DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 04

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN

Kashi Na ɗaya 02

Fitowa Ta huɗu 04

Daga Haiman Khan Raees

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Barkan Mu da Warhaka.

11. MOHABBATEIN: A Yayinda kake son mutum so na Haƙiƙa, ko mutuwa ba zata iya raba ku ba, domin ko da ɗayan ya mutu zai ci gaba da Wanzuwa a cikin zuciyar ɗayan. Ma'ana dai, daga lokacin da ka faɗa soyayya ta zahiri, to babu kai babu Kaɗaici. Har abada!

12. KABHI KHUSHI KABHIE GHAM: A Rayuwa ba kullum ake kwana a gado ba, wani lokaci ka kan tsinci kanka a cikin farin ciki, wani lokaci kuma akasin haka. Amma ka sani cewa ahalin ka zasu kasance tare da kai a cikin kowane irin yanayi ka tsinci kanka. Idan kuwa soyayya ta ratso, to ka tsaya da kyau ka yanke hukuncin da ya dace, ko da ace ya saɓa musu, kada ka damu komai zai yi daidai. Ahali sun saba haka.

 13. MY NAME IS KHAN:
A duk inda ka tsinci kanka a rayuwa, ka kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana, ka zama mai cika alkawari kuma mai magana ɗaya. Kada ka raina mutum ko yaya yake, kada ka zalunci kowa. Ka taimakawa duk wani mai neman taimako ko da kuwa ba garin ku ɗaya ba, ko da yaren ku ba ɗaya ba kuma ko da Addinin ku ba ɗaya ba. Abu mafi muhimmanci kuma, kada ka ji tsoron bayyana Ra'ayin ka ko a ina ne.

14. HUM TUMHARE HAIN SANAM: Yarda da juna shi ne ginshiƙin kowane irin zama zaka yi da wani. Ba zaku taɓa samun nagartacciyar zamantakewa ba Matuƙar baku yarda da juna ba. Sannan yanke hukunci cikin fushi da ƙiyayya yana iya tarwatsa alaƙar da ke tsakanin masoya kuma yana iya farraƙa su. Lallai ya kamata mutum ya kula da kyau yayin yanke hukunci don kada ya bar baya da Ƙura.

15. MAIN HOON NA: Haƙiƙa so Makaho ne, kuma so mahaukacin abu ne, don haka babu wata damuwa don kayi hauka a kan soyayya. Sannan shi so yana iya faruwa a kowane irin yanayi, a kowane waje, ga kowane mutum ba tare da duba tsari ko cancanta ba. Don haka kada kayi mamaki don kaga Tsofaffi suna soyayya, ko kuma kaga tsohuwa da yaro suna soyayya, dama abin haka yake.

16. VEER-ZAARA: Kada ka ka bari wani abu yayi maka Iyaka da abinda kake so, domin shi so baya bin kowace irin doka face nashi. Babu abinda ya shafe shi da ƙasa, Addini, kalar fata, yare ko kuma ƙabilar Masoyan. Kana iya son duk wanda ya kwanta maka a zuciya ko wanene shi, daga baya komai ya biyo baya, kai dai kawai kayi so na gaskiya.
Haka kuma fim ɗin ya koya mana cewa, ko da ace akwai wani Shamaki a tsakanin Masoyan gaskiya, wannan shamakin bai isa ya hana su jin ɗumin juna a cikin zukatan su ba. Kamar dai yadda Squadron Leader Veer Pratap Singh daga India 🇮🇳 ya kamu da son Zaara Hayat Khan daga Pakistan 🇵🇰.

17. KABHI ALVIDA NAA KEHNA:

Wannan Fim ya sha suka daga mutane da dama kan rashin ɗa'a da halin banza da aka nuna a ciki. Amma hakan bai hana saƙon sa fitowa fili ba. Idan har Zamantakewar auren ku baya yi muku daɗi, kuna iya rabuwa da juna salin Alin. Domin cin Amanar juna a bayan fage ba zai magance muku matsalar ba, aure wani irin zama ne da yake buƙatar abokan zaman su so junan su dagaske, kuma su kula da juna yadda ya kamata.

18. JAB TAK HAI JAAN:
Wannan fim mai suna Jab Tak Hai Jaan ya baiwa mutane da dama damar fahimtar Camfi a zahirin sa da kuma irin yadda yake iya hana masoyan gaskiya kasancewa tare da junan su. Amma in har son na gaskiya ne, ƙaddarar ku zata haɗa ku daga Ƙarshe ko ana ruwa ko ana iska.

19. RAEES: Duk da cewa wannan Fim ya samu mixed reviews a yayin fitowar sa, hakan bai hana saƙon da ke cikin sa fitowa ba. Abu na farko dai da fim ɗin yake koyarwa shi ne kowane ɗa yana buƙatar ya ɗauki maganar mahaifiyar sa da girma Matuƙa. A duk inda ta ce maka bari ka bari inda ta ce maka yi je kayi, zaka ga haske. Sannan a gidan ka fa lallai kana da iko, amma a mafi yawancin lokuta matar ka ita ke da iko akan Ikonka a cikin gidan, don haka wani abun fa dole sai dai kayi haƙuri kuma kayi shiru sannan ka maida shi wasa.
Haka kuma ko wacce irin Harka zaka yi ka zamo mai gaskiya zaka ga ci gaba. Sannan kai tsaye fim ɗin ya tabbatar mana da cewa MAZA MA FA SUNA YIN KUKA, kuma yin wannan kukan bai kai ace za'a binciki mazantakar su ba.

20. FAN: Abu ne sananne cewa kowane Jarumi yana da masoya a duniya, kuma kowane Jarumi yana son Masoyan sa a ko ina cikin faɗin duniya. Amma me? Akwai wani mummunan tunani da yake shiga cikin zukatan wasu masu yiwa wasu jarumai Makauniyar soyayya na cewa, duk da cewa bai san su ba, ai da ya gansu zai gane su kuma zai karɓe su hannu biyu tare da girmama su. Saboda me? Tunanin su a iya kansu kawai ya tsaya. Wannan Fim na Fan yana ɗauke da darussa masu yawa wanda Alhamdulillahi mafi yawancin mutane basu so fim ɗin ba saboda gaskiyar da ya nuna, amma har cikin zuciyar su sun fahimci saƙon. Fan ya nuna mana cewa duk son da za ka yiwa mutum to kada ka zurfafa, kada ka zuba yawan tsammani a tsakanin ka da wanda kake so, kada ka taɓa barin abinda kake da shi don ganin ka samu abinda kake nema har sai ka samu tukun. Sannan, ba dukkan abinda kake gani bane yake haka a baɗini, kada kuma ka taɓa tsammanin cewa kafi kowa domin duk irin matakin da kake tunanin ka kai akwai wanda ya fi ka. Amma babban Darasin wannan shiri shi ne KA DA KA GAZA BADA HAƘURI GA WANDA KA SAƁA WA, KO MAI ƘANƘANTAR SA

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)