SHAWARA GA MUSULMI

SHAWARA GA MUSULMI
Sau da yawa musulmi sukan yi mamakin a ina choci-choci suke
samun makudan kudin da suke tafiyar da al'amuran chocinsu har
chochina ke iya mallakar jirgin sama? Wasu kan zargi cewa
manyansu ke bada kudaden ko ma gwamnati ke basu,to bari kuji
sirrin. Dukkan kirista idan yaje choci yana bada wani kudi da suke
kira offerings'. Da wannan suke tara makudan kudade.
Wannan yasa nayi wani nazari inda na gano cewa inda musulmi
zamu dauki wani tsari mai kama da wannan hakika zai taimakawa
masallatanmu ba sai an dinga rokon mutane taimakon masallaci
ba.
Nayi wani dan bincike a kano inda na gano cewa a kano kadai
akan samu musulmi miliyan uku da suke halartar sallar juma'a
duk sati a masallatai daban daban. Sai nayi tambaya cewa 'nawa
ne mafi karancin kudin da duk wani musulmi baligi zai iya
bayarwa duk juma'a ba tare da ya takura ba? Mafi yawancin ansar
dana samu ta tsaya akan naira ashirin (N20). Sai nayi lissafi na ga
cewa idan duka mutum milyan ukun nan da zasu halarci sallah
duk juma'a kowa zai bada naira ashirin da duk sati za a samu
naira miliyan sittin(N60,000,000), a wata za a tara naira milyan
dari biyu da arba'in(N240,000,000). Shin ya kake tunanin irin
taimakon da wannan kudi zasu bayar wajen tafiyar da
masallatanmu? Hakika har nakasassun cikinmu za a iya daukar
nauyinsu da wannan kudade.
Da wannan nake kira ga dukkan musulmi daga yau yayi wa kansa
alkawari cewa duk juma'a idan yaje masallaci don sallar juma'a
zai nemi akwatin 'fisabilillah'na wannan masallacin ya saka mafi
karancin naira ashirin(N20) a matsayin sadaka. Ku tuna irin falalar
da Allah (SWT) yayi alkawari ga masu taimakon addini.
Kuma don Allah duk wanda yaga wannan posting din yayi sharing
ga dukkan group din yake ciki domin samun ladan 'umarni da
kyakyawan aiki.' Allah yasaka mana da alkhairi ya kuma daukaka musulunci da musulmai baki daya amin.
Post a Comment (0)