UKU-BALA'I 31

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA DAYA.

Tsaye tayi ki kam!. tana faman yatsine fuskarta da cizon laɓɓanta sai faman ajiyar numfashi take kamar wacce tayi Gudun ceto rai.
"Ni wallahi gabadaya na gaji".
Ta fadi tana mai jingina da bishiyar dogon yaron dake bakin hanyar da zata fiddo su daga cikin surkuk'in dajin da suke. kallo daya za kayi wa wajan ka tsoro ta sosai musamman in ka kasance mai karyayyiyar zuciya in aka ce ka shigo wajan ko da kudi ne ba zaka shigo ba daji ne sosai mai dauke da surkuk'in ciyayi da dogayen bishiyu kamar su sukayi kansu ga wasu gingima-gingiman duwatsu suma abin dai na tsoro gashi nan ba kajin kukan komai sai na gyare da tsintsaye.
Tsaya tayi da tafiyar da take yi jin abin da Hafsi ta fadi ta juyo kallo daya zakayi mata ka gane itama ba karamin gajiya tayi ba sai faman numfarfashi take yi jin jikinta take kamar wacce akayi wa dukan kawo wuka.
"Ke kam kin fiye tsirfa wallahi ni ban ce na gaji ba sai ke mai jikin kuruciya kai jama'a ke dai kam anyi ranguwa wallahi Hafsi".
Sake turo baki tayi gaba tana kokarin zama gindin bishiyar.
"Haba mana Goggo Marka ki dubi uwar tafiyar da muka dauko fa aiko akan abun hawa muke wallahi sai mun gaji ga kuma fargaba da tsoro ki dubi dajin nan fa ki gani ba kowa bane zai iya shigarsa ko ni dai na shiga a tsakanin rayuwa ko mutuwa wallahi ban ma yi tunanin zan fito ba don tuni na fara dankaro salati a bakina...".
Cak! ta tsaya da maganar da take hango maciji tayi saman jikin bishiyar da take jingine wata irin razananniyar kara ta saki idanuwa warware Goggo Marka dake rike da kugu jin ihun Hafsi ya sanya Goggo Marka shekawa da gudu tana tsalle tsalle kamar wacce abu ke biwa kafa dama tuni a tsorace take tun da suka shigo cikin dajin gabanta ke faman dukan luguÉ—e.
Ihun Da Hafsi ta cigaba da yi ne ya sanyata tsayawa can gefe tana faman numfarfashi tana bin ko ina da kallo.
"Ke Hafsi Lafiya kike kuwa".
"Maci...ji neee".
Ta fadi cikin rawar baki da na jiki da sauri Goggo Marka ta sake fallewa can gefe tana mai cewa.
"Rugo ki baro wajan mana tun kafin ya illata ki in ma zaki iya kashe shi kawai...".
Ai ba ta karasa abin da take cewa ba itama kurma ihu jin abu ya taba mata kafa.
"Laha'ilaha 'ilallahu muhammadan rasulullahi Sallallahu alaihin wasallam".
Kam! ta kame a tsaye lokaci guda fitsari ya fara bin kafafuwanta.
Hafsi dake can gefe tana faman kurma ihu da tsalle-tsalle kamar wata biri lokaci guda ta fallo a guje tana mai wurgi da kallabin dake kanta zaninta kuwa gabadaya ta tattareshi ta cukuikuye zuwa kugunta a haka har ta iso wajan da Goggo Marka take a kame kanta tayi tana rungume gabadaya ta ma k'yalk'aleta ji kake rigija sun zube a kasa hakan ya dawo da Goggo Marka hayyacinta ta shiga ihu tana mai cewa.
"Ya sare mani kafa shi kenan na bani na lalace shikenan Alkiyamata ta zo wayyo ni kai na...".
Hafsi ta gani zube gefe guda tana faman sakin numfashi gami da dariya ya sanyata yin fakare da idanuwa jikinta sai k'yarma yake yi a hankali ta shiga jan numfashi tana mikewa kafun ta gyara daurin zaninta.
"Ba dai ya sare ki ba ko Hafsi".
Ta fadi tana bin sassan jikinta da kallo Hafsi ce ta sake kecewa da dariya tana mikewa har lokacin jikin nata bai daina bari ba.
"Goggo menene haka a jikin ki?".
Jin abin da Hafsi ta fadi tana zare ido ya sanya Goggo Marka sakin sallallami tana tsalle kamar wata biri hakan ya kara baiwa Hafsi dariya har tana rike ciki ganin hakan ya sanya Goggo Marka dubanta tare da yi mata dakuwa don ta lura kawai so take yi ta firgita ta.
"Fitsari fa Goggo Marka".
Ta sake fadi tana kwashewa da Dariya sai a lokacin ta lura.
"Ikon Allah".
Ta fadi tana mai juya zanin nata da yayi jagaf!.
"kai Goggo Haka kike da tsoro ashe har na fiki dauriya ma".
Harara ta galla mata.
"ke dalla jaye wahala ba dadi gareta ba, kuma ai tsoro halas ne wallahi ke yanzu in macijin nan ya gaftaramin sara ai sai dai buzu na... Kin ga tashi mu bar wannan azababben dajin tun kafin almatsutsan cikinsa su saukar mana akanmu mu bani mu lalace".
Ta fadi tana mai tattare zaninta da yayi jagaf! Takalmanta a hannu a hankali take taka kasa tana mai dube dube.
Tafiya sosai sukayi kafun su fito hanyar da za ta kai su bakin titi nan ma sai da suka zauna suka huta sosai Hafsi sai faman kwakwazo take yi akan ita fa ta gaji bayan ta kamar zai karye haka take ji duban ragwanta Goggo Marka tayi mata.
"Ke dai akwai sakankiya wallahi na dauka duk ke ake yi wa wannan wahalar amma kin ishi mutane da ihu kin gaji".
Turo baki tayi gaba tana kau da kai a hankali ta mike daga zaman yan borin da tayi ganin Goggo Marka ta dauki hanya ko magana batayi mata ba.
Sun yi tafiya mai dan tsayi kafin su isa bakin titi nan Goggo Marka ta shiga neman tsayar da Mai tasi domin shiga kowa ta tsayar ta sanar da shi inda zata sai ya ce a,a tun tana tsaye har taji ta fara gajiya amma ba su samu mai tasi ba ita kuwa Hafsi na can gefe yashe sai faman numfarfashi take yi.
"Don Allah taimaka".
Ta fadi lokacin da wani mai Tasi yayi slow daidai su jiki na bari ta isa gareshi.
"Gwada zaka kai mu don Allah".
Dubanta yayi sosai kafun ya dubi Hafsi.
"Iyaka ta Kauyen Mutum Daya ba zan shiga Gwada ba".
Ware idanu tayi tana mai yin kasa da murya.
"Haba d'ana taimaka don Allah wallahi mun jima a nan zaune ba mu samu abin hawa ba duk mun gaji ga rana ka ga jikanyata can ma zaune tana numfarfashi".
Dubanta yake yi sosai yana sake duban Hafsi a hankali.
"Nawa za ku bayar?".
"Naira dari za mu baka".
Tsuke fuska yayi lokaci guda.
"nifa ba zan shiga Gwada ba sai dai in sauke ku a Mutum daya ku nemi wata motar ta karasa da ku".
kara kashe murya tayi tana kokarin masa magiya yayi saurin tare.
"Allah ba zan je ba in zaku shiga na kai ku mutum daya to in ba kwaso nayi gaba".
Shiru tayi tana tunani kafun ta juya ta dubi Hafsi da ta zuba musu ido tana jin komai gyada kai tayi alamun su je kawai da babu gwara ba dadi kuma a saka a baka yafi a rataya.
Haka suka dunguma cikin motar Goggo Marka sai faman tsaki take yi tana gunguni wai dan tasi din ba shi da tausayi tana tsohuwa amma ba zai taimaka mata ba gashi ya tsula musu kudi.
Ba wanda ya kulata haka ta karaci maganar ta tayi shiru a haka har suka isa Mutum daya suka sauka ba su fi mintina biyu ba suka samu motar Gwada nan ma sai da aka kai ruwa rana da direba don ya lura Goggo Marka yan son banza ce shi kuwa ya nuna mata ya fi ta son kudi ko bakano haka ya ganshi ya barshi.
Haka tashiga motar tana ta mita shima sai masifa yake yi mata yana hadawa da yarensa na yarbanci abu yaki ci yaki cinyewa kamar cin kwan makauniya ganin da yayi ta zage sai surfa ruwan bala'i take ana bata hakuri amma ina aiko ya ja burki yace ta fice masa daga mota.
"kai kam anyi watsantsan d'a wallahi dan bakin mugun abu".
Ta fadi a zuciya amma a fili sai tayi lakwas ganin haka ya sanya sauran fasinjan baiwa direban hakuri haka ya koma ya ja motar yana faman jan tsaki kamar harshensa zai katse.
********
*9/MAY*
*_WATA ALKARYA_*
Tunda ga ne sa zaka hango tsilli tsille na tamfol da aka kankafa kamar dakuna wani saman tamfol kuma a kwai tuta dake kafe akai an rubutu sunan Malik bin yazid da rubutun arabic sosai wajan yayi tsit kamar ba kowa sai mashina kiran bajat dake warwatse a tsakar wajan ko wani tamfol daya kuwa an kewayeshi da ginin dutse wanda ya kusan rufe shi can gefe guda kuma wani tamfol din ne amma duk yafi sauran girma da fadi nesa ba kusa ba.
Zaune yake jikinsa sanye da bakar jallabiya fuskarsa cike take da kasumba ga wani gemu ajje sosai ya naÉ—e kansa da farin kyalle mai laushi sosai idanuwansa jajaye ne fuskarsa daure tamau kamar bai taba dariya ba gefensa bindigogi ne kirar Ak47 kusan biyar.
Duban mutumin dake durkusa gabansa yayi da wani irin kallo mai razanar da wanda akayi wa shi yana mai fadin.
"Baaba BG nayi maka gargaÉ—i na farko kuma na karshe a wannan alkaryar ban taba samun matsala da duk iyalan kungiyar nan ba sai kai a karo na uku kenan ina sanyaka aiki kana bani matsala ban san me kake nufi ba ya kamata ka sani wannan alkaryar da ka shigo ba a sassauci sannan ba a saka mutum aiki ya kiyi rayuwar saida rai ce a wannan sansanin rayuwa ce ko mutuwa ya kamata ka sani jahadi kake yi ko mutuwa kayi a wannan hanyar ka zama shahidi".
Ya karashe yana mai dago daya daga cikin bindigun da suke yashe gefensa kafun ya daga zuwa sashi da kuka yake tashi lokaci guda ya saita jikake durum ya dauke mai kukan can gefe guda kansa yayi fata-fata kafafuwansa sai motsawa suke yi kafun su kame lokaci guda.
Wani dan kyalle ya dago yana mai goge jikin bindigar kafun ya saki wani murmushi mai zafin gaske yana duban Baaba BG da yake sunkuye jikinsa sanye da jallabiya kansa da rawani fuskarsa cike da kasumba ba ka iya gane asalin fuskarsa saboda tulin suma da ya tara.
"Ka sani ba zan yarda da wannan gangancin naka ba domin kuwa a ko wani lokaci zan iya dauke ka daga duniyar nan kamar yarda na dauke waccan yarinyar da take wa mutane ihu".
Har zuwa lokacin Baaba BG bai dube shi ba kan sa na kasa sai faman jan numfashi yake yi.
Motoci ne kirar Sharon suka shigo wajan a jere guda uku ko wacce da tuta a jikin ta can gefe guda sukayi parking kafun su fara fitowa da É—aiÉ—ai ko wanne cikin su fuskarsa yane ba ka iya gane su hannayensu dauke da manya manyan bindigogi daya daga cikin su ne ya fara takowa har ya iso in da shugaban nasu yake ya zube a kasa kamar zai masu sujjada.
"Yah Shugaba mun kammala komai".
GyaÉ—a kai yayi kafun ya daga kai yana kallon yarda ake fiddo da mata matasa daga cikin motocin jikin su sanye da kaya iri daya kallo daya zakayi musu ka gane yan makaranta ne wacce fuskarta cike da tsoro wasu ma sai rusar kuka suke yi.
Murmushin gefen kunci yayi kafun ya mike kan kafafuwansa ya fara takawa kamar wani mai ji da sarauta da mulki har ya isa wajan izuwa lokacin an gama fiddo da su akalla za su kai dari da yan kai jera su akayi ya shiga bin su da kallo daya bayan daya yana kara fadada murmushin fuskarsa.
"Kun tabbata dukkansu ku ka kwaso".
Duban juna sukayi su duka kafun su gyada kai alamun 'eh' daya daga cikin su ne ya dora da cewa.
"Yah Shugaba yanzu haka ma kauyen Sarwadi mun tayar dashi ba wani wanda yayi rai a cikin su.
Murmushinsa ne ya sake faɗaɗa kafun ya sanya hannu ya fizgo daya daga cikin matar wacce ta kasance ita kadai ce mace mara hijabi da cikakkiyar suttura sosai ya damki gashin kanta yana ja kafun ya yi wani gurgi da ita ta baje a kasa gami da sakin wata razananniyar kara mai sauti gaɓadayan sauran suka shiga ihu su ma suna kokarin tarwatsewa da sauri fizgo bindiga daga hannun yaran nasa ya shiga sakar musu wuta ciki zafin nama kawai zubewa suke yi a kasa kafin wani lokacin duk rabin su ya bajar da su akasa sauran kuwa takurewa sukayi waje daya wasu ba su daina gudu ba suka yanki cikin dajin sosai suna faman ihu da kururuwa.
Wata dariya ya saki kafun ya dubi Sauran Yaran sa.
"Kar ku sake daya daga cikin wadancan da suka yanki daji su sake numfashi a doron kasar nan ina son kafin mintina naga gawar su".
Kafun ya dire kalamansa wasu su falle da gudu sun yanki daji sauran da ba su tafi ba ya dube su.
"ku kwashe dukkan su ku zuba masu sark'a".
Yana fadin haka ya juya ya dubi wacca ya damkar wa gashi dazu sai faman rusa kuka take yi jikinta na kyarma idanuwanta sun kaÉ—a sun yi jajir gefen kanta na zubda jini in da ta bugu sosai.
Isa yayi gareta ya dan rankwafa yana mai sakin murmushi kafun wani lokaci fuskar canza ta koma wata kala daban ta tsananin rashin Imani da tausayi kanta ya sake kai hannu ya cafka yana mikar da ita kan kafafuwanta wani ihu ta saki gami da rushewa da kuka wani zafi ne da raÉ—aÉ—i da zugi take jin duk wani kafa ta sumar guda daya na fita komai take ji na jikinta yana canzawa kamar bana ta ba ji take yi kamar ba a duniya take ba kamar wata duniya ce ta azaba take ji ita kadai ne a ciki.
Haka ya ja ta akasa tana ihu tana komai har ya isa daidai mazauninsa har lokacin Baaba BG na durkushe in da ya barshi cilli yayi da ita waje guda kafin ya dago bindiga ya saita goshin sa.
"In har kika sake naji wani abu mai kama da kuka sai na tarwatsa miki kan ki yanzun nan".
Ya fadi yana tamke fuskarsa cikin wani irin yanayi na rashin tausayi da imani.
Dago idanuwanta tayi da take jin su kamar bana ta ba sun kaÉ—a sun yi jajir jijiyoyin kanta duk sun fito sunyi raÉ—a-raÉ—a abin ka da farin mutum gabadaÆ´a jikinta ya rine yayi jajir waje guda ta haÉ—e jikinta ta dunkule zuciyarta na kara dokawa da tashin hankali mai girman gaske ba abin da take tunawa sai yarda aka ci zarafin su aka keta musu mutunci a gaban idanuwansu aka yanka iyayen su a gaban idanuwansu aka bambaka musu kauyensu garinsu da suke zaune cikin kwanciyar hankali lokaci guda an canza musu rayuwa an kaskantar da su an mai da su ko dabbobi sun fi daraja da kima ba ta san yarda zata ce ba bata san ya zata kira wadannan mutanan ba sosai take hango salon da suka shigo masu gari da shi na tsayin sati biyu suna nuna musu suna Allah ne hanyar tsira da dacewa suke nuna musu ashe ba haka bane sai da suka saki jiki da su lokacin guda suka fiddo musu da kudirin su da manufarsu.
Wani kuka ne taji ya kufce mata lokaci guda da sauri ta kai hannunta ta toshe bakin ta amma duk da hakan sai da kukan nata ya fito waje runtse idanuwanta tayi cikin sadakarwa jira kawai take taji alburushi ya ratsa tsakanin kwanyarta sosai ta hango yarda a gabanta aka dannewa mahaifinta kirji aka soka masa wuka a makoshi tana kallon yarda suka mai dashi kamar wani kare suka dinga ball da gawarsa har sai da suka ga numfashin sa ya daima motsi kafun su rabu dashi bayan sun cinna masa wuta.
Wasu zafafan hawaye take ji suna sauka a kuncin ta lokaci guda kuma taji ana dauke mata su a hankali ta fara buÉ—e idanuwanta da take jin kamar za su zazzzago kasa saboda raÉ—aÉ—i da zugi da taji suna yi mata.
Wani razananiyar kara ta saki ganin wanda yake gabanta lokaci guda ta dunkule waje daya jikin ta na faman kyarma idanuwanta na kansa tsanarsa take ji tana tsarga ko wani sashi na jinin jikinta sosai take ji a fadin duniyar nan ba wanda ta tsana kamar sa rokon Allah take yi ya daukar mata ranta da wannan BALA'I da take ciki rokon Allah take yi ya rabata da wannan mugun azzalamun da bai san imani da tausayi ba a zuciyarsa.
"Dama kin daina kukan nan domin kuwa yanzu rayuwa ce zaki sauya duniyarki zaki canza komai naki zai canza ki sani wannan wata duniya ce zaki fara rayuwa a cikinta tare dani zaki kasance har zuwa lokacin da nayi raayin rabuwa dake".
Hannu ya kai yana kokarin shafe fuskarta a karo na biyu da sauri taja da baya gabanta na sake bugawa lokaci guda ta shiga kankame jikinta tana hadewa waje daya.
"ki kasance da Malik Bin Yazid a duniyarki sabuwa".
Wani irin zaro idanu tayi waje kamar za su fada birkicewa da rkicewa da razana duk suka gauraya lokaci guda a gareta zuciyarta ta ji ta sauya bugu numfashin taji ya fara fizga cikin tashin hankali magunan jinin jikinta take ji suna yin kasa suna tsayawa cak! jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa sunan da taji ya ambata ya shiga ansa amo mai sauti a kwanyarta lokaci guda numfashinta ya tsaya cak! ta sankare a wajan.
Ta jima cikin wannan yanayin kafun ta ja wani numfashi mai tauri kirjinta taji yayi mata nauyi har zuwa lokacin idanuwanta na kansa shikuwa sai faman murmushi yake yi don ya luta da razanar da tayi.
'Malik Bin Yazid'
Ta fadi a zuciyarta sosai ta gane sunan sosai ta tuna sunan. sunan da ko fadin sa akayi dole ka shiga tashin hankali saboda irin tashin hankalin dake tattare dashi ba zata manta wannan sunan ba sosai tajima da haddace shi sosai ta gane shi rikakken dan ta'adda da ake nema RUWA A JALLO mutumin da ya addabi al'umma mutumin da ya kasance masifa da bala'i a rayuwar al'umma ya hana su kwanciyar hankali da natsuwa yana rayuwarsu tafiya yarda ta kamata mutumin da ya haifar da bala'i da rashin kwanciyar hankali ga zuciyoyi masu yawa mutumin da ya haifar da ciwo mai girman gaske a zuciyoyi masu yawa shine Allah ya hada ta dashi ita ce yau tare dashi rayuwar tace ta juye zuwa duniyarsa ita kuwa wata irin mummunar ƙaddara ce ta fado mata rayuwa ita kuwa wani irin BALA'I ya fado mata rayuwa a daidai wannan lokacin bata san mai za ta ce ba bata san ya za ce da wannan ƙaddarar ba ta sani rayuwarta ta kare komai nata ya sauya zuwa tashin hankali da bala'i ta sani tayi bankwana da farin ciki tayi bankwana da kwanciyar hankali ta rabu da iyayenta har abada ga shi yanzu ita kuma ƙaddararta ta jona ta da wannan bala'in wanda ba ta san ya zata kwatantashi ba.
Gyada kai ta shiga yi idanuwanta na fiddo da wasu hawaye masu tsananin zafi da kokarin yayyaga mata fatar fuska duban sa take yi da wani irin yanayi mai girman gaske tana ayyanawa a ranta wannan mutumin mai rai daya a jikinsa shine ya addabi miliyoyin mutane ya hana su kwanciyar hankali bata san ya zata kwatatta wannan lamarin ba.
"Karki yi tunanin sake wata rayuwa kawai ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid".
Wani zafi taji kirjinta nayi kafun wani abu mai girman gaske ya zo ya tokare mata kirji dago idanunta tayi tana duban Baaba BG wanda tun da aka kawo su duniyar BALA'In nan ta lura dashi a durkushe har izuwa wannan lokaci tsoho ne sosai wanda wahala da bala'i suka dakusar dashi wajan kara zama tsoho na karfi da yaji fuskarsa kawai ta kalla ta gane bala'in da yake ciki idanuwansa a kasa ko motsin kirki ba yayi wani irin tausayin sa taji ya tsirgar mata da sauri ta kau da kai kafun ta dubi Malik wanda har lokacin yana rankwafe a gabanta.
Kallon sosai tayi masa lokaci guda ta ji zuciyarta ta kekeshe da duk wani tashin hankali da take ji komai taji tsaya mata na tsoro kallon sosai da sosai tayi masa kafun ta kau da kai tana jan tsaki can kasar makoshinta.
Wani wawan Mari da sanya ta sakin fitsari da ganin taurari taji ya gilma a kuncin ta lokaci guda ta baje a kasa gami da kurma uban ihu.
Mikewa yayi zuciyarsa na wani irin tukuki da zafi bindigi ya ciru daga kugunsa karama lokaci guda ya saita ta sosai idanuwansa na bayyanar da wani tashin hankali mai girman gaske runtse idanu tayi tana jiran saukar alburushin domin ta gama sadakarwa ba za ta sake ko da minti daya a duniya nan ba.
Tun tana jin tafiyar numfashinta da sauri-sauri gabanta na wani bugu mai girman gaske a hankali ta fara kiran sunan Allah kafun taja numfashi mai girma ta buÉ—e idanuwanta tsaye ta hangeshi har yanzu bindigar na saitinta amma bai harba ba.
Mamaki ya cika mata zuciya sosai ganin yanayin da yake ciki gabadaya idanuwansa na kanta ga bindiga a hannunsa amma ya kasa harbawa kuri tayi masa da idanu tana mai sakin ajiyar zuciya sunayen Allah a laɓɓanta ba ta san ma mai za tayi ba komai take jin yana zama al'ajabi da mamaki a gareta ba ta ankara ba kawai taga ya cafko hannunta ya mikar da ita cikin wani irin yanayi na mazantaka ya shiga jan ta ciki hanzari kamar zai kifata da kasa ita kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah lokaci guda fargaba da razana da tsoro suka shiga tsalle -tsalle a zuciyarta har lokacin da suka iso wajan da Baaba BG yake yashe idanuwa ya dago a cikin galabaitaccen yanayi ya dubeta ita ma shi take duba cikin wani yanayi na tsanani sadakarwa sosai suke kallon juna cikin yanayi na tashin hankali mai girman gaske tana kallon shi yana kallonta har zuwa lokacin da taji Malik ya fizge ta zuwa cikin tamfol din sa yayi cilli da ita a ciki ba komai a cikin tamfol sai hargitse wanda sam ba su dakyan gani bindigogi da alburusai can gefe kuma wata yakunaniyar shimfiɗa ce mai dauke komaitsai da sauri ta dago kai gabanta na cigaba da bugawa tana dubansa shima ina ya ke duba kafun ya ajje kallonsa ga kan shimfiɗarsa.
"Zaki kasance dani kamar yarda na sanar dake ki shirya zama dani ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una".
Abin da zuciyarta ta shiga fadi kenan cikin kyarma da tsoro lokaci guda ta shiga matse jikinta waje daya duban sutturar jikinta take yi yarda aka kekketa ta sosai ana hango wasu sashi na jikinta ya bayyana a fili runtse idanu tayi wasu hawaye su ka balle mata.
Ta sani shikenan rayuwarta ta kare shikenan duniyarta ta gama k'awa da tashin hankali wnda ba ta san ran fita daga cikin sa
A Hankali taji ya fara takowaa kusa da ita gabanta yana tsananta faduwa jikinta sai kyarma yake yi lokaci guda numfashin ta ya fara sama da kasa lokaci guda ta saki razananniyar kara cikin firgici da tashin hankali komai taji ya tsaya mata cak! duniyar tana juya mata bata san abin da ke faruwa ba idanuwanta dai na kansa har lokacin da iso gareta ya rankwafa yana mai kamo hannayenta duk biyu yana mikar da ita a hankali idanuwanta suka shiga rufewa kafun taji jikinta na narkewa lokaci guda tana watsewa a kasa....


😘😘 *_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)