SHARHIN FIM ƊIN BUSINESSMAN

SHARHIN FIM DIN BUSINESS MAN

Sunan Fim: BUSINESS MAN

Bada Umarni: Puri Jagannadh 

Daukar Nauyi: R. R. Venkat 

Labari: Puri Jagannadh 

Hada Sauti: S. Thaman 

Tacewa: S. R. Shekar 

Kamfanin Da Ya Shirya: R. R. Movie Makers 

Ranar Fita: 13 Janairu 2012 

Business man Fim Din dabanci ne da aka shirya shi a kasar Indiya cikin harshen Telugu a shekara ta 2012. Puri Jagannadh shi ne ya rubuta kana Kuma ya bada umurnin Fim Din. Wannan Fim ya samu Karbuwa sosai a wajen masu sharhin Fina-Finai da ma 'yan kallo, musamman Masoyan jarumi Mahesh Babu. An fara daukar wannan Fim ne a ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 2011 a Hyderabad, an dauki yankin farko na wannan fim ne a garin hyderabad, Mumbai da kuma Goa, Yayinda aka dauki wata Waka a Bangkok. An kammala shirya wannan fim ne a ranar 10 ga watan Disambar 2011 bayan an dauki kwanaki 74 ana aiki, hakan ya sa fim din ya zama daya daga cikin Fina-Finan Telugu da aka fi saurin kammala daukar su a cikin 'yan kwanaki kalilan 

An Fassara wannan fim zuwa harshen Hausa Da sunan DAN KASUWA, an fassara Fim Din da harshen Tamil da Malayalam da sunansa na asali, an kuma sake maimaita fim din a shekarar 2013 cikin harshen Bengali inda aka sa masa suna BOSS: BORN TO RULE. 

LABARIN FIM DIN 

Fim Din ya fara ne da nuno kwamishinan 'Yan Sandan Mumbai Ajay Bhardwaj Yayinda yake sanarwa da manema labarai tabbacin Kwamushe Ta'addanci da Jagaliyanci a birnin. Hakan kuma ya biyo bayan wani Yunkuri ne da rundunar 'yan Sandan suka yi domin ganin sun kwantar da tarzoma tare da wanzar da zaman lafiya mai dorewa. 

Ana tsaka da hakan ne kuma sai ga wani dan jagaliya daga kudancin kasar India mai suna Vijay Surya ya shigo garin Mumbaai da nufin zama fitaccen dan jagaliyar da babu kamar sa. Bayan ya samu masauki a wani yankin masu karamin karfin Mumbaai da ake kira da Dharavi, sai aka gabatar da shi ga wani dan Siyasa mai suna Laalu. Shi kuwa Laalu a wannan lokaci dama yana cikin tsaka mai wuya, don haka sai Surya ya taimake shi. 

Bayan nan, Surya kuma sai ya dauki wani bangare na 'yan jagaliyar Mumbai da ke karkashin shugabancin Naseer domin su ci gaba da aiki a karkashin sa. Laalu ya zama babban abokin Surya ne, bayan daya daga cikin yaran sa mai suna Shakeel ya sheke shaidar da yake da damar batawa Laalu lissafi dangane da wani aikin Maa Shaa'a da ya aikata. 

Bayan nan Kuma sai Surya ya yiwa talakawan dake zaune a Dharavi Alkawarin zai biya musu dukkanin basussukan da ake binsu ta yadda babu wanda zai kara kwacewa dayan su gidan sa. Fadar hakan ke da wuya sai Surya yasa yaran sa suka je wani banki dake Maharashtra suka farfasa shi, suka kwashe takardun filayen jama'a dake cikin sa sannan suka barnata duk wata ajiya dake Bankin. 

A hankali a hankali sai Surya ya zama shahararren dan jagaliyar da kowa ke shakka a garin Mumbaai, Yayinda talakawan Dharavi Kuma suke matukar nuna masa Kauna da bashi matsayin mai ceton su. Surya yana sane da Manufar Bhardwaj, don haka sai ya nemi kare kansa ta hanyar yin soyayya da 'Yar Bhardwaj din mai suna Chitra, wacce ta kasance kyakkyawa kuma kwararriyar mai Zane. Da fari ya je mata da batun shi dan kasuwa ne mai sha'awar Zane-zane ne, amma daga baya sai suka bige da soyayya. 

Sai dai kuma, a dai-dai Lokacin da Surya ya fahimci cewa son Chitra ya shiga zuciyar sa da gaske ne shi kuma Bhardwaj ya fara jika masa aiki ta hanyar Bayyanawa Chitra asalin ko shi wanene, jin haushin hakan yasa ta tsane shi. A nan take kuma aka kama Suryan. Sai dai ba'a dade ba aka sake shi, domin ya sa yaransa sun sace Chitra kuma sun ki bada ita har sai an sake shi. Surya yayi Alkawarin daina Ta'addanci matukar Bhardwaj zai bashi Chitra ya aura, amma daga Bhardwaj har chitran babu wanda ya amince. 

Wannan Abu da suka yi masa yasa Surya ya sha alwashin cewa zai kafa Kasuwancin da sai girgiza garin Mumbaai kuma 'yan sanda basu da ikon yi masa komai, kuma sai ya auri Chitra. 

Daga nan sai Surya ya kafa wani babban Kamfanin shige-da-fice mai suna Surya Exports & Imports a matsayin basajar aiyukan Jagaliyancin da yake yi. Daga nan kuma sai yayi shirin faɗaɗa aikin ta'addancin sa a kowane sassa na Ƙasar India, inda ya fara da kafa rassan Kamfanin Surya Exports & Imports a ko'ina birni da ƙauye. Sannan kuma sai ya riƙa ɗaukar 'yan jagaliyar kowane yanki a matsayin ma'aikatan sa, kuma ya tirsasawa kowane babban ɗan jagaliya biyan harajin kaso biyu na kowane aiki da yayi a wannan yankin. 

Hakan yasa Surya ya tara maƙudan kuɗaɗe nan da nan inda kafin kace kwabo ya zama biloniya. A yayin ƙaddamar da Bankinsa na kasuwanci ne ya shaida wa Bhardwaj ƙudurin sa na son mulki, tare da haƙiƙancewa kan cewa aikin ta'addaanci ya ragu matuƙa tun daga lokacin da ya fara ɗaukar 'yan jagaliya aiki, kuma ya sake bayyana masa cewa yana da Burin ganin ya kauda aikata ta'addanci a Ƙasar inda baki ɗaya tare kuma da taimakawa masu ƙaramin ƙarfi. 

Surya ya samu nasarar taimakawa Laalu, inda ya zama shugaba bayan ya doke Ghokle wanda Ghanapuleti Jai Dev ya ɗauki nauyin sa. Jai Dev wani hamshaƙin ɗan siyasa ne da yake muradin ganin ya kai matsayin Firaminista ta kowane hali. Ghokle ya bayyanawa Bhardwaj mugun nufin Jai Dev wanda hakan yasa ya sheƙe shi. Bayan nan kuma, sai Surya ya fahimci cewa Jai Dev yana shirin kashe Bhardwaj da Chitra. Hakan ya sa ya hanzarta zuwa gidan su domin ya tseratar da su, duk da cewa ya samu nasarar tseratar da Chitra, a wannan artabu da akayi ne ajalin Bhardwaj ya same shi. Hankalin Chitra yayi matuƙar tashi, amma Surya sai yai ta lallashin ta. 

A sannan ne Surya ya samu damar bata labarinsa, inda ya bayyana mata cewa shi ɗan Amurka ne amma haihuwar India, kuma Jai Dev ne ya cuci iyayen sa sannan ya kashe su tun yana ɗan ƙaramin yaro. Wannan dalili da kuma irin yadda akai ta wulaƙanta shi a gidan marayu ne yasa ya tsane su kuma ya koma yadda yake a yanzu. 

Daga nan, sai Surya ya maida hankalin sa kan babban zaɓen Ƙasar da ke ƙaratowa. A nan ne ya haɗu da jagoran Jam'iyyar adawa wato Guru Govind Patel ta hanyar Laalu, inda suka ƙulla harƙall ya bashi miliyan 350 na kamfe kuma ya sha alwashin sai ya maida shi Firaministan India. Daga nan sai Surya ya dinga kashe kuɗi a dukkan mazaɓun Ƙasar kamar baya so. Wannan dalili ne yasa Jai Dev ya kasa taɓuka komai a harkar siyasar. 

Bayan nan kuma, sai ya bayyanawa duniya irin mugun aikin da Jai Dev yake aikatawa. Jin haushin hakan yasa Jai Dev ya sace Chitra domin ya ɗau fansa a kan Surya. Surya ya tunkari Jai Dev, inda ya yiwa yaransa Lilis har aka yi masa rauni. Daga ƙarshe dai ya kashe Jai Dev kuma ya ceci Chitra,inda ya ƙara bayyana mata buƙatar sa na son kasancewa tare da ita a rayuwar sa. A ƙarshen Fim ɗin dai an nuno Guru Govind Patel ya lashe zaɓen Firaministan India a lokacin da shi kuma Surya yake asibiti Chitra na jinyar sa. 

Jaruman Fim Ɗin Tare Da Matsayin Da Kowanne ya fito a kan sa. 


* Mahesh Babu = Vijay Surya

* Kajal Aggarwal = Chitra

* Prakash Raj = Jai Dev

* Nassar = Ajay Bhardwaj

* Sayaji Shinde = Laalu

* Raza Murad = Guru Govind Patel

* Dharmavarapu Subrmaniyan = Sakataren Laalu

* Rajev Mehta = Arun Ghokle

* Mahesh Balraj = Naseer

* Aakash = ƙaramin Surya


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)