SHARHIN FIM ƊIN STUDENT OF THE YEAR 2

TAƘAITACCEN SHARHIN FIM ƊIN STUDENT OF THE YEAR 2

Daga Haiman Raees

Student of the Year 2 Fim ɗin yaren Hindi ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2019.

Bada Umarni: Punit Malhotra

Ɗaukar Nauyin Shiri: Karan Johar, Hiroo Yash Johar, Apoorva Mehta da kuma Fox Star Studios

Rubuta Labari: Arshad Sayed

Sautin shiri: Salim–Sulaiman

Jami'in Shiri: Ravi K. Chandran

Tacewa: Ritesh Soni

Kamfanin da ya shirya: Dharma Productions da Fox Star Studios

Kamfanin Da yaɗa Shirin: Fox Star Studios

Ranar Fita: 10 May 2019

Tsawon Shirin: Mintuna 145

Ƙasa: India

Harshe: Hindi

Kasafin Kuɗi: ₹80 crore

Box office: ₹12.06 crore[Ranar Farko]

An fara Ɗaukar wannan Fim ne a ranar 9 ga watan Afrilun shekara ta 2018 Dehradun, yayin da aka kammala Ɗaukar shirin a cikin watan Satumbar 2018. Vishal-Shekhar ne suka tsara kiɗoɗin waƙoƙin fim ɗin, yayin da Anvita Dutt Guptan, Kumaar Vayu suka rubuta waƙoƙin Fim ɗin. An fitar da Kundin waƙoƙin fim ɗin ne a ƙarƙashin kamfanin Zee Music Company.

KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN FIM ƊIN

Rohan Sachdev wani gwarzon ɗalibi ne mai aiki tuƙuru da ke karatu a Makarantar a Pishorilal Chamandas College da ke garin Mussoorie, kuma suna tarayya da wata kyakyawar yarinya mai suna Mridula Chawla. Sai dai ƙaddara ta jawo rabuwar su yiyinda Mridula ta canja makaranta zuwa Saint Teresa, wanna makaranta kuwa ta Ƴaƴan masu kuɗi da masu faɗa aji wadda ta ke garin Dehradun

 Rohan ba shi da ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar makarantar balle su kasance tare da Mridula, amma saboda son da yake yi Mata sai ya je ya shiga gurbin waɗanda ake taimakawa ta harkan wasanni watau scholarship har dai ya samu damar shiga wannan makarantar.
Ita kuma Mridula tana shiga makarantar sai ta canja sunan ta izuwa Mia Chawal
Domin ta dace da sauran ƴan makarantar. Ko da ta haɗu da Rohan, da fari ta yi nesa da shi, amma daga baya sai suka koma kamar yadda su ke a da.



Daga nan sai aka gabatar da Rohan wa Manav Singh Randhawa, wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ɗan mai kuɗi kuma ɗalibin da ya cinye Gasar Gwarzon Ɗalibi na Makarantar har sau biyu. Nan da nan sai Rohan da Manav suka zama abokai. Sai dai kuma Rohan ya tsinci kansa a cikin cakwakiya sakamakon ƙiyayyar da ƙanwar Manav watau Shreya Singh Randhawa ta ke nuna masa.

Ana nan watarana sai aka saka Gasar rawa a Makarantar, inda aka haɗa Rohan da Mia a matsayin waɗanda za su kara da Manav da Shreya. Ita dai Mia tana so ne tayi nasara domin ta kankarowa kanta girma da ƙima a makarantar, Yayinda ita kuma Shreya ta ke so ta yi nasara domin ta nunawa gallababbben mahaifinta baiwar rawar da ta ke da ita domin ya bata damar shiga makarantar koyon rawa da ke birnin landan. Manav da Shreya dai su suka lashe wannan gasa sakamakon turguɗewa da Mia ta yi a lokacin gudanar da Gasar. Yayin da Rohan ya je wajen Mia domin ya lallashe ta, sai ya taras da ita a rungume da Manav.
Rohan sai ya sambaɗi Manav, hakan ya jawo aka sllame shi daga makarantar Saint Teresa; Daga nan sai ya koma makarantar sa ta farko wato Pishorilal Chamandas College. Ana cikin hakan ne kuma sai Shreya ta kogin son Rohan.

 Rohan da sauran abokan wasan sa da ke makarantar Pishorilal Chamandas sai suka zage damtse don ganin sun lashe kofin gasar makarantu na kowace shekara da ake yi watau 29th Annual Inter-College Dignity Cup. A Shekarun da suka gabata, makarantar Pishorilal ce ta ke zuwa ta Ƙarshe idan aka yi irin wannan gasa. Amma sakamakon namijin ƙoƙarin Rohan da kuma Jajircewar tawagar ƴan wasan, sai ga shi Pishorilal Chamandas College ta make Saint Teresa, inda ta lashe wannan gasa, yayin da shi kuma Rohan ya lashe kanbun Gwarzon Ɗalibin Shekara Watau Student of the Year.

Jaruman Shirin da kuma matsayin da suka fito a cikin sa.

Tiger Shroff - Rohan Sachdev

Tara Sutaria - Mridula "Mia" Shankar

Ananya Panday - Shreya Randhawa

Aditya Seal - Manav Singh Randhawa

Samir Soni - Principal Gujral

Gul Panag - Coach Kuljeet

Abhishek Bajaj - Abhishek Sharma

Manoj Pahwa - Coach Mahipal

Ayesha Raza - Principal Singh

Rajesh Kumar - Chacha

Manasi Joshi Roy - Chachi

Chetan Pandit - Mr. Randhawa

Samreen Kaur - Mahaifiyar Mia

Manjot Singh - Dimpy

Sahil Anand - Jeet

Daljeet Singh - Abdullah Wahab

Harsh Beniwal - Puggi

Alia Bhatt - (Fitowa ta musamman)
Will Smith - (Fitowa ta musamman)

WAƘOƘIN FIM ƊIN DA MAWAƘAN SU

1. "The Jawaani Song" Anvita Dutt Guptan (original by Anand Bakshi) Vishal Dadlani, Payal Dev, Kishore Kumar

2. "Mumbai Dilli Di Kudiyaan" Vayu Dev Negi, Payal Dev, Vishal Dadlani

3. "The Hook Up Song" Kumaar Neha Kakkar, Shekhar Ravjiani

4. "Fakira" Anvita Dutt Guptan Sanam Puri, Neeti Mohan

5. "Main Bhi Nahin Soya" Anvita Dutt Guptan Arijit Singh

6. "Jat Ludhiyane Da" Anvita Dutt Guptan Vishal Dadlani, Payal Dev



Post a Comment (0)