 Cannes Film Festival, Kuma an nuna shi bikin International Film Festival of India a cikin shekarun 2002 da 2014 a sashin "Devdas Section" da "Celebrating Dance in Indian cinema"
Shirin Devdas ya samu damar lashe kyautar Gwarzon fim na Filmfare Award, ya samu damar lashe lambobin yabo na National Award guda biyar, sannan ya ƙara gaba da wasu lambobin yabo na Filmfare Awards guda goma.
LABARIN SHIRIN
A farko-farkon Shekarun 1900, Kaushalya ta samu labarin cewa ɗanta Devdas yana nan dawowa daga Landan bayan ya shafe tsawon shekaru 10 yana karatun Lauyanci. Cikin Murna Kaushalya ta bayyanawa maƙwabciyar ta Sumitra wannan labari, ita ma kuma tayi murna Matuƙa.
To ita Sumitra tana da wata 'ya mai suna Parvati "Paro" Chakraborty wacce tun suna yara ita da Devdas sun shaƙu Matuƙa gaya. Lokacin da aka tura Devdas birnin Landan don yayi karatu, sai Paro ta kunna wata aci-balbal domin tunawa da dawowar Devdas, kuma wutar bata taɓa mutuwa ba.
Yayinda Devdas ya dawo, sai shaƙuwar su da Paro bisa abota ta yarinta ta koma soyayya. Kowa ya aminta da cewa Devdas da Paro za su auri juna saboda suna son juna kuma sun dace, amma sai wata sirikar Devdas wacce ta kasance Uwar gulma ce mai suna Kumud ta tunawa Kaushalya wato mahaifiyar Devdas cewa ai Paro 'yar Zuri'ar' yan rawa ce ta Fannin mahaifiyarta, don haka bata dace da ahalin Mukherjee ba. Ana cikin haka ne kuma sai ita Sumitra watau mahaifiyar Paro ta nuna Muradin ta na son ganin ta aurar da ɗiyar ta ga Devdas, ita kuwa Kaushalya sai ta ƙi amincewa kuma ta kunyatata a cikin jama'a ta hanyar cewa su 'yan ƙaramin gida ne watau matalauta. Cikin rashin kwanciyar hankali da samun nutsuwa Sumitra ta haɗa auren Paro da wani mutum mai kuɗin gaske wanda har ma yafi ahalin su Devdas kuɗi. Shi wannan mutumin sunan sa Thakur Bhuvan Chaudhry, shekarun sa arba'in kuma yana da manyan 'ya'ya guda uku.
Yayinda mahaifin Devdas shi ma ya ƙi amincewa da ya auri Paro, sai Devdas ya bar gidan su ya koma gidan Magajiya ya tare. Amma kafin ya tafi sai da ya barwa Paro wasiƙa inda yayi mata ƙaryar cewa dama can babu wata soyayya a tsakanin su. A can gidan Magajiyar ne ya haɗu da wata mace mai kirki da ake kira da Chandramukhi wacce ba'a jima ba ta kamu da Son shi. Bayan wani ɗan lokaci sai Devdas ya fahimci cewa yayi Kuskuren barin Paro, inda ya dawo gareta a ranar da ake ɗaura mata aure. Ya nemi su gudu su je wani wajen su yi aure amma sai ta ƙi kuma ta tuna masa da irin yadda yayi watsi da ita cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Anan dai Devdas yayi mata alƙawarin cewa zai zo ya ganta kafin mutuwa ta riske shi.
Can ita kuma Paro sai ta gano cewa mijinta fa ya aureta ne kawai domin ta zama uwa ga 'ya'yan sa ba don wani abu ba, domin shi bayan matarsa wacce ta mutu baya son wata mace a duniya. Haka ta ci gaba da gudanar da duk wani haƙƙi da ya rataya a wuyanta a cikin gidan.
Shi kuwa Devdas, ganin cewa ya rasa Paro, sai ya koma gidan magajiyar nan wajen Chandramukhi da zama dindindin inda ya zama hamshaƙin mashayi. Ana cikin haka ne sai mahaifin Devdas ya kwanta cutar ajali inda ya buƙaci ganin ɗan nasa, amma har baban ya mutu bai je ba, daga baya ya je wajen jana'iza inda a nan ma yayi abin kunya domin ya je cikin maye kuma ya suma a can.
A hankali dai cuta ta kama Devdas har ya kai matakin da idan ya sake ya ƙara shan ko da ɗigon barasa ne to zai iya mutuwa. Hakan yasa ya koma gidan su domin ya samu lafiya amma sai ya iske wannan Uwar gulmar ta sace makullan ajiyar gidan, Yayinda ya tuhume ta sai ta faɗawa mahaifiyarsa cewa ai Devdas ne ya sace makullan. Mahaifiyarsa ta yarda da maganar kumud fiye da tasa don haka ta kori Devdas daga gidan.
Ita kuma Paro sai ta je gidan Magajiyar da Chandramukhi take tana tuhumar tada cewa ai ita ce ta jawo Devdas ya fara shan giya gashi nan yanzu yana gab da mutuwa, amma ba'a daɗe ba sai ta fahimci cewa Chandramukhi tana Matuƙar ƙauna tare da kula da Devdas. Daga nan sai Paro ta roƙi Devdas da ya daina Shaye-shaye hakanan amma yaƙi ji. Sai ma ya sake nanata mata alƙawarin sa na cewa kafin ya mutu zai sake dawowa har ƙofar gidanta a karo na Ƙarshe.
Bayan nan sai Paro ta gayyaci Chandramukhi zuwa bikin Durga Puja wanda zai wakana a cikin gidan mijinta, anan ne ta gabatar da ita ga sirikanta ba tare da ta bayyana musu cewa ga Sana'ar ta ba. Amma surikin mijinta watau Kalibabu, da yake shima tantiri ne kuma yana kai ziyara gidan Magajiyoyi sai ya bayyana musu asalin ko wacece Chandramukhi kuma ya ci mata zarafi a gaban baƙin da suka halarci wajen. Hakan fa bai ishe shi ba kuma sai da ya faɗawa Bhuvan alaƙar da ke tsakanin Paro da Devdas. Wannan dalili ne yasa Bhuvan ya kafawa Paro dokar kada ta sake fita daga cikin gidan. Devdas ya faɗawa Chandramukhi cewa tayi haƙuri kawai ta rabu da shi, daga nan ya yanke Shawarar ya zaga gari ko zai ji ɗan dama-dama. Bayan ya shiga jirgin ƙasa, sai suka gamu da wani tsohon abokin sa da suka yi Kwaleji tare mai suna Chunnibabu wanda ya roƙe shi da ya sha barasa ko kaɗan ce saboda da tunawa da abotar su. Devdas ya san cewa idan ya sha barasar nan abin ba zai mai kyau ba, amma duk da haka ya sha.
Yayinda yake gab da mutuwa, Devdas ya je gidan Paro domin ya cika alƙawarin da ya ɗauka. Bayan ya faɗi a gindin wata bishiya da ke ƙofar gidan, sai Paro ta rugo tun daga cikin gidan da nufin zuwa wajen sa, amma sai mijinta ya bada umurnin a rufe gidan. Devdas ya ga dishi-dishin Paro Yayinda ta rugo zuwa wajen shi amma sai ƙofar gidan ta rufe kafin ta iso inda yake, hakan yasa ta fashe da kuka daga cikin gidan. Devdas ya samu damar furta sunan Paro da ƙyar kafin ruhin sa ya fita daga gangar jikin sa. Yana mutuwa kuwa ita ma wannan aci-balbal da Paro ta kunna ta mutu.
JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA
* Shah Rukh Khan - Devdas Mukherjee
* Madhuri Dixit - Chandramukhi
* Aishwarya Rai - Parvati Chakraborty
* Jackie Shroff Chunni Lal
* Kirron Kher - Sumitra Chakraborty
* Smita Jaykar - Kaushalya Mukherjee
* Ananya Khare - Kumud Mukherjee
* Vijayendra Ghatge - Bhuvan Chaudhary
* Tiku Talsania - Dharamdas
* Milind Gunaji - Kalibabu
* Neha Pendse - Chaurangi
* Manoj Joshi - Dwijdas
* Ava Mukherjee - yar Devdas
* Sunil Rege - Neelkanth
* Vijay Crishna - Sir Narayan Mukherjee
* Jaya Bhattacharya - Manorama
* Disha Vakani - Sakhi
* Dina Pathak - mahaifiyar Bhuvan
* Amardeep Jha - mahaifiyar Kalibabu
* Radhika Singh - Yashomati
* Apara Mehta - Badi Aapa
* Muni Jha - Kaka
KUNDIN WAƘOƘIN SHIRIN
Kundin waƙoƙin shirin Devdas ya samu sauti ne daga Ismail Darbar Yayinda rubutawa kuma ya fito daga alƙalamin Nusrat Badr. Mawaƙan da suka rera waƙoƙin shirin sun haɗa da Shreya Ghoshal, Kavita Krishnamurthy, Udit Narayan da kuma Vinod Rathod. Yayin da Monty Sharma shi kuma ya tsara taken shirin.
Wannan shi ne shirin da ya fara kawo mawaƙiya Shreya Ghoshal Bollywood har aka Santa. Ta ja hankalin mahaifiyar Sanjay Leela Bhansali ne yayin da ta ganta a bikin Sa Re Ga Ma tana rera wata waƙar Lata Mangeshkar. Daga nan ne aka bata damar ta rera waƙoƙin da Paro zata hau. Waƙar Farko da Shreya Ghoshal ta fara rerawa a matsayin mawaƙiyar Bollywood ita ce "Bairi Piya" a lokacin tana da shekaru 16 a duniya. Ta rera Waƙoƙi biyar ne a cikin wannan Kundin Waƙoƙi wanda su ne suka jawo mata gagarumar nasara a rayuwar ta, domin ta samu lambobin yabo da dama ciki har da National Film Award for Best Female Playback Singer da waƙar "Bairi Piya"
Rahotanni sun bayyana cewa a ƙalla an siyar da kwafin Kundin waƙoƙin wannan shiri guda miliyan huɗu kuma yana daga Kundaddaki uku da suka fi kowanne kawo kuɗi a shekarar da suka fita.
WAƘOƘIN CIKIN SHIRIN
1. "Silsila Ye Chahat Ka"
2. "Maar Daala"
3. "Bairi Piya"
4. "Kaahe Chhed"
5. "Chalak Chalak"
6. "Hamesha Tumko Chaha"
7. "Woh Chand Jaisi Ladki"
8. "Morey Piya"
9. "Dev's Last Journey" (The Theme)
10. "Dola Re Dola"
LAMBOBIN YABON DA SHIRIN YA SAMU
1. 10 Filmfare Awards
2. 16 IIFA Awards
3. 5 National Awards
4. 5 Star Screen Awards
5. 7 Zee Cine Awards
6. 1 Star Award
7. 1 Asian Film Award
<••••••••••••••••••••••••••••>
Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com